Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
KwaZulu-Natal floods: Iyalin da suka rasa yara tara a ambaliyar ruwa lokaci guda
Har yanzu yankin KwaZulu-Natal na Afirka ta Kudu bai gama farfaɗowa ba daga ambaliyar ruwa mafi muni cikin shekara 60, wadda ta kashe mutum aƙalla 435 a watan Afrilu. Ana ci gaba da yi wa mutane da yawa jana'iza a lokaci ɗaya.
Duk da haka wasu dangin sun kasa binne 'yan uwansu saboda ruwa ya tafi gawarwakinsu. Wakilin BBC Pumza Fihlani ya aiko da wannan rahoton daga yankin.
Cikin wani tanti da ke kan dutse 'yan taku kaɗan zuwa wajen Pietermaritzburg, wasu ɗaruruwan mutane ne ke zaune gaban akwatinan gawa shida, kansu durƙushe suna ta yin addu'o'i.
Wani abin alhini ya faru ga iyalan Mdlalose. Slindile Mdalose mai shekara 43 da kuma yara tara masu shekarau biyu zuwa 10 sun mutu a ambaliyar ruwan da ta ɗaiɗaita KwaZulu-Natal.
Suna tsaka da barci lokacin da ruwan ya cim musu, inda ya shafe gidansu. Mako uku ke nan amma har yanzu ba a ga gawar wasu daga cikinsu ba.
"Na faɗa maka gaskiya har yanzu a ɗimauce muke, ba mu da ta cewa. Ba mu da wani tunani. Wannan abin ya yi griman da mun kasa fahimtarsa ma," a cewar kawun yaran mai suna Thokozani Mdlalose.
"Idan ka yi yunƙurin kawar da tunaninka wani wajen sai ka tuna wannan, sai ka tuna wancan. Abin ya yi yawa. Abu ne mai girma rashin mutum ɗaya. Mafi muni shi ne rashin mutum. Rashin mutum 10 kuma wani abu ne daban."
An yi jana'izar Slindile Mdalose da yaranta biyar - Uyanda, Lubanzi, Ziyanda, Asanele, Lulama - a wata safiya. Kazalika, ita ce gwaggon sauran yara huɗu waɗanda har yanzu ba a gan su ba.
"Ganin cewa har yanzu ba mu gan su ba, cewa ƙila suna can suna ruɓewa a wani wajen - ba zan iya faɗar abin da ke cikin raina ba a yanzu. Na kasa ma gane me nake tunani," in ji Mista Mdlalose.
Ya ƙara da cewa yaran tara na da son wasa da kuma ban-dariya, kuma suna saka wa danginsu farin ciki.
Gwaggonsu mai suna Nonkululeko Mdlalose ta ce lokaci na ƙarshe da ta yi magana da 'yar uwarta a waya mintuna kaɗan su rasu ta ji alamun tana cikin tsoro.
Ana ta zabga ruwan sama fiye da yadda suka taɓa gani. Duk da haka ba su yi tunanin hakan zai zama wani bala'i ba, a cewar Nonkululeko Mdlalose.
"Ban taɓa jin irin wannan baƙin cikin ba. Na zaci ina da ƙarin zuciya amma na gano ba ni da shi, muna buƙatar taimako, na lura cewa muna buƙatar shawarwari. Wannan abu ne mai girma ga kowane ɗan Adam," kamar yadda ta bayyana.
Ba su kaɗi ne ke cikin alhini ba. Ambaliyar ta kashe mutum 435 sannan har yanzu wasu gwammai sun ɓace, abin da ya saka danginsu cikin matsanancin hali.
An binne ƙasa da 200 zuwa yanzu, kuma akwai aƙalla gawa 59 da har yanzu ba a samu masu su ba.
Kamfanin binne gawa na Icebolethu Funeral Services, ɗaya daga cikin mafiya girma a KwaZulu-Natal, sun binne mutum fiye da 70 zuwa yanzu.
Ɗaya daga cikin shugabannin kamfanin, Mthokozisi Bhengu, ya ce gawarwakin ba sa cikin yanayi mai kyau saboda ruwa ya lalata su, kuma suna buƙatar a binne su cikin gaggawa don guje wa ƙara lalacewarsu.
"Iyalai na da al'adu da suke son yi, kamar binne kowa a lokaci guda, amma dole muke shawartar waɗanda 'yan uwansu suka ɓace cewa yayin da suke ci gaba da nemansu, mu dinga binne waɗanda suke mutuware a yanzu don rufa musu asiri," in ji shi.
Game da gawarwakin da ba a samu masu su ba, gidajen jana'iza sun ce har yanzu ba a cimma matsay ba a kansu.
Ɗaya daga cikin zaɓin da ake tunani shi ne ɗibar ƙwayoyin halittarsu na DNA don a ajiye bayanan ta yadda idan danginsu suka zo nemansu za su iya samu - wani abu da zai iya rage musu raɗaɗi.
Gwamnati da ƙungiyoyin ba da tallafi sun nemi ba da tallafi don rage wa iyalai kuɗaɗen jana'iza. Amma an ce hanyoyin samun tallafin na da wuya kuma yana jawo tsaiko wajen gudanar da jana'iza.
"Nan gaba ya kamata gwamnati ta turo ƙwararru a kowane rikici irin wannan tun daga farko, su fada mana yadda ya kamata a tafiyar da lamarin," a cewar wata shugabar gidan binne gawa.
Ms Mcoyi ta ƙara da cewa jinkirin da hakan ke haifarwa na ƙara wa iyalai nauyi.
Magajin garin Kwazulu-Natal, Sihle Zikalala, ya ce gwamnati na ƙoƙarin tallafa mabuƙata.
Game da sake gina gidajen iyalai kamar na Mdlaloses, ya ce gwamnatin na duba inda za a samu filin da ya dace da za a tsugunar da waɗanda suka rasa gidajensu.
Shugaba Cyril Ramaphosa ya ce ana buƙatar ƙarin kuɗaɗe fiye da dala miliyan 68 da aka ware don gyara yankin na KwaZulu-Natal.
Abu ne da zai ɗauki lokaci ga mazauna wannan yanki - daga waɗanda suka rasu 'yan uwansu zuwa ga waɗanda suka rasa muhallansu. Yayin da ɓarnar da ambaliyar ta haifar ke ci gaba da bayyana, da yawa na buƙatar duk wani tallafi da za su iya samu.