Chelsea 1-0 Man City
Wannan sakamako ne mai kyau ga Chelsea domin zai taimaka mata a neman gurbin shiga gasar Champions League.
Wannan shafi ne kai tsaye da zai ke kawo muku labarin wasanni a karawa tsakanin Chelsea da Manchester City da sauran karawar da ake yi a wannan lokacin.
Mohammed Abdu
Wannan sakamako ne mai kyau ga Chelsea domin zai taimaka mata a neman gurbin shiga gasar Champions League.
An koma zagaye na biyu ko Chelsea za ta yi Liverpool aiki ko kuma kungiyar ta Anfield ta ci gaba da jiran lokacin da za ta lashe Premier League na bana.
An je hutu za su sha ruwa sannan a ci gaba da zagaye na biyu.
Ko Liverpool za ta daga kofin Premier League da ana kammala wasan nan?
Chelsea za ta yi wa Liverpool aiki kenan.
Kungiyar Arsenal ta yi nasara a gidan Southampton da ci 2-0 a wasan mako na 31 da suka buga a gasar Premier League.
Karon farko da Arsenal ta yi nasara tun bayan da aka koma ci gaba da wasannin bana.
Ta yi rashin nasara a hannun Man City da kuma Brighton

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta bai wa Australia da kuma New Zealand izinin karbar bakuncin gasar cin kofin duniya ta mata da za a yi a 2023.
Kasashen biyu da za su yi hadaka sun yi nasara ne a kan Colombia da suka yi takara tare, bayan da Brazil da kuma Japan suka janye tun farkon cikin watan Yuni.
Gasar 2023 za a yi ta da kasashe 32 maimakon 24 da suke karawa a baya.
Za a fara gasar cin kofin duniya ta mata daga Yuli zuwa Agustan 2023.

Asalin hoton, Getty Images
Man City ce ta buga kwallo gidan Chelsea aka yi cin kasuwar sama ta yi waje inda Mendy ya hade da dan uwansa sai Pulisic ya ja kwallo har zuwa gidan City ya kuma zura a raga.
Ba ka rasa magoya bayan Liverpool da suka yi murnan cin kwallon ba domin tana da mahimmaci a wajensu.
Chelsea ta yi motsi mai kyau.
Chelsea ta bude wuta don ganin ta samu sakamako tun da wasan ya fara nutsawa a yanzu haka,
Wannan wani mai goyon bayan Liverpool ne ya fara murnar cin kofi da za su yi, amma dai da saura sai yadda wasan nan ya tashi.

Asalin hoton, Getty Images
Kyle Walker ne ya bugo kwallo sai dai kuma Ross Barkley ya sa kai ta yi waje.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
City ta bugo kwana sai dai ba hadari inda aka sa kai ta yi sama cikin fili.
Har yanzu City ce ke rike kwallo.
Man City ta kusan cin kwallo bayan da aka yi bugun kusurwa sai Fernandinho ya samu kwallo a da'ira ta 18 shi kadai ya sa kai sai dai golan Chelsea ya sa mata hannu ta yi saman raga.
Real Madrid ta zama ta farko da ke da yawan cin wasan La Liga a gida, bayan da ta doke Real Mallorca kuma shi ne na 1,100 da ta yi nasara.
Jumulla Real ta yi wasan gasar La Liga 1,435 a gida da canjaras 205 da rashin nasara a wasa 130.
Wacce take biye da Real Madrid a yawan cin wasa a gida ita ce Barcelona da nasara 1,095.
Real ta yi wasan La Liga a bana ba a doke ta ba a gida, bayan da ta ci wasa 12 da canjaras 4.
Kakar da Real ta fi taka rawar gani a gida a La Liga ita ce ta 1987/88 da kuma 2009/10, inda ta ci wasa 18 ta kuma ci kwallaye 3,833 a lokacin.
Real Madrid wacce take da maki iri daya da na Bacelona ta koma ta daya a kan teburin La Liga, bayan da ta doke Real Mallorca 2-0.
Ranar Asabar 27 ga watan Yuni, Barcelona za ta ziyarci Celta de Vigo a wasan mako na 32.
Sai a ranar Lahadi 28 ga watan Yuni, Espanyol za ta karbi bakuncin Real Madrid.

Asalin hoton, Getty Images
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Benjamin Mendy ne ya samu kwallo daga kusiurwar wajen kwana ya bugo ta da karfi zuwa gidan Chelsea ko wani dan wasan zai yi karo da ita ta fada raga.
Sai dai mai tsaron raga Kepa ya kama cikin sauki,
Manchester ce kan gaba a rike kwallo Chelsea na kokarin tsare gida duk da ita ce ke karbar bakuncin a Stamford Bridge ba 'yan kallo.
Riyad Mahrez ya buga kwallo daga barin hagu amma N'Golo Kante ya tare sai dai ta koma wajen City Chelsea sai tare take ta yi .
Kevin de Bruyne ya dan fadi daf da Bernardo Silva kuma Mason Mount yana tare da shi.
Ko wa zai yi nasara a wasan?