Kantin abincin da ya hana masu hijabi da jallabiyya shiga cikinsa a Saudi Arabia

Asalin hoton, Getty Images
Wani babban kanti ko gidan sayar da abinci da kayan kwalan da makulashe na kasar Faransa, ya hana mata masu hijabi da abaya da maza masu jallabiyya a birnin Jeddah na Saudi Arabia, shiga cikinsa.
sai dai kuma masu wurin sun musanta hakan, bayan da ake ta suka da caccakarsu a shafukan intanet, da hana mata da ke sanye da hijabi ko abaya shiga.
Wannan gidan abinci na duniya na kasar Faransa, Bagatelle, ya gamu da suka da caccaka a shafukan intanet, bayan da labarin zargin cewa reshen nasa na birnin Jeddah a Saudi Arabiyar ya hana mata da ke sanye da hijabi ko abaya, da kuma maza da suma suka sanya tufafin da galibi aka san 'yan Saudiyya da sanya wa kamar jallabiyya ko alkyabba, shiga cikinsa.
Jama'a da dama a Saudiyyar sun fusata inda suka rika nuna bacin ransu a shafukan intanet kan yadda suke cewa, wani kamfani na waje na neman tilasta wa 'yan Saudiyya wata al'ada da ba tasu ba, abin da ya kai har wasu ma na kira da a rufe gidan.
Hukumar gidan abincin na Bagatelle, ta aika wa da BBC wata sanarwa, wadda a cikinta take cewa, reshen nasa na Jeddah, wanda wani kamfani na Saudiyya ke tafiyarwa, bi aikata wni abu irin wannn da ake zarginsa da yi ba, na hana mata da ke sanye da hijabi ko abaya, ko kuma maza masu jallabiyya ko alkyabba shiga, ta ce abin da ta yi kawai ta bi ka'idoji da tsarin wurin shakatawa na bakin teku ne kawai, wanda wuri ne na 'yan kasuwa, inda a nan reshen nasu yake.
Kuma tsarin da ainahin masu wannan wuri suka yi shi ne, wanda gaba dayn wurin shakatawar shi ma na Saudiyya ne, tsarin shi ne duk wanda ke da wuri a wajen ya bi dokar amfani da tsarin tufafin Turawa.
Kantin abincin na Bagatelle ya jaddada cewa shi yana bi da mutunta dokoki da al'adun mutanen dukkanin wurin da yake da wani reshe, wanda ya hada da rassansa da dama da suke Saudi Arabiya.
Masu kantin suka ce sun ma rufe reshen nasu da ke Jeddah kusan tsawon wata biyu baya.
Wannan hayaniya da ta taso dai wata alama ce ta irin sabanin al'ada da ake cin karo da shi, a yayin da kasar ke rungumar sauye-sauye na zamani, musamman kokarin bunkasa harkar yawon bude idanu domin samun masu ziyara daga musman kasashen Yamma, na Turawa.
Kuma daya daga cikin wuraren da hukumomin Saudiyyar ke son janyo hankalin 'yan yawon bude-idanun shi ne bakin tekunta na Maliya, inda wannan gidan abinci yake a bakin ruwan.











