Yadda komawar magoya bayan al-Bashir kan mulki ta tayar da jijiyoyin wuya a Sudan

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Daga Mohanad Hashim
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- An wallafa
Shekaru uku bayan kifar da gwamnatin tsohon Shugaban Sudan Omar al-Bashir bayan zazzafara zanga-zanga, an gano cewa sojoji na bai wa tsoffin yan jam'iyyarsa ta National Congress Party (NCP) manyan mukamai, wanda hakan ya sa ake fargabar za su iya dawowa da karfinsu a fagen siyasa.
Gwamnatin hadaka da aka kafa ta zo karshe ne bara, bayan Janar Abdel-Fattah Burhan ya yi juyin mulki ga fararen hula, da suka taka muhimmiyar rawa wurin gagarumin boren da ya kawo karshen mulkin al-Bashir.
Sai dai a yanzu da dama na ganin cewa sojojin da ma sauran mambobin majalisar tsaro na goyon bayan tsoffin jami'an gwamnati, wadda ta gudanar da Shari'ar Musulunci mai tsauri a lokacin.
Hamza Balol, wanda jigo ne a kungiyar rajin demokradiyya ta FCC da aka kafa gwamnatin hadin gwiwa tare da sojoji, na ganin cewa sojojin sun yi wa tafiyar zamba cikin aminci.
A cewarsa wadanda suka yi juyin mulkin "na bai wa shugabannin tsohuwar gwamnati don su samu shiga a fagen siyasa."
"Dole ne kungiyoyin farar hula da su hada hannu su kawo karshen wannan juyin mulki," in ji Mr Balol.
Sama da mutum 100 ne aka kashe cikin watan Oktoban bara, a jerin boren da aka rika gudanarwa na bukatar a mayar da kasar mulkin farar hula.
Daya daga cikin umurnin da Janar Burhan ya bayar bawan juyin mulkin shine na dakatar da ayyukan kwamitin da aka kafa don lalubo hanyoyin ci gaba bayan kifar da gwamnati, sannan kuma ya soke duka matakan da kwamitin ya dauka.
Kwamitin a karkashin wani lauya Wajdi Saleh da aka tsare bayan sojoji sun kwace mulki, ya yi kokari wurin bankado cin hanci da rashawa da ya zama ruwan dare a zamanin al-Bashir.
Ya bankado sunayen jami'an gwamnati da yan kasuwa, tare da ƙwace kadarori da rufe asusun ajiyar mutane da dama.
Haka ma kwamitin na bincike kan huldodin da suka gudana a tsakanin shugabancin NCP da kuma manyan Janar- Janar bayan an yi juyin mulki.
Sai dai kwamitin ya fuskanci suka daga wasu, da ke ganin yana aiki ne ba bisa ka'ida ba, kazalika ya zama wani makami na muzguna wa wasu.

Asalin hoton, Getty Images
Bayan juyin mulkin, sojoji sun yi kokarin kulla huldar ƙud-da-ƙud da jam'iyyar NCP da yan korenta, don su samu damar dorewa kan mulki.
Daruruwan ma'aikata da aka kora a babban bankin kasar sun dawo aiki, hakama a ma'aikatar shari'a da kafafen yada labarai da sauran ma'aikatun gwamnati.
Daga cikinsu akwai Janar Ahmed Mufdal, tsohon gwamnan Kudancin Kordofan kuma tsohon Shugaban NCP.
A yanzu shi ne sabuwar hukumar samar da bayanan sirri da aka yi wa garambawul, wadda a lokacin mulkin al-Bashir ta zama tamkar wani dodo.
An kuma saki wasu daga cikin jiga-jigan jam'iyyar NCP da ake tsare da su, tare da bude musu asusan bankinsu.
Yanzu haka tsohon Shugaba al-Bashir na tsare hannun sojoji tun bayan kama shi da zargin cin hanci da rashawa a 2019.
Kuma tun a watan Yulin 2020 ake masa sharia kan juyin mulkin da ya yi, da ya kawo shi kan madafun iko a shekarar 1989.
Dama abin da masu rajin kare dimokradiyya ke fatan gani, kuma an fara shari'ar ne tun kafin Janar Burhan ya ƙwace mulki.
A yanzu sojojin sun ki mika Bashir hannun Kotun Hukunta Manyan laifuka ta Duniya don fuskantar tuhumar kan rikicin Dafur, zargin da ya musanta.
Wasu masu sharhi sun yi amannar cewa a karshe sojojin za su saki tsohon Shugaban. kamar yadda aka saki Shugaba Hosni Mubarak a Egypt bayan sojoji sun kwace mulki a 2013.

Asalin hoton, Getty Images
Ali Karti wanda shine Shugaban riko na kungiyar Sudan Islamic Movement, wata hadakar kungiyoyin musulunci. Kuma shine ake ganin kashin bayan dawowar jam'iyyar NCP.
Yanzu haka yana zaune ne a Turkiyya, kuma ya yi hira ta kafar talabijin a karon farko cikin sama da shekaru uku. A hirar ya kare NCP, ya kuma ce jam;iyyun Musulunci na bukatar kwaskwarima don shiga zabe mai zuwa.
Mr Karti wanda tsohon ministan harkokin waje ne na daga jerin mutanen da kwamitin da ke aikin bankado badakalar da aka yi a gwamnatin Bashir ke nema.
An ƙwace daruruwan filayensa da ke Arewacin Khartoum, kuma ya musanta aikata ba daidai ba.
Ana kuma zarginsa da hannu a muzgunawa masu neman yancin kafa kasar Sudan ta Kudu, a karkashin rundunar soji ta Popular Defence Forces da aka kafa a shekarun 1990.

Asalin hoton, Getty Images
Shi ma tsohon ministan yada labarai Amin Hassan Umar wanda aka yi hira da shi a baya bayannan ya jaddada cewa akwai rundunar musulunci mai mayaka 500,000 da ke shirye su kare Sudan daga barazana.
Duk da ba za a iya tantance gaskiyar ikirarin nasa ba, idan har gaskiya ne akwai adadin wadannan mayaka 500,000, to kuma sun fi karfin rundunar Rapid Support Forces (RSF), wadda ta kunshi mayakan Janjaweed da ake zargi da aikata miyagun laifuka a yakin Dafur.
An kiyasta cewa RSF na da mayaka daga 50,000 zuwa 150,000.
Wasu masu sharhi sun yi amanna cewa manyan sojoji da suka hada da Janar Burhan na amfani da kungiyoyin Islamaa don rage karfin fada aji da kwamnadan RSF Janar Muhammad Hamdan Dagalo ke dashi.
Yanzu haka Mr Dagalo ne mataimakin Shugaban sojojin da suka yi juyin mulki.











