Najeriya 0-1 Argentina
Najeriya ta samu bugun tazara amma golan Argentina ya kama kwallon.

Asalin hoton, Reuters
Argentina ta fitar da Najeriya daga Gasar Cin Kofin Duniya bayan ta doke ta da ci 2-1 a ranar Talata.
Najeriya ta samu bugun tazara amma golan Argentina ya kama kwallon.

Asalin hoton, Reuters
Har yanzu babu ci a wasa tsakanin Iceland da Croatia

Asalin hoton, AFP
Sai yanzu ne Messi ya fara buga gasar cin kofin duniya da ake yi a Rasha, domin bai yi kokari a karawar da suka tashi kunnen doki 1-1 da Iceland da wasan da Croatia ta casa Argentina ba.

Asalin hoton, Getty Images
Argentina ta samu bugun tazara amma golan Najeriya ya ture kwallon da Messi ya bugo.
An ba Balogun katin gargadin bsyan ya yi wa Di Maria keta lokacin da ya kai wa Najeriya wani hari.

Asalin hoton, AFP
Kwallon da Lionel Messi ya ci Nijeriya shi ne na 100 da aka zura a raga a gasar cin kofin duniya da ake yi a Rasha.

Asalin hoton, Getty Images
Golan Najeriya Francis Uzoho ya bugu amma ya murmure bayan an duba shi.
Wasa yana ci gaba da yin zafi, inda duka bangarorin suka zage damtse.
Najeriya ta kai wa Argentina hari amma an dakile.

Asalin hoton, BBC Sport
Argentina ta samu bugun tazara amma Najeriya ta fitar da kwallon.

Asalin hoton, Getty Images
Argentina na ci gaba da danna Najeriya amma masu tsaron bayan Najeriya suna dakilewa.
Ahmed Musa ya kai wa Argentin hari amma kwallon ta fita waje.
Argentina ta sake kai wa Najeriya hari amma ba tare da samun nasara ba.

Asalin hoton, Getty Images
Argentina na danna Najeriya, amma Najeriya ita ma ta kai hari gidan Argentina.
Argentina ta kai wa Najeriya hari amma kwallon ta fada a hannun gola.
Bari mu tuna muka ana karawa a dai wannan lokacin tsakanin Iceland da Croatia.

Asalin hoton, BBC Sport

Asalin hoton, BBC Sport
An fara wasa tsakanin Nigeria da Argentina da gumurzu tsakanin Iceland da Croatia.

Asalin hoton, AFP
Tsohon dan wasan tawagar Argentina Diedo Maradona yana cikin wadanda za su kara wa Argentina kwarin gwiwa.

Asalin hoton, Getty Images