Zanga-zangar adawa da 'cin zalin da Rwanda ta yi' da ƴan mata masu nishaɗi a hotunan Afirka na mako: 10-16 June 2022

An wallafa

Kayatattun Hotunan Afirka na wannan makon:

Short presentational grey line
A man gestures while sitting above harvested bales of wheat packed in the back of a pickup truck in a field in the Sidi Thabet region near Ariana north of the capital Tunis on June 13, 2022.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A Tunisa, yanzu Lokacin girbi ne, inda a nan manoma ne ke dakon alkama a ranar Litinin.
A demonstrator gestures as with others tries to reach the border between Democratic Republic of Congo and Rwanda during a protest in Goma on June 15, 2022. Several thousand people demonstrated on Wednesday in Goma, on the border with Rwanda, in the east of the Democratic Republic of Congo (DRC), to denounce "Rwandan aggression" and express their support for the Congolese army, in a context of maximum tension between Kinshasa and Kigali.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wasu masu zanga-zanga kenan a Kongo ranar Laraba, ke yin Alla-wadai kan 'cin-zalin kasar Rwanda' a yayin da kasashen biyu ke zargin juna na baiwa 'yan tawaye wurin zama dai-dai lokacin da dangantaka ke kara tsamari tsakanin su.
The members of the "Happy girls" netball team take part in a practice session at Katlehong township, south-east of Johannesburg.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Juma'a a garin Katlehong na Afirka ta Kudu, kungiyar kwallon kwando ta mata na wasa a tsakaninsu.
Members of the DHL Stormers Dancers practise their dance routines, at a church hall, in Cape Town.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A birnin Cape Town ranar Alhamis, wasu masu wasan zari-ruga na atasaye gabanin wasan da za su yi na gasar zari-ruga a ranar Asabar.
A boy takes a nap while lying on a carpet and sheltering from the sun.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A can N'Djamena da ke Chadi kuwa, wani yaro ne ke barci a wani sansani na makiyaya a ranar Juma'a. Makiyaya masu kaura da yawa ne ke jajircewa domin sauyin yanayi wanda ke kawo karancin ciyawa da ruwa ga dabbobinsu - inda hakan ke haddasa rikice-rikice tsakanin su da al'ummomi.
Child refugees from the Democratic Republic of Congo (DRC) play on on swings at the Nyakabande Transit Center in Kisoro, Uganda.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A dai ranar Juma'a, yara na wasa a kan lilo a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke iyakar garin Kisoro na kasar Uganda.
South Sudanese asylum seeker Nyalada Gatkouth Jany who tried to cross the Mediterranean Sea four times and went into prison in Libya, gets her hair cut at Gashora Emergency Transit Centre in Gashora, Rwanda.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Juma'a a Rwanda, wani mai neman mafaka dan kasar Sudan, Nyalada Gatkouth Jany, na duba kyawunta da madubi.
Supporters of the Economic Freedom Fighters (EFF) political party, sing and dance at the Makwarela stadium in Limpopo.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Alhamis a lardin Limpopo na Afirka ta Kudu, masu goyon bayan jam'iyyar adawa ta EFF na rawa da rera wakoki a wani bikin tunawa da shekara 46 bayan zanga-zangar dalibai bakaken fata da aka yi wa lakabi da 'soweto'.
Moonchild Sanelly on stage with Gorillaz in Vienne, France.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A nan, mawakiyar Afirka ta Kudu ce Moonchild Sanelly ke rawa da takwararta ta Birtaniya Gorillaz a kasar Faransa.
A composite of Lotfi Bouchnak in traditional costume during a studio photoshoot.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Duk dai a ranar, shahararren mawakin kasar Tunisia, Lofti Bouchnak na tsaye domin daukar hoto a Tunis, babban birnin kasar.
Fazil Omar Senior high school students play the "enter ball" game as the game developer Oluwaseun Sanni directs a game session during a time-out in Lagos' Iwaya community. The game is played with dice and two cowrie shells on a board.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A jihar Lagos, wani dalibi, Oluwaseun Sanni na nuna wa 'yan uwansa dalibai na makarantar sakandari yadda ake yin wasan kwallo na teburi a ranar Laraba.
Senegalese activist Modou Fall, called the plastic man, president of the association Senegal Propre at the entrance of Pikine, a suburb in Dakar.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Duk dai a ranar a Dakar, Modou Fall, mutumi da ke sanye da rigar ledoji wanda ke jagorantan kungiyar masu kula da muhalli da ake kira 'Clean Senegal' sun fita zagaye da sakon 'a daina amfani da ledoji'.
Tunisian dancers perform during the 4th edition of the Carthage Choreographic Days in Tunis, Tunisia. The event runs from 11 to 18 June 2022.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Nan, masu rawa ne suka fita kan titi a Tunis a ranar Talata, inda suke rawa a matsayin ranakun koyar-da-rawa.
A nun walks out of Ouagadougou cathedral on June 12, 2022.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A nan kuma, an gudanar da taron addu'a a ranar Lahadi a wata majami'a da ke Ouagadoughou, babban birnin Burkina Faso.
Sheep are rescued after the overloaded ship Badr 1 sank in Sudan's Red Sea port of Suakin sank. It was crammed with thousands of animals, most of which drowned.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Duka dai a ranar, an ceci wadannan tumaki bayan da jirgin-ruwan da ya dauke su daga Sudan zuwa Saudiyya ya nutse, inda dubban dabbobi suka nutse.
Liberian Albinos attend an official program held to mark International Albino Awareness Day in Monrovia, Liberia, 13 June 2022. According to reports, the Liberia Albino Society petitioned members of the National Legislature to enact a law that would end discrimination and provide empowerment for its members. International Albinism Awareness Day is observed annually on 13 June to celebrate the human rights of persons with albinism, and to battle discrimination against those diagnosed with albinism worldwide. The United Nations" General Assembly adopted a resolution, establishing 13 June as International Albinism Awareness Day, which confirmed global focus on albinism advocacy, and encourages everyone to celebrate and promote albinism awareness globally. Albinism is a rare, non-contagious condition; both parents must carry the gene in order for it to be passed on, regardless if they themselves do not have albinism.

Asalin hoton, iStock

Bayanan hoto, A Monrovia, babban birnin Laberia, mutane ne ke maci domin bikin ranar zabiya ta duniya. A wannan hoton, yara ne masu lalurar zabiya ke zaune yayin macin na ranar Litinin
People play a football match organised by the Liberia Albino Society(LAS) on 11 June 2022 ahead of International Albinism Awareness Day on 13 June.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A nan a Liberia, Lokacin farin-ciki ne da kuma wayar-da-kai. Kungiyar masu lalurar zabiya a Liberia na kira ga gwamnati don kawo dokoki da zasu kawo karshen tsangwama da bayar da dama ga mutane da ke rayuwa da lalurar.
Mohammad Omar tends to tomatoes in a greenhouse farm on the outskirts of Mogadishu.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Lahadi, Dogayen ganyayyaki, kamar wannan, ana kara amfani da shi wajen noman tumaturi da borkono da sauran shuke-shuke kusa da Mogadishu, babban birnin Somalia.
Fish vendors stand by their stalls at the Gikomba fish market in Nairobi.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wannan hoton kasuwar sayar da kifi ce da ke Nairobi, babbar birnin Kenya aka dauka daga sama a ranar Talata.
Fishermen tend to their boats on the shores of the Paquitequete neighborhood in Pemba.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Nan, masu kamun kifi ne ke tattaunawa tsakaninsu a cikin jiragen-ruwa a garin Pemba, da ke arewacin Mozambique a ranar Alhamis.
Artworks of Kenyan artist Shabby Mwangi on display during the contemporary art exhibition "documenta fifteen" at the documenta hall in Kassel, Germany.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Alkaluma da mai zane-zane Shabby Mwangi dan kasar kenya na bayyana kan masu ziyara zuwa wannan wurin na nuna zane-zane da ke Kassel, a kasar Jamus, ranar Laraba.
A young Egyptian jumps into the water of the Nile river during hot weather in the Qanater neighbourhood on the outskirts of Cairo, Egypt.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A kasar Masar, Mutane ne ke tsalle cikin kogin Nilu yayin da yanayin zafi ya kai maki 43 na ma'aunin Celsius a ranar Asabar...
People swim in the Nile river during hot weather in the Qanater neighbourhood on the outskirts of Cairo, Egypt.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, An kuma ayyana dokar-ta-baci a wasu sassan kasar, wanda hakan ya sanya cibiyoyin lafiya ke cikin shirin ko-ta-kwana a dai-dai lokacin da yanayin zafi ke karuwa.
1px transparent line
Residents cycle along a road at dawn on the outskirts of Kigali, Rwanda.

Asalin hoton, Dukkan Hotuna suna da hakkin mallaka.

Bayanan hoto, Sannan a ranar Laraba, mahaya kekuna ne ke zagayawa a wajen birnin Kigali, babban birnin Rwanda da sanyin safiya.

Dukkan hotunan na da haƙƙin mallaka.