Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Asakaa: Yadda wani sabon salon waka ya karbu a kasar Ghana
- Marubuci, Daga Lanre Ogundimu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Kumasi
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 3
A yayin da ake tsaka da barkewar annobar korona, wani mawaki da ke zaune a Birtaniya ya hau jirgi zuwa Ghana domin hada gwiwa da wani yaro dan makaranta don yin wata waka wadda ke nuna sabon salon waka a Afirka. Wakar, mai suna Sore, da Yaw Tog, matashi mai shekara da Stormzy suka yi ta karbu sosai a YouTube inda fiye da mutum miliyan shida suka kalle ta.
Salon wakar Asakaa na Ghana shi ne ke tashe yanzu a Afirka kuma tana fatan zai samu karbuwa irin wadda salon wakar Afrobeats na 'yan Najeriya da salon wakar amapiano ta Afirka ta Kudu suka samu a duniya.
Salon wakar na Asakaa ya hada da irin wakokin Ghana da wani bangare na salon wakar gambara da ake yi a Amurka da kuma amfani da karin-harshen Twi.
Daya daga cikin masu son irin wannan salo na waka shi ne, marigari Virgil Abloh, dan kasar Ghana mazaunin birnin Chicago, a cewar mawaki Kwaku DMC.
Lokacin da darakta a kamfanin yin tufafi na Louis Vuitton kuma makusancin Kanye West ya ga bidiyon salon wakar asakaa mai suna Suzy a shafukan sada zumunta, ya wallafa shi a shafinsa na Instagram sannan ya ja hankalin Kwakwu DMC.
"Na tashi da safe inda na yi karo da sakonnin, sakonni da dama suka shigo min, kamar me ke faruwa. Shin an yi min kutse ne ko wani abu daban?" yana iya tunawa. "Sai na garzaya akwatin sakona sai kawai na ga ashe Virgil ta ambato suna na."
Kwaku DMC shi ma ya bi Abhol, wanda ya fada masa cewa wakar ta "karbu sosai" kuma wai ya yi farin ciki ganin matashin ɗan Ghana da irin wannan wakar". Kuma ya ce zai yi duk mai yiwuwa wajen taimaka wa wakar da soma aiko min da tufafi da takalma.
Mawaki da ke tasowa Jay Bahd na da yaƙinin asakaa na daya daga cikin wakokin matasa da ke tasowa da za su ba da mamaki daga Ghana, kuma wannan fata ba boyayya ba ne.
Manhajar sauraron wakoki da ke mayar da hankali kan kasuwar Afrika, Boomplay, ya ce wakokin da ake nunawa kauna na Yow Tog da Jay Bahd na cikin wakoki 20 da aka fi saurara.
Wakar tasu ta karade yankuna da dama kama daga Amurka da Burtaiya da Jamus.
Sai dai amfani da yarensu shi ne abin da ya sa wakarsa ta yi fice kuma ta bambanta.
Sunan kadai abu ne da mutane ke nunawa soyayya a duniyar wakoki.
Kalmar "magana da harshen Twi shi ne "kasa", kuma asakaa ya yi amfani da ita sosai.
Makadi kuma mai shirya waka Rabby Jones shi ya zo da kalmar. Yana tukin mota cikin tsakiyar dare tare da wasu mawaka daga Kumasi babban birnin Ghana, na yankin Ashanti.
"Mun saki kida irin na zamani, kuma Jay Bahd ya kasance wanda yake gambara. Na yi ihu na ce: Asakaa. Nan da nan abin ya zo min kuma muka ci gaba a haka, a cewarsa.
Duk da cewa asalinsa ba mawakin asakaa ba ne, amma yakan bambanta kansa da salon kida Ghana da Birtaniya.
An sake haifo asakaa a yankunan makwabtan Kumasi kuma abin ya karade ko ina a kasar.
Duk da cewa wannan salon wakar ya karbu a yammacin Ghana, wannan abu ne da matasa mawaka da masu shirya wakoki a Kumasi ke kokarin sake karfafawa, suna tabo yadda sautin kidan ya samu cigaba tun daga 2020.
"Ba su da masaniya sosai kan abin da ya kamata su yi," a cewar mawakin gambara O'Kenneth.
"Amma duniya ta karɓi wannan salon wakar da kida a cewar O'Kenneth, wanda ya soma daukar hankali har a shafukan sada zumunta saboda litattafansa da hadin-gwiwar da ya da Kumerica a Agustan 2020.
Duk da cewa muryarsa ta bambanta a zahiri, a lasifika murya na da tausasawa.
Yana kaunar kasarsa, Ghana, amma ya fi samun karbuwa a Turai, kuma yana samun habaka a duniya.
Tsattsauran yanayin al'ummar Kumasi na nuna cewa har yanzu akwai mutanen da ba su rungumi akidar asakaa ba.
O'Kenneth na fahimci cewa akasarin masoyansa sun fito ne daga yammaci.