Abubuwan da kuke bukatar sani game da bambancin lokacin motsa jiki tsakanin namiji da mace

.

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Daga Philippa Roxby
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Health reporter
  • An wallafa

Motsa jiki yana da kyau matuƙa a lokacin da ake yinsa, sai dai lokacin da ya kamata a samu abin da ake so wurin motsa jiki ya bambanta tsakanin mace da namiji, kamar yadda wani binciken Amurka ya bayyana.

Bincken ya gano cewa mata sun fi ƙona kitse a lokacin motsa jiki da safe fiye da maza, inda kuma da yamma maza sun fi ƙona kitsen.

Akasarin abin da aka sani kan wannan lamari an same shi ne daga irin binciken da ake yi a kan maza.

Bambancin sinadaren jiki, da kuma bambancin bacci tsakanin mace da namiji duk za su iya taka muhimmiyar rawa.

Wani bincike da aka yi kan maza 30 da mata 26 waɗanda duka suna da cikakkiyar lafiya kuma suna tsakanin shekara 25 zuwa 55 an shafe makonni 12 ana binciken inda aka sa ido kan irin motsa jiki daban-daban da ake yi wanda suka haɗa da guje-guje.

Wani rukuni na mutanen ya yi atisaye na sa'a ɗaya tun kafin 8:30 na safe inda ɗayan rukunin kuma suka soma yi da dare tsakanin 18:00 zuwa 20:00. Duka waɗanda aka yi gwajin da su akwai iri abincin da aka amince su ci.

Masu binciken sun yi gwajin jini da kitsen kowa da ƙarfin mutum da yadda mutum zai iya sarrafa jikinsa.

Duka waɗanda aka yi gwajin da su sun samu ci gaba a kiwon lafiyarsu a tsawon makonni 12.

"Lokacin da ya fi kyau wurin motsa jiki shi ne lokacin da mutum zai iya yi a lokacinsa," in ji Dakta Paul Arcerio, wanda jagora ne a bincike, marubuci kuma farfesan kiwon lafiya da halayyar ɗan adam a kwalejin Skidmore da ke New York.

Sai dai ya bayyana cewa akwai wani abu da ke faruwa wanda ke nuna cewa akwai lokacin da ya kamata namiji ko mace duka kowa ya motsa jiki.

Wannan layi ne

Da wuri ko kuma latti?

Bisa irin sakamakon da aka samu, matan da suke so su rage kitsen jikinsu da kuma rage hawan jini ya kamata su rinƙa motsa jiki da safe, in ji Dakta Arcerio,

Wannan na da muhimmanci sakamakon ciki ya nannaɗe sassan jikin mutum da ke can ciki, da suka haɗa da hanta, kuma hakan na da hatsari.

Mazan da ke cikin binciken ba su cika damuwa ba da lokacin motsa jiki da rana ba, inda suke samun ci gaba a lafiyarsu da safe da dare.

Sai dai an gano cewa motsa jiki da dare ya fi ga maza inda yake ƙara kyautata zuciyarsu da kuma yadda ɗan adam ke firar da bayan gida da kuma fitsari," in ji Dakta Arcerio.

Hakan na nufin wannan zai rage barazanar yin ƙiba fiye da kima da ciwon suga da ciwon zuciya da shanyewar rabin jiki.

Babu tabbaci kan takamaiman dalilin da ya sa lokutan motsa jiki tsakanin maza da mata suka bambanta, inda masu bincike suka ce ana buƙatar a ƙara zurfafa bincike domin gano dalilin hakan.

Sun bayyana cewa akwai yiwuwar mata na ƙona kitse fiye da maza da safe sakamakon akwai yiwuwar su fi samun kitse a ciki.

Wannan layi ne