Girgizar kasa a Afghanistan: Mutane akalla 920 sun mutu, wasu da dama sun jikkata
- Marubuci, Daga Frances Mao & Matthew Davis
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- An wallafa
Wata gagarumar girgizar kasa da ta faru a Afghanistan ta yi sanadin mutuwar akalla mutum 920 sannan da dama sun jikkata, a cewar shugaban addinin kasar.
Hotuna sun nuna yadda kasa take zaftarewa sanna ta lalata gidajen-kasa a lardin Paktika da ke gabashin kasar, inda masu aikin ceto suke can suna yi wa wadanda suka jikkata magani.
A wuraren da ke da wahalar zuwa, an aike da jiragen helikwafta domin dauko wadanda suka jikkata don a kai su asibit.
Shugaban Taliban Hibatullah Akhundzada ya ce daruruwan mutane sun lalace kuma mai yiwuwa mutanen da suka mutu za su karu.
Wani babban jami'in Taliban - mataimakin minista kan kare aukuwar bala'i - Sharafuddin Muslim ya shaida wa manema labarai cewa mutum 920 ne suka mutu sannan wasu 600 suka jikkata.
Ita ce girgizar kasa mafi muni da ta auka wa kasar a shekaru ashirin.
Girigizar kasar ta faru ne a yankin da ke da nisan kilomita 44km daga birnin Khost da ke kudu maso gabashin Afghanistan da misalin karfe daya da rabi na dare a agogon kasar, yayin da mutane ke tsaka da barci.
Girgizar kasa tana yawan haddasa gagarumar matsala a Afghanistan, inda ake da yankunan karkarar da mutane suka gina gidajen-kasa.


Afghanistan: Abubuwan da suka kamata ku sani
- Gwamnatin Taliban ce take gudanar da mulkin kasar: Kungiyar mai kaifin kishin Musulunci ta kwace iko da kasar ta Afghanistan, kusan shekara 20 bayan gamayyar da sojojin Amurka ke jagoranta ta tumbuke su
- Tattalin arzikinta yana tsaka-mai-wuya: Yayin da dakarun Amurka suka fice daga kasar, kasashen waje da ke ba ta tallafin kudi sun fice daga Afghanistan sannan an rufe asusanta da ke kasashen waje
- Akwai matsalar jinkai: Bankin Duniya ya ce fiye da kashi uku cikin hudu na 'yan kasar ba sa iya samun abubuwan biyan bukatun yau da kullum irin su abinci.

Jami'an Taliban sun yi kira ga ma'aikatan bayar da agaji su yi gaggawar zuwa yankunan da girgizar kasar ta auka wa.
Shekaru aru-aru da aka kwashe ana rikici a kasar sun sa kasar ta fada cikin mummunan yanayi yadda ta gaza inganta tsarin kare kanta daga girgizar kasa da wasu masifu - duk da kokarin da hukumomin bayar da agaji suka kwashe tsawon shekaru suna yi domin inganta wasu gine-gine.
Tun ma kafin kungiyar Taliban ta karbe iko da kasar, kungiyoyin agajin Afghanistan ba su da karfin shawo kan bala'o'i kamar girgizar kasa - ba ta da jiragen kai agaji masu yawa.

Asalin hoton, @Alham24992157
Galibin wadanda lamarin ya rusta da su suna yankunan Gayan da Barmal da ke lardin Paktika, a cewar wani likita da ya yi hira da BBC. Kafar watsa labarai ta Etilaat-e Roz ta rawaito cewa wani kauye a yankin Gayan ya rushe gaba daya.
An ji karar girgizar kasar a nisan kilomita 500 daga Afghanistan, wato a kasashen Pakistan da India. Wasu sun bayar da labarin jin karar girgizar kasar a Kabul, babban birnin kasar, da kuma Islamabad, babban birnin Pakistan.












