Waiwaye: ISWAP ce ta kashe mutum 41 a cocin Ondo, maniyyatan Najeriya sun fara isa Saudiyya

An wallafa

Kamar kowane mako, mun duba muhimman abubuwan da suka faru a makon da ya gabata.

Maniyyatan Najeriya sun fara sauka a Saudiyya

Jirgin farko na maniyyata daga Najeriya ya tashi daga birnin Maiduguri na Jihar Borno ranar Alhamis don gudanar da ibadar Hajji ta shekarar 2022 - 1443 bayan Hijira.

Zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, maniyyatan Najeriya 1,354 ne suka sauka a Saudiyya.

Jirgin farkon ya tashi ne zuwa Saudiyya da maniyyata 500 da tsakar rana.

Shugaban Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya Zikrullah Kunle Hassan da Gwamnan Borno Babagana Umara Zulum na cikin waɗanda suka halarci bikin tashin jirgin.

Zikrullah ya buƙaci maniyyatan su yi wa Najeriya addu'a bayan sun yi wa kansu, "don miƙa wa sabuwar gwamnati mulki cikin kwanciyar hankali" yayin da ake tunkarar zaɓen 2023.

Jumullar maniyyata 43,000 ne aka sa ran za su je aikin daga Najeriya a bana.

ISWAP ce ta kai kashe mutum 41 a cocin Jihar Ondo, in ji gwamnatin Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta yi zargin cewa kungiyar ISWAP mai tsattsauran kishin Musuluncin ce ta kai hari a wani coci da ke garin Owo na Jihar Ondo a Kudu maso yammacin kasar.

Harin ya yi sanadin mutuwar akalla mutum arba'in tare da jikkatar mutane da dama.

Ministan harkokin cikin gida na kasar, Rauf Aregbesola, ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Alhamis bayan kammala taron majalisar tsaron kasar wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Wannan ne karon farko da majalisar tsaron kasar ta dora alhakin harin kan kungiyar ta ISWAP.

Idan hakan ya tabbata, zai kasance karon farko da kungiyar ta kai hari a kudancin kasar. ISWAP ta dade tana kai hare-hare a arewacin Najeriya musamman a arewa maso gabas.

Aregbesola ya ce majalisar tsaron kasar ta damu matuka bisa kashe-kashen da ake yi da sunan batanci ga addini kuma ta umarni jami'an tsaro su cafke mutanen da ke da hannu a abubuwan da suka faru a Sokoto da Abuja kwanakin baya.

An saka dokar hana fita a kananan hukumomi biyu na Adamawa kan rikicin ƙabilanci

Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya sanya dokar hana fita a wasu kananan hukumomi biyu da suka hada da Lamurde da Guyuk biyo bayan rikicin kabilanci.

A wata sanarwar da ya fitar, gwamna Fintiri ya ce dokar hana fitar za ta soma aiki daga karfe 5 na yamma zuwa 6 na safe.

Rahotanni na cewa rikicin ya faru ne da safiyar ranar Litinin, sai dai hankula sun kwanta bayan tura jami'an tsaro domin dawo da doka da oda.

Gwamnan ya ce ba za su lamunci ɓata-gari su tarwatsa kasar ko tarwatsa zaman lafiyar al'umma ba.

Fintiri ya kuma aike da sakon ta'azziya da jaje ga wadanda lamarin ya shafa.

Bola Tinubu ya lashe zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa na APC

Tsohon gwamnan jihar Legas Bola Ahmad Tinubu ya lashe zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa na jam'iyyar APC.

Ya lashe zaɓen ne da ƙuri'a 1,271, kuma dama tun da fari shi ne ƴar manuniya ta nuna ya fi yawan ƙuri'u.

Bisa alƙaluma da aka sanar a bainar jama'a, ministan sufuri Rotimi Amaechi ya samu ƙuri'a 316, yayin da Yemi Osinbajo ya samu ƙuri'a 235.

Shugaban majalisar dattijan ƙasar Sanata Ahmad Lawan ya samu ƙuri'a 152.

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya samu ƙuri'a 47, shi kuwa tsohon gwamnan jihar Imo Sanata Rochas Okorocha bai samu ƙuri'a ko ɗaya ba.

Gwamna Tambuwal ya koma yin takarar sanata a Sokoto

Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya zama ɗan takarar sanata mai wakiltar Sokoto ta Kudu ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP.

Gwamnan ya koma takarar ɗan majalisar dattawa ne bayan zaɓen fitar da gwani na ɗan takarar shugaban ƙasa inda ya janye wa Atiku Abubakar.

Gwamnan ya yi nasara ne ba wata hamayya, kuma zai fafata ne da Sanata Abdullahi Danbaba Dambuwa na jam'iyyar APC.

'Lalacewar tashoshin samar da wutar lantarki 20 ne ya janyo rashin wuta a Najeriya'

Najeriya dai na da tashoshin samar da hasken lantarki 23, wanda suke samar da mega watt dubu 11,165.

Kamfanonin da ke samar da wutar lantarki a kasar ne ke kula da tashoshin.

Ana dai yawan smaun daukewar wutar lantarki a kai a kai a Najeriya, abin da ke janyo dakushewar harkokin kasuwanci musamman masana'antu da sauransu.Bayanai sun nuna cewa sakamakon matsalar rashin wutar da ake fama da ita a Najeriya, an gano cewa tashar samar da hasken lantarki 20 ne a kasar suka lalace, abin da ya janyo ake rasa mega wat 2000.

Daliban Kaduna 701 ba za su rubuta jarrabawar WAEC ba

Dalibai 701 daga jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya ba za su zana jarrabawar kammala sakandire ta WAEC ba saboda rashin ba su damar biyan kudaden da ya kamata su biya.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa daliban, wadanda suka fito daga makarantun sakandire daban-daban a jihar an i ba su damar sanya makinsu na makaranta a shafin hukumar da ake shirya jarrabawar kammala karatun sakandiren.

Ko da yake, hukumar daga bisani ta yi kira ga makarantun da abin ya shafa a kan cewa za a ƙara buɗe shafin domin su sanya makin nasu.

Makarantun da abin ya shafi ɗalibansu sun haɗa da Government Secondary School Kuse, wadda ɗalibanta da ke ajin karshe 290 abin ya shafa.

Sai Government Secondary School Independence Way Kaduna, mai ɗalibai 150 da Government Secondary School Kagarko mai dalibai 110 da kuma Government Senior Secondary School Iddah mai dalibai 100.

Sauran sun hadar da Al-Bahmeen Academy, Kaduna mai dalibai takwas da Kalhyatu AbdulRahman Bin Auf Academy, Jere mai dalibai 15 da Great Panaf Schools Kaduna mai dalibai 13 da ECWA Secondary School, Kubacha mai dalibai 10 sai kuma Government Secondary School Mato mai dalibai biyar.

An rage wa ɗan sandan Najeriya muƙami bayan bidiyonsa da aka gani yana rawa a Tiktok

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta rage wa wani jami'inta muƙami wanda ta kama yana rawa kuma yana rera wata waka da aka bayyana ta ƴan ƙungiyar asiri a wani bidiyo a kafar Tiktok,

Ɗan sandan da aka bayyana sunansa a matsayin Isaac Mathew, an rage masa mukami daga kofur zuwa kurtun ɗan sanda.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar ƴan sanda, Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Ya ce rage wa jami'in girman muƙamin da aka yi, ya biyo bayan shari'ar da aka gudanar akansa da kuma bin tsarin doka kafin yanke masa hukuncin laifin da ya aikata.

Ya ce jami'in ya aikata laifin yaɗa ayyukan ƙungiyar asiri da kuma saɓa dokar ƴan sanda ta amfani da kafafen sada zumunta na intanet.

Kotu a Legas ta yanke wa ɗan shekara 73 hukuncin zaman gidan yari na shekara 24

Wata kotu a Jihar Legas ta yanke wa wani ɗan shekara 73 hukuncin zaman gidan yari na shekara 24 kan laifin almundahana.

Tun da farko hukumar EFCC da ke yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ce ta gurfanar da shi a kotu kan zarge-zarge tara ciki har da batun bayar da cakin banki na bogi da satar miliyan 71.

Ana zarginsa ne da damfarar wani kamfani mai suna Nepal Oil and Gas Services Limited a wani ciniki da ya shafi sayar da wani fili a Onitsha da ke Jihar Anambra.