Kasuwar yan kwallo: Makomar Richarlison, Gordon, Bellingham, Salah, Martinez da kuma Dembele

Richarlison

Asalin hoton, Reuters

An wallafa

Tottenham da abokiyar hamyyarta Chelsea da dukansu ke zaune a birnin London na gagayya da juna domin daukar dan wasan gaban Everton Richarlison, mai shekaru 25. (Sky Sports)

Sai dai Everton ta sanar cewa ba ta shirya sayar da dan wasan tsakiyarta Gordon ba ga kowace kungiya. (Liverpool Echo)

Spurs na kuma kan gaba wurin kokarin sayen dan wasan bayan Barcelona Clement Lenglet, duk da Roma ma na son kulla ciniki kanshi. (London Evening Standard)

Ita kuwa Real Madrid ta ce babu dan wasan da take son kawowa kaka mai zuwa kamar matashin dan wasan Ingila Jude Bellingham da ke wasa a Borrussia Dortmund. (AS, via Mail)

Chelsea na son yi wa 'yan wasan Manchester City Raheem Sterling da Nathan Ake cinikin goro don kara wa gaba da bayansu karfi. (Telegraph - subscription required)

Ana sa ran dan wasan gaban Liverpool Mohamed Salah ya bar kungiyar idan kwantiraginsa ta kare a karshen kakar da ke tafe. (Mirror)

Salah

Asalin hoton, Getty Images

Arsenal kuwa ta mika tayin fam miliyan 35 ga Ajax, don sayen dan wasan bayanta Lisandro Martinez, duk da Manchester United ma ta nuna sha'awar daukarsa. (Mirror)

Anan kuma United din na fatan kammala cinikin daukar dan wasan tsakiyar Barcelona Frenkie de Jong, da kuma na Denmark Christian Eriksen, kafin su kuma mai da hankali wurin dauko dan wasan gaban Ajax, Antony. (Times - subscription required)

To amma jaridar (Mirror) ta ce babu tabbas ko United na iya daukar Antony a yanzu, bayan da Ajax ta nemi fam miliyan 70 kansa.

Ita kuwa Newcastle na dab da kammala cinikin mai tsaron bayan Lille Sven Botman kan fam miliyan 32, don mayar da hankali kan buda cinikin dan wasan gaban Reims Hugo Ekitike duk dai a Faransa. (Mail)

Ana hasashen PSG za ta nada Christophe Galtier a matsayin sabon koci don maye gurbin Mauricio Pochettino, wanda ake sa ran ya bar kungiyar duk da lashe kofin gasar League 1. (ESPN)

Barcelona ta shirya kyale Ousmane Dembele ya bar kungiyar, idan kwantiraginsa ta kare a ranar 30 ga watan Yuni. Tuni Bayern Munich da Chelsea da kuma PSG suka nuna sha'awar kulla yarjejeniya da shi.(Marca)