Hotunan Afirka na mako: Daga ranar 20 zuwa 26 ga watan Mayun 2022

An wallafa

Zababbun hotunan wasu kasashen Afirka da 'yan nahiyar a wasu sassan duniya na wannan makon:

Short presentational grey line
Mai kula da kudan zuma a Kenyan, rike da na'urar gane ingantacciyar zuma. An yi mata kitso, kuma sanye da tufafin gargajiya na 'yan Kenya, ta na leka na'urar da ido daya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Juma'a a Kenya, mai kula da kudan Zuma, na nuna yadda ake gane ingantacciyar zuma ta amfani da na'ura a lambun Nakuru Nyayo da ke birnin Nakuru.
Wani na duba lafiyar kunkuru. Kunkurun na kwance kan teburi. Mata na tsaye a bayansa su na kallo.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A kasar Tunusia ranar Lahadi, wani masanin kimiyya ne yake duba lafiyar wani kunkuru a birnin Sfax.
Ana iya ganin yara uku na wasan zamiya daga kan dalar gishiri. Gishirin fara sol, ga kuma sararin samaniya ta yi launin bula mai ban sha'awa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A dai ranar Juma'ar a kasa guda, wani yaro yana na wasa a dalar gishiri da ke Port Fuad.
Rakumi durkushe kan kafafun sa, kan rairayin sahara a kusa da dalar pyramids a kasar Masar. Sararin samaniya ya gauraya da launin fari da bula mai daukar hankali.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Can a yankin Giza, na kasar Masar, rakumi ke durkushe kan kafafunsa domin hutawa a kusa da dala a ranar Lahadi...
Hoton kyakkyawan zane mai motsi.

Asalin hoton, Annika Hammerschlag

Bayanan hoto, A ranar Lahadi a kasar Senegal kuwa, an baje-kolin zayyanar dan Faransa French, Louisa Marajo, ya baje zanen Palais de Justice a birnin Dakar.
Butum-butumin namiji launin bula, an yafa masa farin kyalle, ga kuma jan bulo kewaye a bayansa da wata kofa, ga kuma ganye ya zuba ta wata rila da aka sarkafa a sama.

Asalin hoton, Annika Hammerschlag

Bayanan hoto, A dai wannan ranar a wuri guda, an baje fasahar mai zayyana dan Faransa Beya Gille Gacha.
Dr Tedros ya na zubawa shugaba Kenyatta sinadarin kashe kwayoyin cuta, ya yin da shugaban na Kenya ya ke dariya.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Lahadi a birnin Geneva, daraktan hukumar lafiya ta duniya da aka sake zaba, Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus, yana zuba wa shugaban Kenya Uhuru Kenyatta sinadarin kashe kwayoyin cuta a hannu.
Sarauniya Silvia ta Sweden tare da Yanga Sobetwa.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Litinin kuwa, a Gripsholm Castle a Sweden, da mai zayyana 'yar Afirka ta Kudu, Yanga Sobetwa, ta dauki hoto tare da Sarauniya Silvia ta Sweden a lokacin bikin ba da kyautar World's Children's Prize, da ke gudanar da wani shirin bai wa yara ilimi.
Dakarun karramawa sun jeru reras, a lamarin da ya fi kama da maci, su na sanye da tufafin bai daya masu launin kunun kanwa da takunkumin rufe fuska.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wamshekare a birnin Pretoria, na Afirka ta Kudu, an yi wa shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz faretin ban girma...
Dalibai 'yan makaranta a wurin zanga-zanga. Sanye da kayan makaranta launin ruwan kunun kanwa...

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Laraba a birnin Johannesburg, dalibai 'yan makaranta na cikin wadanda sukai zanga-zanga kan wariyar launin fata a kofar ofishin hukumar kare hakkin dan adam ta Afirka ta Kudu......
Mace ta wuce ta wani bango da akai zane.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A dai wannan rana, wata mace ta wuce ta wani zabe da aka yi a gudumar Maboneng.
Wani mutum mai saida atamfofi a shagonsa.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Can Abidjan, da ke Ivory Coast, wani mutum ne a kan tsani ya jera atamfofi launuka da zane daban-daban a wani shago
Yara a tsaye su na watan kwallo da ake yi a teburi.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Can a wani bangare na birnin, yara na watan kwallo da ake yi a teburi.
Masu murmushi a wajen bikin kalankuwar Canes, Mayam ce a tsakiya tare da wasu mutum biyu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Alhamis a kasar Faransa kuwa, an warwasa ba kadan ba a lokacin da mai shirya fina-finai 'yar Moroccan Maryam Touzani, sun dauki hoto a wajen bikin kalankuwar fina-finai ta Canes.

Dukkan hotunan suna dauke da hakkin mallaka.