Rishi Sunak ya lashe zagayen farko na zaben shugaban jam'iyyar Consevative

Asalin hoton, Reuters
Tsohon sakataren baitulmalin Birtaniya Rishi Sunak ya lashe zagayen farko na zaben da aka yi domin samar da shugaban jam'iyyar Conservative kuma firaministan kasar.
Ya sami kuri'a 88, inda ministar ciniki Penny Mordaunt ta zo ta biyu da kuri'a 67, ita kuma sakatariyar harkokin waje Liz Truss ta zo ta uku da kuri'a 50.
Sai dai Nadhim Zahawi, wanda shi ne sakataren baitulmali mai ci da tsohon sakataren ma'aikatar lafiya Jeremy Hunt ba su kai labari ba.
Za a sake zubawa tsakanin wadannan mutum hudun da sauran 'yan takarar a ranar Alhamis.
Zuwa karshen makon gobe, ana sa ran rage yawan 'yan takarar, sannan mambobin jam'iyyar ta Conservative kimanin 160,000 za su yanke hukunci kan dan takarar da yafi dacewa ya zama shugabansu, ya kuma zama firaministan Birtaniya.
Ranar 5 ga watan Satumba za a sanar da sakamakon zaben na karshe.
Sauran 'yan takarar sun koma neman goyon bayan masu zaben da a baya suka mara wa Mista Hunt da Mista Zahawi.
Mista Hunt ya shaida wa BBC cewa shi zai mara wa Mista Sunak ne daga yanzu.

Mista Sunak, wanda ya sauka daga mukaminsa a makon jiya yayin da ya nuna rashin goyon bayansa ga rashi iya mulkin Boris Johnson, ya shida wa BBC cewa yayi murna da wannan sakamakon zaben.
Ita ma Ms Mordaunt ta bayyana gamsuwarta da rawar da ta taka.

Asalin hoton, Reuters











