Abin da wasu ƴan Najeriya ke cewa kan yajin aikin masu burodi

Asalin hoton, Getty Images
Wasu ƴan Najeriya na nuna damuwa kan halin da suke ciki ganin za su kara fadawa na wahalar rayuwa sakamakon barazanar da wata kungiya ta masu yin burodi ta yi cewa za ta shiga yajin aiki saboda tsadar kayan yin burodi.
Kungiyar ta Master Bakers and Caterers ta ce mambobinta a fadin kasar har ma wadanda ba 'yan kungiyar ba ne za su shiga yajin aikin wanda zai fara daga ranar Alhamis, 21 ga watan Yulin 2022, har sai abin da hali ya yi.
Shugaban kungiyar reshen Abuja, Ishaq Abdul-Raheem, ya ce sun dade suna daurewa da halin tsadar kayan da suke ciki, da zummar za su samu sauki a gaba, to amma abin kullum sai kara gaba yake.
Dangane da wannan lamari dai, ƴan ƙasar na ci gaba da muhawara a shafukan sada zumunta inda akasari suke kuka da tsadar burodin.

Hassan Saeed dai yana nuni ne da irin matsanancin halin da yake ganin 'yan kasar ta Najeriya na ciki, na tamkar gaba kura baya sayaki.
Abin da hakan ke nuni kuwa shi ne irin matsanancin halin rayuwa da 'yan kasar suke ciki tare da ganin cewa babu wata mafita, illah Allah Ubangiji ya samar da sauki, daga wuyar da ake ciki ta rayuwa a Najeriyar, kamar yadda ya bayyana.
Wasu kuwa duk da cewa masu yin burodin sun ce za su tafi yajin aikin ne, saboda tsadar kayan aiki, roko suke yi ga 'yan kungiyar a kan kada su aiwatar da barazanar tasu.
Mutane irin su Ali Bello Alhaji, masu wannan ra'ayin har wa yau na mayar da al'amarin zuwa ga Ubangiji, domin samun ɗauki ga yadda al'amura ke kasancewa a Najeriyar da ma duniya baki daya.

Wasu kuwa irin su Abdullahi Laki Funtua na ganin idan har yajin aikin zai kasance wata hanya ta samun sauki ga tsadar kayayyakin da ake ciki wadda a karshe za ta iya kaiwa ga samun saukin farashin suna goyon baya.

Ganin cewa a Najeriya, a wani lokaci akan shiga yajin aiki wanda hakan ke janyo karancin wani kayan masarufi ko wani abu na rayuwar yau da kullum kamar man fetur da dangoginsa, inda kuma daga bisani sai ya samu amma da karin farashi, wasu 'yan kasar na ganin yajin aikin na masu burodi wata hanya ce ta neman kara farashinsa, kamar yadda Abubakar Sani Gummi ke nuni.

Burodi cimaka ce ga yawancin 'yan Najeriya masu karamin karfi da ma masu hali. Sai dai a ce irin burodin da yawanci talakawa ke ci ya bambanta da na masu hali, wato kamar abin nan da akan ce ''iya kudinka iya shagalinka.''
Sanin muhimmancin burodin ya sa wasu ke rokon 'yan kungiyar masu yin burodin da su yi hakuri kada su tafi yajin aikin. To amma anya kuwa wannan roko zai samu karbuwa kuwa ganin cewa masu sana'ar sun ce hatta uwar-kudi ma rasa ta suke ballantana riba? Ga dai rokon da wani dan Najeriyar ke yi a shafin Twitter na BBC Hausa:
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Yanzu dai abin jira a gani shi ne yadda daga ranar Alhamis 21 ga watan nan na Yuni, 2022, wannan barazanar yajin aiki ta masu gidajen burodi a Najeriya za ta kasance.
Za a ga yadda rayuwa za ta kasance ga wadanda ke amfani da burodi da su kuma masu gidajen burodin, da uwa uba gwamnati kan yadda za a tunkari wannan lamari.
Walau, karin farashin burodin ko kuma dakatar da yinsa. Amma dai abu ne mawuyaci a ce an kai ga dakatar da yin burodin na wani lokaci mai tsawo gainin yadda rayuwar al'umma da dama ta ta'allaka a kansa.











