'Shin armashin Ranar Dimokraɗiyya na raguwa ne a Najeriya?'

An wallafa

A Najeriya a duk ranar 12 ga watan Yunin kowacce shekara ake bikin zagayowar Ranar Dimukuradiyya a kasar, bayan da Shugaba Buhari ya sauya daga 29 ga watan Mayu.

A shekarar 2022, ranar ta zo dai-dai lokacin da jam'iyyun siyasar kasar suka kammala zabukan fitar da gwani na wadanda za su tsaya musu takara a zaben 2023.

Farfesa Abubakar Mu'azu malami, a sashen koyar da aikin jarida a jami'ar Maiduguri da ke Najeriya, ya shaida wa BBC cewa, ita wannan rana ana gudanar da ita ne domin tunatar da jama'a irin gwagwarmayar da aka yi da sojoji har aka samu suka yarda suka bayar da mulki ga fararen hula.

Ya ce, gudanar da bikin ranar na da muhimmancin saboda mutane su sani cewa akwai wadanda suka yi gwagwarmaya suka tsaya tsayin-daka wajen komawa tafarkin dimukuradiyya, inda har wasunsu sai da aka kai su gidan yari.

Farfesan ya ce, wasu kuma har guduwa suka yi suka bar kasar saboda gwagwarmayar.

Malamin jami'ar ya ce, "Duk da ana gudanar da bikin ranar, to a gaskiya armashinsa na raguwa, saboda yawancin mutane suna tsammanin idan an koma mulkin farar hula za a samu abubuwa na walwala da tsaro da cigaba, to amma abubuwan ba sa samuwa yadda ake so."

Farfesa Abubakar Mu'azu, ya ce a yanzu yadda tabarbarewar tsaro ta addabi jama'a, ya sa mutanen Najeriyar ma ba sa ganin ayyukan da ake yi, inda har wasu ma na cewa menene ma amfanin dimukuradiyyar ma tun da ba za a samu zaman lafiya ba.

Karin bayani

Wannan rana da galibin al'ummar Najeriyar suka fi sani da June 12, rana ce da tarihin kasar ba zai manta da ita ba saboda a ranar ne aka gudanar da zaben Najeriya na 1993, kodayake har kawo yanzu hukumar zaben Najeriyar ba ta sanar da wanda ya yi nasara ba.

To sai dai kuma alamu sun nuna cewa dan takarar jam'iyyar SDP, wato Moshood Kashimawo Olawale Abiola, ne ya kama hanyar cin zaben inda ya kayar da abokin takararsa na jam'iyyar NRC Bashir Othman Tofa.

An dai ki sanar da sakamakon zaben ne saboda soke zaben da gwamnatin mulkin soja a karkashin Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta yi.

Soke zaben dai ya janyo gagarumar tirjiya daga 'yan jam'iyyar SDP da kuma 'yan gwagwarmaya da ke rajin kafa gwamnatin farar hula a wancan lokaci abin da ya kai ga tsare wasunsu da dama ciki har da Abiola.

Wannan rana ta 12 ga watan Yuni, ta kara karfi ne bayan da gwamnatin mulkin dimukuradiyya ta tsaya da kafarta a 1999.

An rinka gudanar da bikin wannan rana ne tun daga shekarar 2002, haka kuma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kara wa wannan rana karfi a shekarar 2018 bayan da ya sauya Ranar Dimukuradiyya daga ranar 29 ga watan Mayu zuwa ranar 12 ga watan Yuni.

Sauya Ranar Dimukuradiyya daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni bai yi wa wasu 'yan Najeriyar dadi ba inda har wasu na ganin cewa siyace kawai.

A kowacce rana irin wannan gwamnatin Najeriyar kan bayar da hutu ga 'yan kasa, sannan ta shirya biki a matakin tarayya, haka suma jihohin kasar musamman na shiyyar kudu maso yammaci wato na Yarabawa kan shirya irin wannan biki da nufin tunawa da ranar da aka yi zaben 12 ga watan Yuni.