Russia 2018: Argentina ta fitar da Najeriya

Argentina ta fitar da Najeriya daga Gasar Cin Kofin Duniya bayan ta doke ta da ci 2-1 a ranar Talata.

Rahoto kai-tsaye

Barkanku da shigowa wannan shafin

Jama'a, barkanku da shigowa wannan shafin inda za mu kawo muku yadda za a kara tsakanin Najeriya da Argentina a wasanninsu na uku na gasar cin kofin duniya da ake yi a Rasha a shekarar 2018.