Yadda aka fafata a Premier ranar Asabar

Sharhi kai-tsaye kan wasannin Premier mako na 11

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Arsenal 1-0 Wolves, Arsenal 1-0 Wolves

    Minti 45 na farko ya kare

  2. Sheff Utd 3-0 Burnley, Sheff Utd 3-0 Burnley

    Sheff Utd ta kara kwallo ta uku

  3. Sheff Utd 2-0 Burnley, Sheff Utd 2-0 Burnley

    Sheff Utd na ci gaba da jan ragamar wasan.

  4. Gasar Serie A, Roma 2 - 1 Napoli

    A gasar Serie A ta kasqar Italiya kuma Roma ce ke cin Napoli.

    Arek Milik na Napoli ya zira kwallo daya a ragar Roma, sauya kwallo daya kacal a farke

  5. Man City 0-1 Southampton, Man City 0-1 Southampton

    Pep Guardiola ya juya ga magoya baya yana neman su kara ci gaba da bai wa tawagarsu kwarin gwiwar farke kwallon da aka zira masu.

  6. Arsenal 1-0 Wolves, Arsenal 1-0 Wolves

    Arsenal na ci gaba da kai kora, yau dai kamar ba Wolves ba irin kwallon da ake buga mata...

  7. Brighton 0-0 Norwich, Brighton 0-0 Norwich

    Har yanzu babu ci tsakanin kungiyoyin biyu.

  8. Aston Villa 1-0 Liverpool, Aston Villa 1-0 Liverpool

    Liverpool ta zira kwallo amma ana dubawa...... sai dai kash na'urar VAR ta hana kwallon

  9. GOAL, West Ham 0-2 Newcastle

    Duk da cewa ita ce a waje amma ta samu damar kara kwallo ta biyu ta hannun Federico Fernández

  10. GOAL, Aston Villa 1-0 Liverpool

    Trezeguet ya cilla Kwallo a ragar Liverpool

  11. GOAL, Arsenal 1-0 Wolves

    Pierre-Emerick Aubameyang ne ya jefa kwallo a ragar Wolves

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  12. GOAL, Sheff Utd 1-0 Burnley

    John Lundstram ne ya jefa kwallon

  13. West Ham vs Newcastle, Newcastle

    Newcastle ta mamaye wasan da take bugawa tsakanin ta da West Ham duk da cewa ita ce a waje.

  14. GOAL, Man City 0-1 Southampton

    Southhamton ta jefa wa City Kwallo daya a raga ta hannun James Ward-Prowse

  15. Man City vs Southampton, Man City vs Southampton

    Man City vs Southampton

    Daya daga cikin sauyi uku da Pep Guardiola ya yi a yau in aka kwatanta da wasan baya shi ne, dan wasan bayan Sifaniya Angelino zai fara buga wa Manchester City wasa a wannan kakar.

    Kyle Walker tare da Sergio Aguero sun dawo, yayin da aka ajiye Joao Cancelo da Fernandinho da kuma Benjamin Mendy.

    Tawagar Man City: Ederson, Walker, Stones, Fernandinho, Angelino, De Bruyne, Gundogan, Silva, Bernardo Silva, Aguero, Sterling.

    Yan benci: Gabriel Jesus, Mendy, Mahrez, Joao Cancelo, Otamendi, Foden

  16. Man City vs Southampton, Man City vs Southampton

    Wannan ne wasan Premier na farko da Southampton za ta buga tun bayan rashin nasarar da ta yi a hannun Leicester City da ci 9-0, sai dai mai horaswa Ralph Hasenhuttl ya yi wasu sauye-sauye uku a wasan yau.

    Mai tsaron raga Alex McCarthy da dan wasan tsakiya Stuart Armstrong za su fara buga wasansu na farko a wannan kakar, yayin da Jack Stephen ya dawo cikin yan baya a yau.

    An ajiye Angus Gunn, Maya Yoshida da kuma Ryan Bertrand a benci.

    Tawagar Southampton: McCarthy, Valery, Bednarek, Stephens, Vestergaard, Hojbjerg, Ward-Prowse, Romeu, Armstrong, Ings, Redmond.

    Wadanda ke benci: Yoshida, Long, Adams, Djenepo, Boufal, Gunn, Danso.

  17. Ozil zai buga wasansa na biyu a Premier, Arsenal vs Wolves

    Ozil zai buga wasansa na biyu a kakar wasanni ta bana. Wannan ya biyo bayan irin rashin jituwar da aka yi fama da ita a 'yan kwanakin nan tsakanin Ozil da Unai Emery.

    Ozil

    Asalin hoton, Getty Images

  18. Arsenal v Wolves, Arsenal v Wolves

    Kocin Arsenal Unai Emery ya yi canji biyu a tawagarsa bayan can-jaras da ta yi da Crystal Palace a makon jiya, babu Granit Xhka da Pepe, inda ya sauya su da Lucas Torreira da Mesut Ozil. Ozil zai buga wasansa na biyu a kakar wasanni ta bana.

    Tawagar Arsenal:Leno,Tierney, Sokratis, Chambers, Luiz, Ceballos, Guendouzi,Torreira, Ozil, Aubameyang, Lacazette.

    Yan canji: Martinez, Bellerin, Pepe, Willock, Kolasinac, Martinelli, Saka

  19. Da alama United za ta koma matsayin da ta baro, Bournemouth 1-0 Man United

    Da alama Man United za ta koma matsayin da tabaro a makon jiya....babu tabbas ma ko za ta tsaya a matakin. Yanzu haka tana mataki na 8

    Teburin Premier
    Marcos Rashford

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Marcos Rashford
  20. Bournemouth 1-0 Man United, Bournemouth ta zama ta shida a teburi

    Nasarar da Bournemouth ta yi a yau ita ce ta farko a cikin wasa 5 ta buga kuma yanzu ta matsa zuwa mataki na shida da maki 16, maki uku kenan a saman Man United din.