Kayatattun hotunan Afrika: Daga 1 zuwa 31 ga Satumba

An wallafa

Wasu daga cikin zaɓaɓɓun hotuna daga Afrika da na ƴan Afrika daga wasu sassan duniya

A ranar Litinin, Sojoji sun gudanar da fareti domin karrama Janar Brice Nguema lokacin bikin rantsar da shi a matsayin shugaban riko na Gabon a Libreville.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Litinin, Sojoji sun gudanar da fareti domin karrama Janar Brice Nguema lokacin bikin rantsar da shi a matsayin shugaban riko na Gabon a Libreville.
Wani ɗan ƙabilar maasai ya isa taron sauyin yanayi na Afirka a Nairobi ƙasar Kenya

Asalin hoton, Monicah Mwangi/Reuters

Bayanan hoto, Wani ɗan ƙabilar maasai ya isa taron sauyin yanayi na Afirka a Nairobi ƙasar Kenya
A wajen taron a ranar Litinin, masu fafutikar kare muhalli sun yi gangami tare da kira ga mahalarta taron su ɗauki mataki na daƙile gurɓatacciyar iskar masana'antu da ke haifar da ɗumamar yanayi

Asalin hoton, Suleiman Mbatiah/AFP

Bayanan hoto, A wajen taron a ranar Litinin, masu fafutikar kare muhalli sun yi gangami tare da kira ga mahalarta taron su ɗauki mataki na daƙile gurɓatacciyar iskar masana'antu da ke haifar da ɗumamar yanayi
Wannan nau'in tsusa na daga cikin abubuwan da aka nuna a wajen taron

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wannan nau'in tsusa na daga cikin abubuwan da aka nuna a wajen taron
Yayin da kuma wata manomiya ƴar Tunisia ke cire tattasai a gona a ranar Talata

Asalin hoton, Mohamed Messara/EPA

Bayanan hoto, Yayin da kuma wata manomiya ƴar Tunisia ke cire tattasai a gona a ranar Talata
A ranar Litinin gwamnatin jihar Legas cibiyar kasuwancin Najeriya ta kaddamar da sufurin jirgin kasa a tashar Marina

Asalin hoton, Pius Utomi Ekpei/AFP

Bayanan hoto, A ranar Litinin gwamnatin jihar Legas cibiyar kasuwancin Najeriya ta kaddamar da sufurin jirgin kasa a tashar Marina
Masu jimami a kusa da ƙaburburan da aka yi wa jana'iza wadanda gobara ta kashe a ranar Lahadi a Johannesburg, Afirka ta Kudu.

Asalin hoton, Siphiwe Sibeko/Reuters

Bayanan hoto, Masu jimami a kusa da ƙaburburan da aka yi wa jana'iza wadanda gobara ta kashe a ranar Lahadi a Johannesburg, Afirka ta Kudu.
Lauyoyi sun halarci sauraren ƙarar sojoji shida da ake tuhuma da aikata laifukan take haƙƙin ɗan adam a wata kotun soji a Jamhuriyyar Dimoƙuradiyyar Congo a ranar Laraba

Asalin hoton, Alexis Huguet/AFP

Bayanan hoto, Lauyoyi sun halarci sauraren ƙarar sojoji shida da ake tuhuma da aikata laifukan take haƙƙin ɗan adam a wata kotun soji a Jamhuriyyar Dimoƙuradiyyar Congo a ranar Laraba
Dubban mutane sun halarci bikin rantsar da shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ranar Litinin

Asalin hoton, Tafadzwa Ufumeli/Getty Images

Bayanan hoto, Dubban mutane sun halarci bikin rantsar da shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ranar Litinin
Mata a Addis Ababa, suna aikin haɗa biredin injera a ranar Juma'a

Asalin hoton, Amanuel Sileshi/AFP

Bayanan hoto, Mata a Addis Ababa, suna aikin haɗa biredin injera a ranar Juma'a

Dukkanin hotuna suna da haƙƙin mallaka