Mutanen Habasha da ke sauya sunansu saboda alfahari

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Daga Berhanu Gemechu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Afaan Oromoo
- An wallafa
Ana samun karuwar alfahari a tsakanin al'ummar Oromo, wato kabila mafi girma da ta samar da mutane kamar Moti Begi wadanda ke sauya sunayensu.
Mutumin, mai kimanin shekara 40 da aka fi sani da Dereji Begi, ya sauya sunansa saboda alfahari ya koma Moti Begi, ma'anar Moti dai a harshensu ita ce sarki.
A Habasha, duk sunan farko na da matukar muhimmanci, yawancin bangare na biyu a sunan ba sunan wani ba ne da mutum ya gada, yawanci sunan mahaifin mutum ne na farko.
Mr Moti, wanda injiniya ne, ba shi ne kadai mutumin da ya sauya suna ba, akwai abokansa bakwai da suka sauya nasu sunayen.
Daruruwan shekaru, al'ummar Oromo na jin kunyar yarensu na Afaan Ormoro wanda suka gada tun kaka da kakanni.


A kokarinsu na hade kan masarautar ta zama dunkulalliya, sarakunan gargajiyar yankin sun mayar da yaren Amharic a matsayin wanda za a rinka yi a gaba dayan yankin.
Yawancin mutanen yankin sun zabi sunayen Amharic don amfani da su, to amma saboda sauyawar zamani da kuma siyasa tun daga 1991, halayyar mutane ta sauya musamman daga bangaren matasa wadanda suka taimakawa Abiy Ahmed zama firaminista.
Ya dare karagar mulki a 2018, kuma shi ne firaminista na farko daga kabilar Oromo.
Mr Moti ya shaida wa BBC cewa, hanyar da zan bi don na kara tabbatar daga kabilar dana fito ita ce ta sauya sunana, inda na koma Mr Moti a yanzu.
Abin da ya ja hankalinsa shi ne yadda wani talla da aka yi a yankin Oromia, inda yawancin 'yan Oromo ke rayuwa a kasar da ke rarrubuwar kawuna saboda kabilanci.

Asalin hoton, Getty Images
Jami'an lafiya a yankin sun kaddamar da gangamin daukar likitoci dubu biyu aiki da kuma sauran ma'aikatan lafiya, sannan dole su zamo suna iya magana da harshen Oromoo.
To amma wadanda ba sa magana da harshen Oromoon sun yi watsi da daukar nasu aiki.
Ga Mr Moti, wannan sai ya zame masa darasi, saboda yawancin wadanda aka ki dauka aikin duk sun girma ne a Oromia kuma ba su yi kokari sun koyi yaren da yawancin wadanda ke zaune a yankin ke amfani da shi ba.
Sai ya yi amfani da wannan damar.
Ya ce," Wannan ne ya sanya na sauya sunana".
Yawancin yaran da suka girma a Oromo fiye da shekara 30, bayan rushewar mulkin markisanci suna da wani ririn suna.
Masu bincike sun sanya aka fito da wani sabon tsrai a gwamnati kan yadda za a rinka koyawa yara amfani da harshen uwa a makaranta, sannan kuma yaren Amharic ya zamo wanda za arinka amfani da shi a wajen aiki.

Asalin hoton, Getty Images
Yaran Oromoo sun fara samun sunayen Afaan Oromoo da kuma na Amharic a mastayin suna guda.
Wani mutum dna shekara 32, Abdi Gamachu, na da sunan Amharic wato Girma, wato mai daukaka, wanda yake kuma amfani da shi har ya sauya suna.
Mahifiyarsa ce ta zabar masa sunan bayan da wata ma'aikaciyar jinya a asibitin da ta haihu ta canja mata wajen rubutu ta sanya masa Abdi ma'anar sunan mai fata.
A gida da wajen abokansa an sanshi da Abdi.
Ya ce a yanzu yana matukar farin ciki ya samu sunan da ya ke so, sanann yana so ya canja dukkan takardunsa da sunan.
Ga Mr Moti, ya ce hanyar da zaka yi amfani da ita mafi sauki wajen bata ainihin tushenka ita ce ka daina amfani da harshen.
Yana jin cire sunansa na Amharic, shi da sauran mutane kamar sun koma kan al'adarsu ne.










