Fitattun hotunan Afirka na mako: 29 April-5 May 2022

An wallafa

Zababbun hotunan mako na sassan Afirka:

Short presentational grey line
'Yan mata cikin kwale-kwale a tafkin Victoria a Uganda -Litinin 2 Mayu 2022

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Matasan mata a cikin kwale-kwale a tekun Victoria da ke babban birnin Uganda wato Kampala a ranar Litinin.
Maza na sayan hula a birnin Dakar, Senegal - Juma'a 29 Afirilu 2022

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Maza Musulmai a birnin Dakar na Senegal, suna sayan Hula da aka fi sa ni da "kufis" a kusa da wani masallaci a ranar Juma'ar karshe ta watan azumin Ramadan.
Mace daure da kwarkwaron nannade gashi a wurin gyaran gaji da ke Bujunbura a Burundi Litinin 2 Mayu 2022

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wata mace a wurin wanke gashi da ke birnin Bujumbura a kasar Burundi, ranar Litinin a wani bangare na bukukuwan Sallar Idi bayan kammala Azumin Ramadan…
Wasu iyalai na dunba kyakkyawan yadi mai launin sararin samaniya a wani shago da ke Khartoum, a Sudan - Juma'a 29 Afirilu 2022

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Lokacin sallar Idi Musulmai na cancada ado - wasu iyalai sun zo wani kanti domin sayan kayan sallah a birnin Khartoum, na Sudan ranar Juma'a.…
Tela ya na dinki a birnin Khartoum, a Sudan - Juma'a 29 Afirilu 2022

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wani tela na dinki a bangaren shagalin sallah karama...
Mata na daukar hoto a Lagos, Najeriya - ranar Litinin 2 Mayu 2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Birnin Lagos ranar Litinin - lokacin da Najeriya ta bi sauran kasashen Afirka ranar sallar Idi, mata na daukar hoton salon dauki da kan ka a wajen wani masallaci....
Yara maza uku sanye da kyawawan tufafi da tabarau ranar Litinin 2 Mayu 2022

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A birnin Maiduguri na jihar Borno a arewacin Najeriya, cibiyar mayakan Boko Haram, wadannan yaran na sanye da tabarau launi daban-daban a ranar Idi..…
Hawan sallah, ranar durbar, a jihar Kano da ke arewacin Najereiya… - Litinin 2 Mayu 2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hawan sallah, ranar durbar, a Jihar Kano da ke arewacin Najereiya…
Yara zaune kan rakumi a birnin Nairobi na Kenya - Litinin 2 Mayu 2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Birnin Nairobin Kenya- yara maza da mata sun dare kan rakumi domin nishadin zagayowar ranar sallah…
Ana iya ganin masu girka abinci a manyan kwane wuta na ci a murhu a birnin Cape Town, ranar Litinin 2 Mayu 2022

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A birnin Cape Town na Afirka ta Kudu kuwa, masu aikin sa kai ne ke girka abinci a manyan tykwane a wani yanki da ya yi fama da wariyar launin fata a bangaren shirye-shiryen sallah.…
Balan-balan a sararin samaniyar masallacin Tunis, a Tunisia -Litinin 2 Mayu 2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An saki balan-balan launi daban-daban a sararin samaniya a wani masallaci a birnin Tunis na kasar Tunisia ranar Idi…
Daliban makarantar islamiyya da gidan marayu na Kabowa Hidayat a Kampala, Uganda - Litinin 2 Mayu2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yara na kallon balan-balan a makarantar islamiyya ta marayu Turkish Islamic school a Uganda ranar Litinin...... Yawancin daliban 'yan gudun hijirar Somalia ne......
Yara mata kan lilo mai shillo a Mogadishu, Somalia - Litinin 2 Mayu 2022

Asalin hoton, Ronald Grant

Bayanan hoto, A nan kuma Mogadishu ne, yara mata na wasan lilo mai shillo a ranar Idi a Somalia.
Rached Ghannouchi a Tunis, kasar Tunisia - Juma'a 29 Afirilu 2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Juma'a, tsohon dan siyasa a Tunisia Rached Ghannouchi, kuma tsohon kakakin majalisar dokoki da shugaba Kaïs Saïed, an dauki hoton tsakanin karafa.
Wata mace na tsalle hannu sama cikin murna a sansanin 'yan gudun hijira da ke Ouallam, a jamhuriyar Nijar - Talata 3 Mayu 2022

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ziyarar sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres a wasu kasashen Afirka - wata mace ke tsallen murna da maraba lale gare shi a ranar Talata, lokacin ziyara sansanin 'yan gudun hijira da ke Nijar, wanda rikicin boko haram ya raba da muhallansu.
Mace sanye da hula mai hoton marigayi Mwai Kibaki a filin wasa na Nyayo da ke Nairobi, Kenya - Juma'a 29 Afirilu 2022

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ranar Juma'a wata mace a lokacin binne tsohon shugaban Kenya marigayi Mwai Kibaki a filin wasa na Nyayo a Nairobi', wanda manyan mutane a ciki da wajen kasar suka halarta.
Mai kayan kawa sanye da rigar da aka rubuta "Still No... Respectfully" a makon kawa na Afirka ta Kudu, da aka yi a Johannesburg - Juma'a 29 Afirilu 2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A dai wannan rana, wata mai tallan kayan kawa a birnin Johannesburg a kasar Afirka Ta Kudu…
Mutane na kallo bikin kayan kawa na mako a Afirka ta Kudu, domin baje kayan shekarar 2022, a Johannesburg, Afirka ta Kudu - Juma'a 29 Afirilu 2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rana ta biyu na makon kawa a Afirka Ta Kudu domin baje kolin kayan shekarar 2022…
Mai tallan kayan kawa lokacin baje kolinsu a bikin da aka yi na mako guda a birnin Johannesburg, na Afirka ta Kudu ranar Juma'a 29 Afirilu 2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An baje kolin kayan kawa masu kayatarwa a lokacin bikin.
Mutane da aka yi musu fantin fuska a Ivory Coast - ranar Asabar 30 Afirilu 2022

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ranar Asabar a Ivory Coast, an yi bikin kalankuwa na Bonoua, wanda aka bayyana da sunan Mardi Grasda aka yi na mako guda........
Wani na cin wuta a bikin gagrgajiya na mutanen Bonoua, a Ivory Coast - 30 Afirilu 2022

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Bikin al'adun gargajiya na mutanen Aboure...
Bikin kalankuwa na Popo"Ebe" (maza kyawawa) a Bonoua, Ivory Coast - 30 Afirilu 2022

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Bikin kalankuwa mai suna Popo, ya hada mutane gasa daban-daban, kama daga dafa abinci, wasanni, rawa da zaben sarauniyar kyau. Wadannan mazan ana kiransu da "Ebe"an zabe su a matsayin mazan da suka fi kowa kyau na wannan shekarar.
Ranar Alhamis, mambobin rundunar tsaron Habasha sun gudanar da fareti a wani biki a birnin, Addis Ababa. - Alhamis 5 Mayu 2022

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Alhamis, mambobin rundunar tsaron Habasha sun gudanar da fareti a wani biki a birnin, Addis Ababa.
Wata mace na daukar hoton dauki da kan ki a birnin Lagos, na Najeriya - Lahadi 1 Mayu 2022

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A karshe an dauki wannan hoton a birnin Lagos din Najeriya a ranar Lahadi, wani bangare na bikin ranar ma'aikata ta duniya.

Dukkan hotunan suna dauke da hakkin mallaka.