Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rikicin Rasha: Ƙasar ta zargi kasashen yamma da kokarin bata mata suna
Fadar gwamnatin Rasha, Kremlin ta zargi kasahen yammacin duniya da amfani da majalisar hukumar kare hakkin dan-Adam ta majalisar dinkin duniya, wajen bata sunan Rasha bayan da hukumar ta kada kuri'ar amincewa da gudanar da binciken laifukan yaki a Ukraine.
Kasashe biyu ne kawai, China da Eritrea ne kadai daga cikin mambobin majalisar suka kada kuriar kin amincewa da a yi binciken.
Binciken zai mayar da hankali ne wajen nazarin zargin da ake yi cewa dakarun Rasha sun aikata munanan laifuka na keta haddi a arewacin babban birnin kasar, ta Ukraine, Kyiv, a farkon yakin da Moscow ta kaddamar bayan mamayar makwabciyar tata.
Shugabar hukumar ta kare hakkin dan-Adam ta duniya Michelle Bachelet ta ce, yawan kisan gillar da aka aikata abu ne mai tayar da hankali.
Sai dai jakadan China, kasar da ita da Eritrea suka kada kuriar kin amincewa da kudurin, a majalisar ta dinkin duniya ta yi korafi da cewa ana neman siyasantar da hukumar.
Rasha ba ta kada kuri'a ba saboda an dakatar da ita a watan da ya gabata.
Gissou Nia lauya ce ta kare hakkin dan-Adam, ta gaya wa BBC cewa sakamakon kuri'ar yana da muhimmanci:
Ta ce "Majalisar na yunkuri na gaske domin ta tabbatar da gaskiya. Akwai muhimanci ga matakin na neman tabbatar da gaskiyar ainahin wa ya aikata wadannan laifuka na keta haddi, wanda wannan abu ne da ba ko da yaushe muke gani ba a binciken hukumar ta kare hakkin dan-Adam.''
Yayin da hankalin duniya ya karkata ga yakin na Ukraine, shi kuwa shugaban hukumar kula da ayyukan jin-kai a Majalisar ta Dinkin Duniya, Martin Griffiths, cewa ya ce duniya ba ta lura sosai ga sauran rikice-rikice da ke wakana a sassan duniya banda yakin na Ukraine ba.
Mista Griffiths ya bukaci kasashe da hukumomin duniya da kada su kawar da kai daga mummunan farin da ake fama da shi a gabashin Afirka.
Shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya ce mutane miliyan 20 a yankin na cikin hadarin fadawa cikin tsananin yunwa.
A yayin ziyarar da ya kai ranar Alhamis, wasu yankuna da ke fama da matsalar karancin abincin a Turkana da ke Kenya, shugaban ya gana da al'ummomi wadanda suka gaya masa cewa tuni su ma riga sun saba da tsananin yunwa, a don haka suna bukatar taimakon gaggawa