Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Taliban tana son a daina jin duriyar mata a Afghanistan - MDD
Babban mai bincike na musamman kan hakkin dan-Adam na Majalisar Dinkin Duniya a Afghanistan Richard Bennett, ya ce tarnaki da matakan takurawa da gwamnatin Taliban take sanya wa mata, tana yi ne domin ta sa a daina gani da jin mata a cikin al'ummar Afghanistan.
Mista Bennett ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da 'yan jarida a babban birnin kasar ta Afghanistan, Kabul a karshen rangadin kwana goma sha daya da ya je, ziyarar da ta kasance ta farko tun bayan da aka kirkiri gurbin aikin nasa.
Tun bayan da Taliban ta kwace mulki a bara, gwamnatinsu ta hana 'yan mata zuwa makarantun sakandare, yayin da su kuma mata manya aka hana su wasu ayyukan na gwamnati, sannan an haramta musu yin bulaguro ko tafiye-tafiye su kadai, ba tare da muharraminsu ba, kana kuma an umarce su da su rika rufe jikinsu gaba daya idan suka fito waje, ko kuma suna cikin jama'a.
Mista Bennett ya ce tsare-tsare da manufofin Taliban sun takaita sosai ko takura wa mata a 'yancinsu na walwala.
Ya ce, ''Na nuna matukar damuwa a kan tabarbarewar 'yancin dan-Adam a fadin kasar, da kuma kawar da mata daga harkokin jama'a abu ne na damuwa musamman.''
''Matakai irin su dakatar da ilimin sakandare, ilimin sakandare na 'yan-mata, shamaki mai tsanani ga aiki, ba dama ta shiga harkokin siyasa da aikin gwamnati, iyaka a 'yancin walwala, gamayya da bayyana ra'ayi, doka mai tsanani ta tilasta sanya hijabi, da shawara mai tsanani ta zama a gida sun zama daidai da tsarin cikakkiyar wariyar jinsi, kuma manufa ce ta sa a daina ji da ganin mata a cikin al'umma.'' in ji jami'in.
A ranar 7 ga watan Mayu ne fuskokin mata a Afghanistan suka fuskanci sabuwar dokar Taliban bayan sun sanar cewa dole ne mata su saka niƙabi a bainar jama'a karon farko cikin shekaru da dama.
Jami'an Taliban sun bayyana dokar da cewa shawara ce amma sun saka wasu dokoki kan duk wanda ya ki bin dokar.
Jami'an gwamnatin Taliban na kasancewa a shagunan sayar da tufafi na mata, inda suke sa ido kan abubuwan da mata masu shagunan ke sayarwa da kuma ko tsayin tufafin ya kai yadda hukumomi ke bukata.
Soraya mai kasuwancin karamin jari ba ta taba tunanin za a tilasta mata ba wata rana wajen saka nikabi kamar yadda Taliban ta yi a shekarun 1990.
"Abin bakin ciki ne cewa wasu mutane a kan titi su zo kaina su ce na rufe fuska ta," in ji ta, tana bayyana abin da ya faru lokacin da ta fita sayayya.
"Hatta telan da na je wajensa sai da ya nemi na rufe fuska ta kafin na yi magana da shi."
Da ma can ayawancin matan Afghanistan na saka tufafi masu kama da hijabi, amma dokar bayan sun kwace mulki ta bukaci mata su saka doguwar riga ko kuma nikabi da zai rufe fuska duka amma ban da ido.
Muharraminsu namiji ne zai dinga saka ido kan tufafin da za su dinga sakawa, ko kuma su fuskanci hukunci. Za a iya gayyatarsu don amsa tambayoyin hukuma da kuma daure su idan ta kama.
Wata kungiya ta yi zanga-zanga a Kabul a watan nan game da dokar saka kayan gargajiya da aka saka.
"Cikin wata takwas da suka gabata Taliban ba ta yi mana komai ba sai saka mana dokokin tufafi. Akwai matsalolin siyasa da na tattalin arziki amma Taliban ba wannan ne a gabanta ba," in ji Maryam, wata mai zanga-zanga.