Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Russia 2018: Argentina ta fitar da Najeriya

Argentina ta fitar da Najeriya daga Gasar Cin Kofin Duniya bayan ta doke ta da ci 2-1 a ranar Talata.

Rahoto kai-tsaye

  1. Ana shirye-shiryen fara wasa

    Ana ci gaba da shiye-shiryen fara wasa tsakanin kasashen biyu.

  2. Nigeria da Argentina

    Argentina ta yi amfani da koci uku wajen buga wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya kuma kowan ne da salon da ya yi, san nan ta yi amfani da 'yan wasa 45.

  3. 'Yan wasan Najeriya suna atisaye

    'Yan wasan Super Eagles suna atisaye kafin fara wasan.

  4. Messi na atisaye kafin ya fuskanci Nigeria

    'Yan wasan Argentina suna atisaye gabanin fara wasan.

  5. 'Yan kwallon Argentina ba sa kokari – 'Yan Najeriya

    Saurari muryoyin wadansu 'yan Najeriya, inda suka bayyana ra'ayoyinsu game da wasan.

  6. Nigeria da Argentina

  7. Iceland da Croatia

    'Yan kwallon da za su buga karawa tsakanin Iceland da Ctroatia a wasa na uku a rukuni na hudu.

  8. Wa zai yi na biyu a rukuni na hudu?

    • Croatia ta kai zagaye na gaba a gasar kofin duniya, za ta ci gaba da zama ta daya a teburi idan ta doke Iceland.
    • Nigeria za ta kai zagaye na biyu idan ta ci Argentina. Maki daya zai kai Nigeria zagayen gaba idan har Iceland ba ta ci Croatia ba.
    • Da zarar Argentina da Nigeria suka yi canjaras to Iceland za ta kai wasannin zagaye na biyu idan har ta doke Croatia da kwallo biyu.
    • Argentina za ta kai zagaye na biyu idan har ta doke Nigeria, sannan Iceland ta kasa nasara a kan Croatia. sai dai idan Iceland ta ci Croatia, Argentina za ta iya kai wa zagayen gaba idan ta yi nasara a kan Nigeria da kwallo biyu ko fiye da haka.
    • Idan kuma Argentina da Iceland suka ci wasansu da yawan kwallaye iri daya, to za a duba kungiyar da ta fi karbar katin gargadi don fayyace ta biyu.
    • Argentina ta karbi katin gargadi uku, ita kuwa Iceland ba ta da ko daya.
  9. 'Kar Najeriya ta mayar da hankali a kan Messi'

    Tsohon dan wasan Najeriya Sani Kaita ya ce kada 'yan wasan kasar su mayar da hankalin su kacokan a kan shahararren dan kwallon Argentina Lionel Messi.

  10. Ko Messi zai taka rawar gani?

    Lionel Messi daya daga manyan 'yan wasan kwallon kafa na duniya da ake sa ran zai haskaka a wasannin da ake yi a Rasha, sai dai ya buga kwallo zuwa mai tsaron raga sau 22 amma bai ci kwallo ba.

    Shin ko zai taka rawar gani a karawa da Nigeria?

  11. Labarai da dumi-dumi, Nigeria v Argentina

    Argentina za ta buga salon wasa na 4-4-2, kuma an ajiye Sergio Aguero da kuma Willy Caballero, yayin da Gonzalo Higuain da Angel di Maria da kuma Marcos Rojo za a fara wasa da su.

    Haka kuma Franco Armani zai tsare ragar Argentina a wasan farko da zai yi wa tawagar..

    Ita kuwa Nigeria za ta yi amfani da 'yan wasan da suka doke Iceland 2-0.

  12. Dakin sauya kayan 'yan wasan Najeriya

    Dakin sauya kayan Super Eagles gabanin fara wasansu da Argentina.

  13. 'Yan wasan da za su fara taka leda a wasan

    Jerin 'yan wasan da za su taka wa Najeriya da Argentina leda.

  14. Za a sake sanfarin kwallon da za a buga a zagaye na biyu

    Hukumar kwallon kafa ta duniya ta ce za ta sake sanfarin kwallon da za a buga a wasan zagaye na biyu a gasar cin kofin duniya da ake yi a Rasha.

    Ana buga kwallon Telstar 18 a wasannin rukuni, inda a ranar Asabar za a fara fafatawar zagaye na biyu, inda za a yi amfani da kwallo mai suna Telstar Mechta.

    Machta a harshen Rasha na nufin "mafarki" kuma tamaular na dauke da launin ja da yake nufin yadda gasar za ta dauki dumi tsakanin kasashe 16 da za su buga wasannin gaba.

  15. Abubuwa 5 da Najeriya ke bukata don doke Argentina

    Najeriya da Argentina za su fafata a wasansu na karshe na rukunin D na gasar cin kofin duniya ta Rasha 2018.

    Wasan shi ne zai tantance makomar kasashen biyu a gasar, kuma hankalin masu kaunar kwallon kafa a duniya ya karkata a kansu.

    Sai Argentina ta doke Najeriya, san nan Croatia ta ci Iceland ko kuma sun tashi canjaras, san nan Argentina za ta samu zuwa zagaye na gaba.

    Najeriya kuma na bukatar ta doke Argentina ko kuma ta tashi canjaras da ita, sannan ta yi fatan kada Iceland ta yi nasara a kan Croatia domin zuwa zagaye na gaba.

    Latsa nan don karanta abubuwan da ake ganin ya kamata 'yan Super Eagles su yi domin samun nasara:

  16. Ahmed Musa ya ci kwallo biyu

    Ahmed Musa shi ne ke gaba wajen ci wa Nigeria kwallo a gasar da ake yi a Rasha, bayan da ya ci Iceland kwallaye biyu.

  17. Ba ma jin tsoron Messi – Super Eagles

    Dan wasan Najeriya Abdullahi Shehu ya ce su ba sa jin tsoron shahararren dan wasan Argentina Lionel Messi.

  18. Peru ta doke Australia

  19. Faransa ta buga kunnen doki da Denmark

  20. Yadda rukuni na hudu ya kasance kafin wasa na uku-uku

    Croatia ta kai wasan zagaye na biyu kai tsaye, yanzu ya rage wadda za ta kai zagaye na biyu tsakanin Nigeria ko Iceland ko kuma Argentina,.