Najeriya 1-1 Argentina
Argentina ta kai wa Najeriya mummunan hari amma mai tsaron bayan Najeriya ya tura kwallon kwana.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Argentina ta fitar da Najeriya daga Gasar Cin Kofin Duniya bayan ta doke ta da ci 2-1 a ranar Talata.
Argentina ta kai wa Najeriya mummunan hari amma mai tsaron bayan Najeriya ya tura kwallon kwana.
Najeriya ta kai wawan hari. Sai dai masu tsaron bayan Argentina sun fitar da kwallon.
Argentina ta samu bugun tazara amma kwallon ta fita.
Najeriya ta samu bugun tazara amma kwallon ta fita.
Najeriya ta sake kai wa Argentina hari.
Victor Moses ya ci wa Najeriya kwallo daga bugun fanariti.
Najeriya ta samu bugun fanerati.
Argentina ta kai wa Najeriya hari amma masu tsaron bayan Najeriya sun dakile kwallon.
An dawo hutun rabin lokaci.
Ana shirye-shiryen dawo daga hutun rabin lokaci.
Yadda kasashen biyu suka murza-leda a tsakanin su.
An tafi hutun rabin lokaci.
Saura minti biyu a tafi hutun rabin lokaci.
Luka Modric na taka rawar gani amma har yanzu babu ci a karawar da yake yi da Iceland.
Najeriya ta kai wa Argentina hari amma an fitar da kwallon.
Argentina na farin ciki da wannan sakamakon, kuma idan aka tashi wasa a hakan ga yadda teburi zai zama.
Najeriya ta kai wa Argentina hari amma golansu ya fitar da kwallon.
Saura minti shida a tafi hutun rabin lokaci
Argentina ta sake kai wa Najeriya mummunan hari amma masu tsaron bayan Najeriya sun dakile kwallon.