Ku San Malamanku tare da Musa Alqasiyuni Sheikh Nasiru Kabara

An wallafa

Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon hira da Malam Musa Alqasiyuni:

Malam Musa Alqasiyuni, ɗa ne ga marigayi Sheikh Nasiru Kabara. An haife shi a unguwar Kabara da ke birnin Kano a raewacin Najeriya. Ya soma karatun allo a wurin marigari Malam Abbas a birnin na Kano.

Daga bisani an saka shi a makarantar Islamiyya da ke Gidan Kadariyya kuma daga bisani ya shiga makarantar Ma'aduddeen inda ya kammala ta a 1979. A shekarar ce kuma ya shiga makarantar Sakandare ta Aliyah da ke Unguwar Shahuci inda ya kammala a 1983.

Daga nan ne Malamin ya shiga Jami'ar Bayero da ke Kano, inda ya yi difiloma kuma bayan ya kammala ne ya soma koyarwa a 1987. A 1989 ya samu aikin koyarwa a ma'aikatar Ilimi ta Jihar Kano, inda kuma ya koma Jami'ar Bayero domin yin Digiri a kan Harshen Larabci.

Kazalika ya yi Digiri na Biyu a dai Harshen Larabci.

Malam Musa Alqasiyuni ya bayyana cewa ya yi kiusan dukkan karance-karancensa na addini da harshen Larabci a wurin mahaifinsa marigayi Sheikh Nasiru Kabara.

"Cikin hukuncin Allah, ni ban fadada wuraren karatu ba. Karatu dai da za a je gaban wani malamai a dauke shi, ban gurfana gaban wani malami ba sai shi mahaifina Sheikh Muhammad Nasiru Kabara.," in ji Malam Alqasiyuni.

Wani abu da malamin ya yi fice a kansa shi ne karatun Ashafa, wanda ya ce mahaifinsa ya umarce shi da ya rika jagorantar mutane tun daga shekarar 1990.

Ya kara da cewa akwai matukar shakuwa tsakaninsa da mahaifinsa domin kuwa ko da abinci ba ya iya ci sai a wurinsa, yana mai cewa "har ta kai lokacin da na yi wayo babu abin da yake raba ni da malam sai barci."

'Farin cikin da ba zan manta da shi ba'

Malam Alqasiyuni ya ce abubuwa da dama na farin ciki sun faru a rayuwarsa kuma daya daga cikin su shi ne "lokacin da malam ya nemi na raka shi aikin Hajji a matsayin dan rakiyarsa. Wannan shi ne aikin Hajjina na farko bayan na yi wayo."

Ya ce daga cikin abubuwan bakin cikin da ba zai taba mantawa da shu ba har da rasuwar mahaifi da mahaifiyarsa.

A cewarsa: "Na girgiza matuka lokacin da Malam (Sheikh Nasiru Kabara) ya rasu, kuma na yi matukar girgiza - watakila wadda ta fi waccan - lokacin da mahaifiyata ta rasu. Girgiza ta uku ta bakin ciki da ya faru da ni ita ce rasuwar dan uwana kanena, Malam Aliyyul Khawwas."

Malamin ya ce babu abin da yake sanya shi farin ciki kamar ganin kawunan kungiyoyin addini sun hadu a kan wani batu.

Iyali

Malam Alqasiyuni yana da aure inda yake da mata biyu da 'ya'ya tara.

Daga cikin 'ya'yansa, akwai mata biyar da maza hudu.

'Abincin da ba na so'

Malamin ya ce ya fi son cin shinkafa, amma ba ya son tuwon dawa.

"Babu abincin da na ki jini kamar tuwon dawa. Na taso a gidanmu kullum da daddare tuwon dawa ake yi, da rana mafi yawa a yi tuwon masara. Wata rana a yi tuwon shinkafa ko shinkafa da miya ko shinkafa dafa-duka. Allah ya sa ba na son tuwon dawa; kulum sai dai ita mahaifiyarmu ta dafa mini shinkafa," in ji shi.