Yadda aka fafata a Premier ranar Asabar

Sharhi kai-tsaye kan wasannin Premier mako na 11

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Bournemouth 1-0 Man United, Shekara 29 kenan rabon da haka ta faru!

    Rabon da United ta yi irin wannan rashin katabus tun a shekarar 1990. Rashin nasararta ya fi nasararta yawa a Premier ta bana - Hudu kawai ta ci cikin 11

  2. Shi ke nan! Wasa ya kare, Bournemouth 1-0 Man United

    An tashi kuma Manchester United ta sha kashi a hannun Bournemouth, sun yi rashin nasara a hudu daga cikin wasa 11 da suka buga a kakar bana.

  3. Bournemouth 1-0 Man United

    Nathan Ake shi ne dan bayan da ya hana United ganin raga a wannan wasa mai cike da kujiba-kujiba. Dan wasan shi ne bangon Bournemouth.

  4. Bournemouth 1-0 Man United, Katin gargadi

    Wilson na Bournemouth ya karbi kati saboda faduwar karya da ya yi a tsakiyar fili

  5. Bournemouth 1-0 Man United

    Minti uku kacal aka kara

  6. Bournemouth 1-0 Man United, Solkjaer

    Minti hudu ya rage a tashi daga wasan. Ba mu san inda Solkjaer zai sa kansa ba idan aka tashi haka

  7. Bournemouth 1-0 Man United, Bournemouth ta yi canji

    L. Cook ya canji Harry Wilson

  8. Bournemouth 1-0 Man United

    Kiris ya hana Greenwood ya jefa kwallo amma ta daki turke ta fito

  9. Bournemouth 1-0 Man United, United ta yi canji

    Greenwood ya karbi Daniel James yayin da Brandon Williams ya sauya Aaron Wan-Bissaka.

  10. Bournemouth 1-0 Man United

    Ashley Young ya bugo kwana amma 'yan bayan Bournemouth sun tsige ta ba tare da wani hadari ba.

  11. Bournemouth 1-0 Man United

    Minti 78 da fara wannan wasa amma har yanzu United ba ta samu nasarar zare kwallon ta ba. Ba ta nuna wata alamar yin hakan ma domin har yanzu rawar da take takawa ba wata mai armashi ba ce.

  12. Bournemouth 1-0 Man United, An kusa ta biyu

    Kiris ya hana Harry Wilson ya kara kwallo ta biyu amma De Gea ya hana ta shiga

  13. Bournemouth 1-0 Man United, Lingard

    Kusan shekara daya kenan Jesse Lingard bai zira kwallo a gasar Firimiya ba, wannan ne lokacin da ya kamata ya nuna kansa, bayan ya karbi Andreas Pereira

    Jesse Lingard

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Jesse Lingard
  14. Bournemouth 1-0 Man United, Bournemouth ta barar da dama mai kyau

    Bournemouth ba ta amfana da bugun tazarar da ta samu ba.

    Ashley Young ne ya ture Adam Smith a bakin ragar United, shi kuma lafari ya bayar da bugun tazara a wuri mai hadarin gaske. Sai dai Bournemouth ba ta amfana daga damar ba.

  15. Bournemouth 1-0 Man United

    An bai wa Lindelöf katin gargadi bayan taka Harry Wilson

  16. Bournemouth 1-0 Man United, Ko United za ta yunkura?

    Manchester United ba su da tabbas ko za su iya sauya wasan a minti daya kamar yadda suka yi a wasansu da Chelsea.

  17. Bournemouth 1-0 Man United, Katin gargadi

    An bai wa Steve Cook katin gargardi bayan fitar da Rashford da ya yi......

    Jesse Lingard na motsa jiki zai shigo wasan......

  18. Bournemouth 1-0 Man United

    Harin farko bayan dawowa daga hutun rabin lokaci yayin da Ryan Fraser na Bournemouth ya dada wa De Gea kwallo amma mai tsaron ragar na United ya kama ta ba tare da wani ji ba.

  19. Bournemouth 1-0 Man United

    Yanzu haka Man United ce ke fafatawa da Bournemouth, inda Bournemouth din ta cilla wa United kwallo a raga a minti na 45 ta kafar Josh King.

    Josh King

    Asalin hoton, Getty Images

  20. Bournemouth 1-0 Man United, Bournemouth 1-0 Man United

    Barkanmu da saduwa a wannan shafin da zai kawo maku rahotanni kai-tsaye na Premier da sauran wasannin lig lig na kasashen Turai a yau Asabar.

    Umar Mikail da Buhari Muhammad Fagge ne ke maku barka da rana