Yadda aka fafata a Premier ranar Asabar

Sharhi kai-tsaye kan wasannin Premier mako na 11

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Karshe

    Nan muka kawo karshen sharhi da rahotannin. Umar Mikail ke maku fatan mu kwana lafiya.

    Wasu daga cikin aikace-aikacen da aka yi a yau

    Abraham

    Asalin hoton, Getty Images

    Messi

    Asalin hoton, Getty Images

    Rashford

    Asalin hoton, Getty Images

    Liverpool

    Asalin hoton, Getty Images

    Man City

    Asalin hoton, @ManCity

  2. Real Madrid ta take wasa, Real Madrid vs Real Betis

    Madrid za ta yi yunkurin dorawa a kan nasarar da ta samu a kan Leganes da ci 5-0 ranar Laraba. Ganin cewa Barcelona ba ta iya cin nata wasan ba idan Real din ta ci za ta haye saman teburi.

  3. Wasa ya kare, Watford 1-2 Chelsea

    Chelsea ta ci gaba da zamanta a mataki na uku da maki 23, godiya ta musamman ga Tammy Abraham da Christian Pulisic, wadanda suka tabbatar da faruwar hakan.

    Chelsea

    Asalin hoton, @ChelseaFC

    Bayanan hoto, Tammy Abraham da Christian Pulisic
  4. Watford 1-2 Chelsea

    Saura minti biyu a tashi daga wasa bayan an kara minti biyar

  5. GOAL Watford 1-2 Chelsea, VAR ta bayar da finareti

    Watford ta samu bugun finareti bayan da Jorginho ya yi wa Gerard Deulofeu keta a kusa da yadi na 7.

    Sai bayan an duba na'uarar VAR ne sannan alkalin wasa Anthony Taylor ya ce finareti ne.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  6. GOAL, Watford 0-2 Chelsea

    Christian Pulisic ne ya ci wa Chelsea kwallo ta biyu, mako biyu kenan a jere dan kasar Amurkan yana cin kwallo a Premier.

    Tammy Abraham ne ya taimaka aka ci kwallon kuma hakan na nufin Abraham yana da muhimmancin gaske ga tawagar Frank Lampard

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  7. Levente ta yi wa Barcelona mahangurba, Levente 3-1 Barcelona

    Barcelona ta sha mamaki a wasan La Liga mako na 12 bayan Levente ta lallasa ta da ci 3-1 a filin wasa na Estadio Ciudad Valencia.

    Messi ne dai ya fara tsokano tsuliyar dodon da kwallon da ya ci daga bugun finareti a minti na 38 kafin daga bisani Jose Campana ya farke ta farke a minti na 61.

    Levente ta yi wa Barcelona rubdugu, inda ta ci kwallo biyu a cikin minti 10 ta hannun tsohon dan wasan Real Madrid Borja Mayoral da kuma Nemanja Radoja.

    Sai dai tun a minti na 74 Messi ya kara ta biyu amma na'ura mai taimaka wa alkalin wasa ta VAR ta hana, inda ta ce an yi satar gida.

    Wannan rashin nasarar ya rikito da Barca daga mataki na daya zuwa na biyu da maki 22 a wasa 11, yayin da abokiyar hamayyarta Real Madrid za ta karbi bakuncin Real Betis da karfe 9:00 na daren yau Asabar.

    'Yan wasan Barcelona

    Asalin hoton, Getty Images

  8. Hutun rabin lokaci, Watford 0-1 Chelsea

    An tafi hutun rabin lokaci yayin da waa ke zuwa wa Chelsea da sauki.

    Watford suna na karshe-karshe a teburi kuma suna buga wasan kamar da ma cen kasan teburin wurin zamansu ne.

    Lallai sai sun kara azama in ba haka ba Chelsea za ta jibga masu kwallaye da yawa.

  9. Ra'ayoyinku daga Twitter, Levente 3-1 Barcelona

    Kauce wa X, 1
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 1

    Kauce wa X, 2
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 2

    Kauce wa X, 3
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 3

    Kauce wa X, 4
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 4

    Kauce wa X, 5
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 5

  10. GOAL, Watford 0-1 Chelsea

    Wanda dai ya saba cin kwallon ne ya ci Tammy Abraham......

    Tammy Abraham

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Tammy Abraham
  11. Liverpool na ci gaba da jan zarenta, Liverpool ta cinye Aston Villa 2-1

    Liverpool ta samu nasarar doke Aston Villa har gida da ci 2-1 bayan kwashe kusan minti 93 ana fafatawa.

    Tun da fari Trezeguet ne ya ci wa wa Aston Villa a minti na 21 da fara wasan, yayin da Andy Robertson ya farke wa Liverpool kwallonta a minti 87.

    Ana gab da tashi daga wasan ne kuma Sadio Mane ya kara ta biyu, wadda da ita ne Liverpool ta ci gaba da zama a saman teburi.

    Har yanzu dai Liverpool ce ke ci gaba da jan ragamar gasar Premeir da maki shida tsakainta da Manchester City da ke biye mata.

    Liverpool dai na yawan samun nasarar jefa kwallo bayan minti 90 da fara wasa. Kwallon da Sadio Mane ya ci ita ce ta 35 da kungiyar ta ci bayan cikar minti 90 na wasa, sama da kowace kungiya kenan a Premier da kwallo 10.

    Liverpool za ta karbi bakuncin Manchester City ne a wasa na gaba kafin daga bisa ni ta je Crystal Palace, inda ake ganin wadannan wasanni a matsayin wadanda za su kawo wa Livepool kalubale.

    'Yan wasan Liverpool

    Asalin hoton, Getty Images

  12. Liverpool ta fi kowace kungiya cin kwallo a mintin karshe, Aston Villa 1-2 Liverpool

    Kwallon da Sadio Mane ya ci wa Liverpool ita ce ta 35 da kungiyar ta ci bayan cikar minti 90 na wasa, sama da kowace kungiya kenan a Premier da kwallo 10.

    Sadio Mane

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Sadio Mane
  13. Aston Villa 1-2 Liverpool, An tashi daga wasa

    Wasa mai cike da wahala amma nasara ta tabbata.... maki shida tsakanin Liverpool da mai biye mata a saman teburi wato Man City.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  14. West Ham 2-3 Newcastle, An tashi daga wasa

    Dan da kyar! Newcastle ta kai bantenta

  15. Brighton 2-0 Norwich, An ta shi daga wasa

    Brighton ta samu nasara sau biyu a jere

  16. Man City 2-1 Southampton, An tashi daga wasa

    City ta sha da kyar a hannun Southampton

  17. GOAL, Aston Villa 1-2 Liverpool

    Cikin minti na 93 Sadio Mane ya kara kwallo ta biyu

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  18. Aston Villa 1-1 Liverpool, Aston Villa 1-1 Liverpool

    Liverpool ta samu bugun tazara a gurbi mai hadarin gaske. Sai dai ta buga kuma ta bigi 'yan wasan Villa zuwa kwana

  19. GOAL, West Ham 2-3 Newcastle

    Robert Snodgrass ya jefa kwallo ta biyu a ragar Newcastle.. kwallo daya ce ta rage a yi canjaras. Abin mamaki ne kamar ba Newcastle ne ke kan gaba da kwallo uku ba a lokacin da aka vdawo hutun rabin lokaci

  20. Arsenal 1-1 Wolves, Arsenal 1-1 Wolves

    Arsenal na dosar wata rashin nasarar, in aka tashi haka maki biyu kacal suka samu cikin wasa uku da suka buga na baya-bayan nan

    Mintina kadan ne suka rage a tashi