Zaben 2023: Yadda waka ke tasiri a siyasar Najeriya

An wallafa

A Najeriya, mawaka na da matsayi na musamman a cikin harkokin siyasar kasar, sakamakon rawar da suke takawa wajen tallata manufofin jam`iyya da na `yan takara.

Tun daga  jamhuriya ta farko ake tafiya da su, kuma har yanzu ba a yar da su ba.

Kamar kowace kakar zabe a Najeriya za a iya cewa gari ya waye domin mawaka sun fara baje-kolinsu.

Yawanci a cikin wakokinsu mawakan kan yi yabo ga gwanayensu ko gugar-zana ga abokan hamayya.

Kuma waka na yin tasiri sosai ga masu neman mukami a siyasa, saboda a wasu lokutan mutane na zaben mutum ne saboda yadda wakar da aka rera masa ta ja hankalinsu.

Masana harkokin siyasa a Najeriya sun bayyana cewa dangantakar da ke tsakanin mawaka da `yan siyasa, dangantaka ce ta jini da tsoka.

Dakta Abubakar Kari, masanin siyasa ne a jami`ar Abuja da ke Najeriya, ya shaida wa BBC cewa wakoki na saurin karbuwa a tsakanin matasa samari da kuma masu kananan shekaru.

Ya ce "wakoki irin na siyasa bugu da kari tattare suke da kade-kade da bushe-bushe da kuma raye-raye, sannan ga zambo da kirari, shi yasa 'yan siyasa ke zakewa a kan cewa sai an yi musu wakoki."

Dr Kari ya ce irin wadannan wakoki na da tasiri kwarai da gaske, ta yadda za a ga ana ta rerasu a tsakanin jama'a.

Duk da cewa mawakan na matukar kaunar jam`iyyunsu, a cewar masanin kaunar ba ta hana wasu mawakan su juya wa jam`iyya ko gwanin nasu baya idan suka hangi kamar an sake hanya.

Masanin siyasar ya ce yawancin mawakan siyasar na fama da rashin akida.

Ya ce," Da dama daga cikin wadannan mawaka 'yan kasuwa ne domin kudi suke nema musamman ma a wannan jamhuriya."

Dr Kari ya kara da cewa a baya yawancin mawakan siyasa musamman ma na jamhuriya ta daya data biyu mutane ne masu akida, to amma a wannan jamhuriya yawancin mawakan siyasar ana daukarsu haya ne.

Ya ce" to shi yasa zaka ga mawaki guda ya yiwa 'yan takara da dama waka wani lokaci ma har da abokan hamayya."

Tun daga jamhuriya ta farko mawaka ke tallata jam`iyyum siyasa da `yan takara har zuwa yanzu, kuma alamu na nuna cewa za su ci gaba da samun tagomashi.