Zaɓen 2023: Yadda wakilan jam'iyyu ke cin karensu ba babbaka a Najeriya

An wallafa

Yayin da masu neman takarar shugaban kasa a jam'iyyun siyasa a Najeriya ke karaɗe jihohi domin ganawa da wakilai ko dalget-dalget, wani abu da ya fito fili shi ne yadda wasu wakilan kan yi bakin-ganga suna alkawarin kaɗa ƙuri`unsu ga duk wanda ya je gare su.

Irin wannan fuska biyun, kamar yadda masana siyasa ke zargi, akan yi ne don karɓar kuɗaɗe daga hannun masu neman takarar, wanda kuma a ƙarshe a cewar masana kimiyyar siyasa ka iya sa a yi zaɓen tumun dare.

Abu ne mai wahala a iya sanin ainihin inda wakilan a jam'iyyu daban-daban suka karkata, la'akari da galibin 'yan takara suke keɓewa da su.

Sai dai wasu masu sharhin siyasa a kasar na ganin cewa ba sabon abu ba ne a kasa gane inda wakilan suka dosa, ko kuma wane ne gwaninsu musamman a irin wannan lokaci da zaɓe ke gabatowa.

'Ana rashawa tsakanin deliget'

Masu sharhin irin su Farfesa Kamilu Sani Fagge na Jami'ar Bayero da ke Kano ya fada wa BBC cewa "ba wani abu ne sabo ba a siyasar Najeriya. Dama daya daga ummul haba'isin cin hanci da rashawa a zabe su ne deliget.''

''Ko wane dan takara idan ya zo deliget dinnan za su nuna za su goyi da bayan shi su karbi kudaden shi.

"Yan siyasa masu dabara sune su ke zuwa a karshe su ji na baya ɗan takara nawa ya ba da, to wanda ya fi ba su kudi a karshe shi suke jefawa kuri'a,'' a cewar Farfesa Fagge.

Da dama masu sharhin siyasar na ganin tun a wurin saben fitar da gwani a Najeriya ne 'yan takara ke fitowa da maitarsu a fili, da ke nuna cewa akwai yiwuwar su ci hanci da rashawa don sun fara nuna kurwarsu wurin raba kuɗi ga wakilan jam'iyya don su zaɓe su.

Kuma a cewar Farfesa Kamilu Sani Fagge irin wannan dabi'a ce ke sa ana zabar 'yan takara da ba su cancanta ba.

''Wanda ya saye deliget komai rashin kyawonsa shi za su zaba. Wanda kuma bai ba su kudi ba ko kuma ya ba su kudi kadan komai kyawunsa ba za su zabe shi ba," in ji shi.

Kuma yayin da ake batun fara zabukan fid da gwani a Najeriya, ba abun mamaki ba ne tuni wasu wakilan sun wasa wukakensu suna ci gaba da cinikin kuri'a kamar yadda aka saba tsakaninsu da 'yan takara.

A karshen wannan wata na Mayu da muke ciki ake sa ran gudanar da zaɓen fid da gwani da sanin kuwa mutanen da za su yi wa jam'iyyun Najeriya takara a matakai daban-daban.