Ambaliyar ruwa a Durban: Ruwa ya ci mutane fiye da 300 a Afirka ta Kudu

    • Marubuci, Daga Shingai Nyoka
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Durban
  • An wallafa

Adadin wadanda suka mutu a yankin KwaZulu-Natal ya kai 300, sakamakon mummunar ambaliyar ruwan da ta faru a yankin.

Hukumomin yankin sun yi kira a ayyana lamarin a matsayin babban bala'i, bayan wasu yankunan sun fuskanci ruwan saman wata guda a kwana daya.

Jami'ai sun yi bayyana lamarin a matsayin bala'i da guguwa hade da ruwan sama mafi muni a tarihin kasar.

Zabtarewar kasa ta janyo mutane da dama sun makale a gine-gine, yayin da ake sa ran karuwar ambaliyar ruwa.

Rahotanni sun bayyana cewa aikin ceto na fuskantar cikas sakamakon rashin kyawun yanayi, amma jirgin helikwafta na ci gaba da dauko mutane da kai su tudun-mun-tsira.

A ranar Talata, BBC ta ga yadda aka yi aikin ceton wata yarinya 'yar shekara 10, wadda tana cikin iyalan mutum hudu da ambaliyar ta rutsa da su a kan wata gada.

Masu aikin sa-kai sun yi kokarin shiga cikin tabon, da kokarin rike rassa bishiya, da amfani da adda wajen kawar da baraguzan gine-ginen da suka toshe hanya domin isa inda take.

Jomba Phiri, wanda ke zaune a babban birnin Durban, ya ce ambaliyar ta yi awon gaba da gidajen jama'a.

"Ban san inda za mu kwana ba," kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Babbar hanyar da za ta sada ka da birnin Durban, ta dangana da yankin Gauteng mai hada-hadar kasuwanci baki daya baraguzai sun toshe ta.

Shugaba Cyril Ramaphosa ya kai ziyara yankin da alkawarin taimaka wa wadanda lamarin ya shafa.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato shugaban na cewa, "Duk da zukatanku na cike da bakin-ciki, za mu taimaka muku."

Ya kuma bayyana lamarin da matsalar sauyin yanayi, lamarin da mutane da dama ba su amince da shi ba. Sun dora alhakin hakan ga rashin kyauwun magudanar ruwa, da gina gidaje ba bisa ka'ida ba musamman a kwari kuma nan ne aka fi samun mutuwar mutanen.

Magajin garin Durban Mxolisi Kaundaya musanta cewa rashin kyawun magudanan ruwa ne ya haddasa ambaliyar, inda ya ce babu wanda ya tsammaci aukuwar ambaliyar.

Ana ci gaba da ganin yadda ambaliyar ta daidaita yankin. Ruwa ya mamaye kusan yawancin hanyoyin da za su sada ka da tashar ruwan Durban, tabo da tarkace sun cika titunan. Tuni aka dakatar da hada-hada a tashar ruwan. Ambaliyar ta lalata wani sunduki da ke ajiye a wani wurin ajiye kayayyaki, yayin da ruwan ya yi gaba da daruruwan kwantenonin da ke wurin.

A yankin Bluff mai cike da masana'antu, BBC ta ga yadda motoci suka yi taho-mu-gama da yamutsewa cikin baraguzai. Kamfanoni na amfani tiyo wajen kauda tarkacen da suka watsu a ciki.

Ana kuma farautar wasu kada, da ruwan ya yi awon gaba da su.

Gonar kada ta Creek Farm, mai nisan kilomita 40 daga arewacin Durban a Tongaat, sun ce ambaliyar ta yi gaba da kada 12.

Wani malamin coci da ke yankin, Ron Naidoo da ke garin Tongaat ya shaidawa BBC bai runtsa ba sakamakon yadda ruwan ke zuba da karfin gaske, da ambaliayr da ya ke yi, ya kuma 'yan sanda sun janyo wata mota daga cikin kogin da ke kusa da inda yake.

"Lamari ne mai tada hankali, saboda wannan ne karon farko da muka ga kogi ya tunbatsa haka," in ji limamin cocin.

A wata sanarwa da gwamnatin KwaZulu-Natal ta wallafa a shafin Facebook, ta yi kiyasin ambaliyar ta janyo asarar biliyoyin rand, da lalata ayyukan ababen more rayuwa da gine-gine, da bayyana ambaliyar da ba a taba gani ba cikin shekaru da dama.

Magajin birnin Durban ya ce turakun wutar lantarki duk sun shafe.

Kafar sadarwa ta yanke, ya yin da manyan kamfanonin sadarwa biyu na kasar suka ce sama da turakun sdarwa 900 da ke kasar duk ambaliyar ta jijjigesu.

Baitil malin Afirka ta Kudu ya ce ayyana yankin cikin dokar ta baci da kiran a kawo musu dauki, da gyaran hanyoyi da kwashe bishiyoyi da gine-ginen da suka fadi.

Wasu rahotanni sun ce an samu sace-sacen kayan mutane a Durban, gwamnatin yankin ta yi allawadai da hakan: "Ba za mu taba amincewa da satar kayan mutane alhalin mu na cikin wani ibtila'i ba, dole mu dauki matakin gaggawa kan haka."

Gwamnati na kira ga mutane su zauna a gida, da kaucewa bin hanyoyin da ambaliyar ta shafa, sannan idan da hali su koma kan tudu inda babu wata barazana ko da ruwan sama ya sake kecewa.

Ambaliyar da guguwar na zuwa ne bayan masana kiimiyya sun yi gargadin sauyin yanayi da tsananin zafi da zubar ruwan sama ka iya zama gagarumar barazana a Afirka ta Kudu.

Daga farkon wannan shekarar, yankin ya yi fama da manyan guguwa uku cikin makonni shida, wadda ta fi shafar kasashen Madagaskar, da Mozambique da Malawi, tare da lalata ababen more rayuwa da mutuwar mutum 230, kamar yadda hukumar kula da yanayi ta duniya ta bayyana.