Matan da suke so a daina kyama da tsangwamarsu idan suna jinin haila a fadin duniya

An wallafa

Sifaniya za ta zama ƙasa ta farko da za ta soma bayar da hutu ga matan da ke fama da raɗaɗin ciwo sakamakon al'ada.

Wannan kudirin, wanda aka tattauna a majalisa a ranar Talata 17 ga watan Mayu, na cewa akwai yiwuwar mata za su iya samun hutun kwanaki uku a duk wata idan suna fama da zafin al'ada kuma akwai yiwuwar hutun zai iya kai kwanaki biyar ga wadanda ciwonsu ya yi tsanani.

Sai dai ba a sa ran wannan hutun zai shafi matan da zafin al'adarsu bai da tsanani.

Wannan matakin na daga cikin wani babban kudiri kan batun lafiyar mata da kuma ƴancinsu na haihuwa wanda gamayyar masu ra'ayin gurguzu na ƙasar ke jagoranta.

Idan aka amince da wannan kudiri ya zama doka, zai zama irinsa na faro da aka taɓa samu a duk Turai.

"Ba mu son tattauna batun al'ada ya ci gaba da zama wani haramtaccen abu. Idan akwai matsala da ba za a iya shawo kanta ba ta hanyar magani, muna ganin yana da muhimmanci a samu hutun zuwa aiki," in ji Ángela Rodríguez, sakatariyar harkokin daidaito ta Sifaniya a yayin wata hira da kafafen yaɗa labarai na ƙasar.

Ƙasashe ƙalilan ne kacal a fadin duniya suka amince a shari'ance da bayar da hutu ga mata masu al'ada -akasarinsu a nahiyar Asia cikin har da Japan da Taiwan da Indonesia da Koriya Ta Kudu da kuma Zambia.

Doka ta farko da aka soma yi kan batun hutu ga masu al'ada ta samo tarihi ne tun a zamanin Tarayyar Soviet inda aka fito da ita a 1922.

Magoya baya sun ce mata na buƙatar irin wannan hutun kamar yadda suke buƙatar hutun haihuwa. Sai dai masu sharhi na nuna cewa irin wannan lamarin zai iya jawo tsangwama da kuma sanyaya gwiwar kamfanoni daga ɗaukar mata aiki.

Shirin BBC na mata 100 rabin muryar al'umma, ya tattauna da wasu mata a wasu ƙasashen da ke da irin waɗannan tsare-tsare na bayar da hutu ga mata masu al'ada domin sanin ko ana samun nasara.

'Abokan aikina maza kaɗan ne suka caccake ni'

Ma'aikaciyar gidan talabijin ta Indonesia Irine Wardhanie ta bayyana wa BBC cewa tun tana makarantar sakandire take fama da raɗaɗin al'ada. A halin yanu tana ɗaukar hutun kwanaki biyu a duk wata kuma ta buƙaci hakan ne daga wurin aikinta

"Kafin na fara al'ada ina samun ciwo sosai. Ina jin gajiya a tattare da ni kuma ina samun ciwon kai mai tsanani. Idan na fara al'ada, cikina na katsawa sosai. Ina jin amai da kuma zazzaɓi. Wannan na ɗaukar kusan kwana biyu zuwa uku," in ji Ms Wardhanie.

"Ki yi tunanin zuwa wurin namiji ya buƙaci hutun al'ada."

"Da farko na damu kan abin da sauran mutane za su rinƙa tunani, sai dai abin ba wahala tamkar tura saƙon e-mail zuwa shugabannina ne kuma suna bani goyon baya," in ji ta.

"Babu wata wahala a kamfanin da nake aiki, kawai tura e-mail nake zuwa shugabana domin sanar da shi. Shikenan.

"Wasu abokan aikina kaɗan ne kaɗai ke nuna rashin jin daɗinsu sakamakon suna kallon matakin a matsayin rashin adalci."

Ba kamar Irine ba, mata da dama a Indonesia ba su da masaniya kan wannan doka wadda ke bayar da dama a ɗauki hutun kwana biyu idan suna al'ada.

"Na yi magana da wasu mata da ke aiki a gidajen yaɗa labarai a Indonesia waɗanda ba su da masaniya kan wannan tsari wanda hakan ya tilasta musu su gudanar da ayyuknsu suna cikin zafin al'ada."

Akwai buƙatar ma'aikatu a Indonesia su bayar da hutun kusan kwanaki 24 a matsayin hutun al'ada.

"Wannan dokar kamfanoni na sarrafa ta ne yadda suka ga dama. Ma'aikatu da dama suna bayar da hutun kwana guda ne kawai a duk wata, wasu kuma ba su bayarwa," kamar yadda Ƙungiyar Ƙwadago Ta Duniya ta bayyana.

Vivi Widyawati na aiki ne kan batun ƴancin mata a ɓangaren ɗinki a ƙasar kuma ta ce ma'aikatan masana'antar da take aiki su samu hutun al'ada abu ne mai wahala fiye ga waɗanda ke aiki a shaguna da sauran wurin sayar da kayayyaki.

"Matan da ke aiki a irin waɗannan wurare ba su cika sanin batun hutun al'ada ba. Ɗaya daga cikin irin ƙalubalen da irin waɗannan matan ke fuskanta shi ne dole ne su samu takardar shaida daga likita," in ji Ms Widyawati.

"Sai su fuskanci barazana irin ta cin zarafi ta hanyar lalata ko kuma su ji kunya idan za su nemi irin wannan buƙata. Bugu da ƙari: kamfanoni da dama ba su son biyan kuɗi idan mace na hutun al'ada."

Mene ne zafin ala'da?

  • Akasarin mata waɗanda ke al'ada na jin zafi sai dai wasu suna samun zafi mai matuƙar raɗaɗi wanda ke jawowa su kasa kataɓus.
  • Ana jin zafin ne a mara inda za a ji kamar ciki yana katsawa wanda zafin ke bazuwa har baya zuwa cinya da kuma jin amai da gudawa da cieon kai.
  • Akwai abubuwa da dama da ke jawo zafin al'ada - misali rashin daidaito a a adadin ƙwayoyin halitta.
  • Bincike ya nuna cewa zafi da mata ke ji a lokacin al'ada abu ne da ake yawan samu, kuma wannan lamari yana kawo cikas ga yanayin ayyukan mata kuan kaso 20 bisa 100 na matan.