Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yanzu busasshen burodi ne gatan mazauna Afghanistan don kar yunwa ta illata su
- Marubuci, Daga Secunder Kermani
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Kabul
- An wallafa
A cikin wata kasuwa da ke kusa da wani shuɗin masallaci a birnin Kabul, wasu buhunhuna ne cike da ragowa kuma busassun burodi.
Akasari dabbobi ake ciyarwa da su, amma yanzu, a cewar masu sayar da su, mazauna Afghanistan ne da kansu ke saya suna ci.
Shafi Mohammed ya shafe shekara fiye da 30 yana sayar da busassen burodi a Kasuwar Pul-e-Kheshti da ke Kabul.
"Kafin yanzu, mutum biyar ne kan sayi wannan burodin a kowace rana, yanzu kuwa mutum sama da 20 [ne ke saya]," a cewarsa.
Kasuwar cike take da hada-hada - kuma duk mutane da muka yi magana da su na kokawa ne kan matsalolin tattalin arziki da suka mamaye ƙasar.
Yanayin samun kuɗi na 'yan ƙasar ya ragu da kusan ɗaya cikin uku tun bayan da Taliban ta hau mulki a watan Agustan 2021, yayin da farashin abinci ke ci gaba da tashi.
Da yake bincika buhuhuna, Shafi Mohammed ya nuna min irin burodin da kwastomomi ke zaɓa don su ci, ba busassu sosai ba ko kuma waɗanda suka daɗe.
"Rayuwar 'yan Afghanistan a yanzu kamar ta wani tsuntsu ne da aka kulle a keji ba tare da abinci ko ruwa ba," a cewarsa. "Ina addu'ar Allah ya raba mu da wannan ƙuncin da baƙin talauci."
An kai kayayyakin agaji Afghanistan saboda fargabar da ake da ita game da fari nan da lokacin hunturu, amma ana ci gaba da gargaɗin cewa ba su isa ba.
Ko ma dai yaya ne, an ɗauki matakin ne saboda shawarar da ƙasashen Yamma suka yanke ta janye dakarunsu daga ƙasar da kuma janye duk wani tallafi da suke ba ta wanda ta dogara a kai.
Kazalika, an hana gwamnatin ƙasar taɓa duk wasu ƙadarorinta tun bayan hawan Taliban mulki.
Akasarin matakan an ɗauke su ne saboda zargin take haƙƙin mata da Taliban ke yi da kuma sauran tsauraran dokoki da ta saka, musamman kan kayan da mata za su dinga sakawa.
Sai dai kuma iyalai marasa ƙarfi ne lamarin ya fi shafa, kamar na Hashmatullah.
Yana aiki ne a matsayin ɗan dako a kasuwar, amma tuni samunsa ya ragu zuwa kashi ɗaya cikin biyar a abin da yake samu a shekarar da ta gabata.
Da yake sayen ledar busasshen burodi, ya faɗa wa BBC cewa: "Tun safe nake aiki abin da zan iya saya kenan."
"Mutane na cikin yunwa," in ji shugaban dilolin. "Idan muka samu burodin mai ɗan tsafta mu ma ci muke," a cewar wani dilan.
A gidansa kuma da ke wata unguwar matalauta a Kabul, Hashmatullah ya dafa wa iyalansa abinci.
Yana yin bakin ƙoƙarinsa wajen ya ga 'ya'yansa uku ƙanana sun ci gaba da zuwa makaranta, ba kamar yadda wasu iyalan ke tura ire-irensu wajen aiki ba.
Sai dai hakan na nufin za su dinga cin busasshen burodi ne kawai, wanda aka yi banɗashonsa.
"Ina jin kunya idan na dawo gida saboda na kasa sama musu cikakken abinci," in ji shi.
"Babu abin da zan iya yi. Ko da na yi yunƙurin neman rancen kuɗi babu mai ba ni...'ya'yana duk sirance saboda ba sa cin abin da ya kamata."
A wajen wuraren sayar da burodi na Kabul, abu ne da ya zama ruwan-dare ganin yara ƙanana da mata na yin dogwayen layuka don karɓar sadakar sabon burodi, wanda ake bayarwa da yamma.
Wasu kan taho da kayan aikinsu na saƙa zuwa wurin saboda kada su rasa sadakar, inda suke shafe tsawon wuni a can.
Ko a lokacin da ake ba da tallafin biliyoyin daloli zuwa Afghanistan, cin hanci da kuma tasirin yaƙi ba sa bari a ji daɗin rayuwar.
Yanzu yaƙi ya ƙare, amma rayuwar na ci gaba da yi wa mutane tsauri ta wasu hanyoyi.