Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Birtaniya za ta bai wa Ukraine manyan makaman zamani don yakar Rasha
Sakataren ma'aikatar tsaron Birtaniya, Ben Wallace, ya sanar da cewa kasarsa za ta aika wa Ukraine taimakon manyan bundugogi masu ruwan makaman roka, a lokaci guda, da ke cin dogon zango, tare da harsasansu.
Mista Wallace wanda ya ce, makanan za su taimaka wa Ukraine kare kanta daga mamayen Rasha, ya yi wanan sanarwar ne bayan da Amurka ma ta yi irin alkawarin.
To amma Shugaba Putin na Rasha ya ce zai mayar da martani na daban, kan wannan tallafi na makamai da kasashen yamma suke bai wa Ukraine, inda ya ce zai kai hari inda a da bai kai ba.
A makon da ya gabata ne gwamnatin Amurka ta ce za ta aika wa Ukraine manyan bundugogin harba tarin makaman rokar na lokaci daya, bayan da Washington din ta samu tabbacin cewa Ukraine za ta yi amfani da su ne domin kare kai amma ba kai hari cikin Rasha ba.
Manyan bindigogin harba makaman rokar da Birtaniya za ta tallafa wa Ukraine da su, iri daya ne da na Amurkar.
Za a iya harba makaman roka 12 cikin minti daya kacal, kuma makamin zai iya cin zangon mil 50.
Ma'aikatar tsaron ta Birtaniya ba ta bayyana yawan wadannan makamai da za ta ba wa Ukraine ba, amma BBC ta fahimci cewa, guda uku za a fara ba ta, hade da tarin harsasansu.
A cikin makonnin da ke tafe ne za a koyar da sojojin Ukraine yadda ake amfani da makaman, a Birtaniya.
Birtaniya da Amurka sun kasance kan gaba wajen bai wa Ukraine taimakon makamai, to amma ba ta wannan samfurin makamin na zamani mai harba makaman roka da ke cin dogon zango, ya zama wani abu na daban, domin abu ne da tuni ya harzuka Rasha.
Haka kuma wannan ya nuna cewa Ukraine na kokarin gogayya da Rasha kan dimbin makaman da take da su.
Domin Shugaba Putin ya yi barazanar kai sabbin hare-hare kan wuraren da a da bai taba ba, muddin kasashen yamma suka sake suka bai wa Ukraine wadannan makamai masu linzami da ke cin dogon zango.
A wata hirar talabijin da aka yi da shi shugaban na Rasha ya ce manufar bai wa Ukraine wadannan makamai ita ce neman tsawaita rikicin.
Ya ce, ''Muddin aka ba su wadannan makamai, za su yi abin da ya dace, mu yi amfani da makamanmu, wadanda muke da isassun da a mu kai hari inda ba mu kai hari ba yanzu.''
Ya kara da cewa, ''Duk wannan baragada da ake yi ta aika karin makamai, domin manufa daya ce kawai, kawai domin a tsawaita rikicin ne kawai." in ji shi.
Shugaban na Rasha ya yi wannan gargadi ne, yayin da fashe-fashen makamai suka girgiza sassan babban birnin Ukraine din Kyiv, Lahadin nan, a hare-hare na farko ta sama a birnin bayan makonni.
Rashar ta ce ta kai harin ne kan motocin yaki na igwa wadanda kasashen Turai suka bai wa Ukraine, yayin da ita kuwa Ukraine din ta ce waje ne na gyaran jiragen kasa.
A halin da ake ciki rahotanni sun ce an kashe wani janar na sojin Rasha a fadan da ake tafkawa a yankin Donbas.
Rasha ta mayar da hankalinta kan yankin na Donbas ne a karshen watan Maris bayan da da ta janye daga yankin babban birnin makwabciyar tata da ta mamaya, Kyiv.
Ganin yadda Rashar sannu a hankali take kara dannawa ta kasa, daruruwan kilomita zuwa gabashin Ukraine din, kasashe da dama sun yi alkawarin aika wa Ukraine makamai na zamani.