Zaɓen fitar da gwani na APC: 'Yan takara bakwai sun janye wa Tinubu, ɗaya ya janye wa Osinbajo

    • Marubuci, Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Abuja Bureau
  • An wallafa

Masu neman jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta tsayar da su takarar shugaban ƙasa bakwai sun janye tare da mara wa Bola Ahmed Tinubu baya.

Kazalika, ɗan takara Mista Nicholas Felix ya janye don mara wa Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo baya.

Dukkan 'yan takarar sun janye ne jim kaɗan kafin fara jefa ƙuri'a a dandalin Eagle Square da ke Abuja, babban birnin ƙasar.

'Yan takara 14 ne suka rage a takarar daga cikin 23 da jam'iyyar ta tantance tun farko.

'Yan takarar da suka janye wa Tinubu

Masu neman takarar da suka janye wa jagoran APC kuma tsohon Gwamnan Jihar Legas Bola Ahmed Tinubu sun ƙunshi waɗanda suka fito daga yankinsa na kudu maso yamma da sauran yankuna.

Su ne:

  • Gwamnan Ekiti Kayode Fayemi
  • Tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom Godswill Akpabio
  • Tsohon Gwamnan Jihar Ogun Ibikunle Amosun
  • Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Dimeji Bankole
  • Gwamnan Jigawa Badaru Abubakar
  • Uju Ohanenye - mace tilo
  • Sanata Ajayi Boroffice

Waɗanda suka rage a takarar

'Yan takarar da za a jefa wa ƙuri'su ne:

  • Yemi Osinbajo (Jihar Ogun)
  • Ahmad Lawan (Jihar Yobe)
  • Bola Tinubu (Jihar Lagos)
  • Tein Jack-Rich (Jihar Rivers)
  • Rochas Okorocha (Jihar Imo)
  • Tunde Bakare (Jihar Ogun)
  • Rotimi Amaechi (Jihar Rivers)
  • Emeka Nwajiuba (Jihar Imo)
  • David Umahi (Jihar Ebonyi)
  • Ogbonnaya Onu (Jihar Ebonyi)
  • Ben Ayade (Jihar Cross River)
  • Yahaya Bello (Jihar Kogi)
  • Ikeobasi Mokelu (Jihar Anambra)
  • Ahmed Rufai Sani

Ku zaɓe ni don na samar da ayyukan yi - Osinbajo

Ɗan takara Mista Nicholas Felix, shi ne kaɗai ya janye kuma yake mara wa Mataimakin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo baya.

Farfesa Osinbajo ya nemi wakilai wato deliget su zaɓe shi don ya samar wa 'yan Najeriya ayyukan yi idan ya zama shugaban ƙasa a babban zaɓen 2023.

Kafin jawabin nasa, hayaniyar da wasu magoya baya suka dinga yi ta kawo masa tsaiko, inda suka hana shi gudanar da jawabi a wajen taron na APC.

"Na gode, na gode sosai," abin da Osinbajo ya dinga faɗa musu ke nan kafin su bar shi ya yi jawabin da kyar.

Ba zan janye wa kowa ba - Tunde Bakare

Fasto Tunde Bakare ya ce bai shiga neman takarar shugaban ƙasa a APC ba don ya janye wa wani.

"Da yawa daga cikin waɗannan 'yan takarar suna da matsala da hukumar EFCC," in ji shi yayin da yake magana kan ƙwarewarsa a harkokin mulki.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake tabbatar da cewa bai taɓa riƙe wani muƙamin siyasa ba, amma ya ce "da yawa daga cikin waɗanda suke da ƙwarewar su suka lalata ƙasa [Najeriya]".

Kada ku ƙyale PDP ta mayar da Najeriya baya - Buhari ya roƙi 'yan Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga 'yan Najeriya su tabbata ba su bar jam'iyyar adawa ta PDP "ta mayar da ƙasa baya ba".

Da yake jawabi a wurin zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyarsu ta APC, Buhari ya ce APC ta sauya Najeriya ta hanyar gudanar da ayyukan raya ƙasa.

"Wajibi ne mu zaɓi masu adalci 'yan kishin ƙasa da ke da aƙidar haɗa kan ƙasarmu...don ciyar da ita gaba.

"Bai kamata mu ƙyale PDP ta mayar da Najeriya baya ba."

Zuwa lokacin haɗa wannan rahoton PDP ba ta mayar da martani ba, wadda tuni ta zaɓi Atiku Abubakar a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a babban zaɓe na 2023.

Yawan daliget ɗin da ke kaɗa ƙuri'a

Ga jerin wakilai ko kuma daliget ɗin da aka tantance don zaɓar ɗaya daga cikin masu neman takarar shugaban ƙasa guda 14 a jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya:

  • Abiya 50
  • Adamawa 50
  • Anambra 63
  • Bayelsa 24
  • Bauchi 55
  • Benue 64
  • Borno 81
  • Cross River 54
  • Delta 73
  • Enugu 51
  • Ekiti 48
  • Edo 52
  • Ebonyi 38
  • FCT (Abuja) 18
  • Gombe 33
  • Imo 81
  • Jigawa 81
  • Legas 60
  • Filato 81
  • Katsina 102
  • Kebbi 63
  • Kwara 48
  • Kogi 63
  • Kaduna 61
  • Kano 126
  • Nasarawa 39
  • Neja 75
  • Ondo 54
  • Ogun 60
  • Oyo 99
  • Osun 90
  • Rivers 69
  • Sokoto 69
  • Taraba 48
  • Yobe 51
  • Zamfara 42