Sai wani lokaci, Najeriya 1-2 Argentina
A nan muka kawo karshen sharhin da muke kawo maku game da wasan Najeriya da Argentina.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Argentina ta fitar da Najeriya daga Gasar Cin Kofin Duniya bayan ta doke ta da ci 2-1 a ranar Talata.
A nan muka kawo karshen sharhin da muke kawo maku game da wasan Najeriya da Argentina.
Croatia da Argentina daga rukunin D za su je zagaye na gaba na Gasar Cin Kofin Duniya wadda ake yi a kasar Rasha. Croatia ta doke Iceland da ci 2-1 a dayan wasan rukunin D.
Najeriya ta samu maki uku ne kuma matsayi na uku a rukunin D, abin da ya fitar da ita daga Gasar Cin Kofin Duniya a kasar Rasha.
An tashi wasa Argentina ta cire Najeriya daga Gasar Cin Kofin Duniya.
Saura minti hudu a tashi wasan.
Argentina ta kara wa Najeriya kwallo ta biyu.
Najeriya ta samu bugun tazara, amma kwallon ta fita waje.
Argentina ta kara samu bugun kwana amma Najeriya ta dakile kwallon.
Wasa yana kara yin zafi, inda kasashen biyu suke kai wa juna munanan hare-hare.
Najeriya ta kusa kara samun bugun fanariti amma alkalin wasa ya ki bayarwa.
Najeriya ta kai wa Argentina wani wawan hari, sai dai kwallon ta fita waje.
Argentina sake kai wa Najeriya hari ta hannun Messi, amma Ahmed Musa ya dakile kwallon.
Wasa ya kara dawo wa sabo,inda duka bangarorin kowa yake kai wa kowa hari.
Yadda teburi ya koma idan aka tashi wasa haka.