Yarjejeniyar Birtaniya da Rwanda: 'Shin gwamnatin Birtaniya za ta tura ni zuwa kasar da ake mulkin kama-karya?'

    • Marubuci, Daga Daniel Henry
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Dan jaridar BBC
  • An wallafa

Lokacin da na tafi yi wa shirin BBC Focus on Africa aiki a Calais, ban taba tsammanin ganin wani wurin cacar casino ba.

Wannan birni na kasar Faransa mai tashar jiragen ruwa da wuya a danganta shi da caca, amma casino din da muka gani a wajen otal din da muka zauna ya nuna cewa mutanen da muke ganawa da su za su iya tarar- aradu-da-ka, da fatan samun wata babbar sa'a - shiga kasar Birtaniya kai-tsaye.

Mun shafe tsawon lokaci da mutanen da ke daukar wannan sansanin da aka kakkafa a matsayin gida.

A shekarar 2016 ne hukumomi suka amince da wurin a hukumance - amma kungiyoyin bayar da agaji sun bayyana cewa har yanzu mutane 1,500 ne ke zaune a daya daga cikin wurin da muka ziyarta.

Neman makoma mai kyau

Kusan kowa a nan na da nashi burin na shiga kasar Birtaniya. Irfan* bai bambanta ba a wannan buri - amma har yanzu ya fita daban.

Ba kamar kowa ba, wannan matashi da ya nuna alamun kadaici - har sai da wani mai tafinta ya je gare shi.

Ya bar kasar Eritrea watanni 18 da suka gabata - a wani bulaguro mai cike da hadari da ya kai shi zuwa kasashen Libya, da Italiya da kuma Belgium.

Mai shekaru 16 ya bayyana cewa ya tsere daga kasar don neman makoma mai kyau.

"Babu 'yanci a Eritrea kuma idan ka kai shekaru 18 dole ka shiga aikin soja," in ji shi.

Muna son mu gano idan yarjejeniyar tsakanin gwamnatocin Birtaniya da Rwanda za ta yi wani tasiri a kan burin da yake da shi.

Komawa kasar Rwanda

Sabbin zuwa wadanda suka ketare tekun Ingila suna cikin wadanda za a tura kasar don neman mafaka da gina sabuwar rayuwa a kasar Rwanda.

Gwamnatin Birtaniya ta bayyana cewa sabbin dokokin za su taka wa mutane birki daga yin irin wannan bulaguro - amma masu fafutika sun nuna ja a kan cewa mutane irin su Irfan sun rungumi amfani da kwale-kwale da manyan motoci don shiga kasar Birtaniya, saboda ba za su iya neman mafaka ba har sai sun shiga cikin kasar ta Birtaniya.

Ifran ya bayyana min cewa bai samu yin magana da iyalansa ba har na tsawon watanni biyu.

"Iyalai na ba su san a inda nake ba, babu wata hanyar sadarwa tsakaninmu."

Mai yin tafintar, wani ma'aikaci a daya daga cikin kungiyoyin bayar da agaji da ke taimaka wa masu neman mafaka a Calais, ya fara damuwa lokacin da yake fassara kalaman Ifran.

Ya sunkuyar da kansa, ya shake kana ya fara kuka. Na duba ko in ga lafiyarsa lau, ya gyada kai.

Mai tafintar kara natsuwa. Sai muka cigaba da tattaunawa.

"Ina kewar 'yan uwana. Na shafe shekara daya a kan hanya yanzu, ban san me ke faruwa da su ba," tafintar ya cigaba da fassara kalaman da Ifran ya furta a baya.

"Me zai faru idan aka gano ka kuma aka tasa keyarka zuwa kasar Rwanda?" Na tambaye shi.

"Shin gwamnatin Birtaniya za ta tura ni Rwanda? Akwai kama-karya a can."

"Idan suka dage, ba na jin zan zauna a Rwanda."

Rwanda kasa ce da kungiyar kare hakkin biladama ta Human Rights Watch ke dauka a matsayin kasa mai mulkin mallaka. Paul Kagame, shugaban kungiyar hadin kan Afirka ya kasance a kan mulki tun a shekarar 1994, kana baya ga shirinsa na dawo da zaman lafiya a kasar Rwanda bayan rikicin kabilanci da kisan kare dangi, an zarge shi da tafiyar da kasar a tsari na jami'iya daya.

Zama a Calais cikin tantina

Irfan ya zaku ya samu mafaka a Birtaniya, bayan da ya yi amanna za a fi kulawa da shi a can fiye da kasar Faransa.

Calais ya kasance wata cibiyar matsalolin masu kaura a Turai. Mutane a nan na yunkurin shiga Birtaniya ta hanyar bulaguron jirgin ruwa mai cike da hadari, ko ta cikin jiragen kasa da manyan motoci.

A watan Yulin shekarar 2016, watanni uku kafin mahukuntan Faransa suka rushe sansanin, wani shirin kidayar jama'a da wata kungiya mai zaman kan ta Help Refugees ta gudanar tya kididdige cewa mutane sama da 7,000 ne ke zaune a can.

A cikin wadannan kwanaki, Irfan da sauran mazanuan sansanin a Calais cikin tantina da dakunan da aka kakkafa da suka hada da gine-ginen da aka bari a kuma karkashin gada.

Yanayin na ban tausayi ne kana samun ababan more rayuwa sun yi karanci.

Babu wanda yake son zama a nan, amma suna nan. Kana suna cike da burin samun sabuwar rayuwa a Birtaniya.

"A Birtaniya ana kula da mutane, za su iya zuwa makaranta," in ji shi.

'Yan gudun hijirar kasar Ukraine

Tare da taimakon kungiyoyin bayar da agaji da fasahar zamani, masu neman mafaka a Calais na da masaniya kan abubuwan da ke faruwa a wajen sansanin. Kana ana dasa ayar tambaya kan kulawar da ake yi wa 'yan gudun hijirar kasar Ukraine.

"Ba za mu hada kan mu da 'yan kasar Ukraine ba. Suna zaune a otal,'' in ji wani matashi da ya yi magana da mu.

"Su [mahukuntan kasashen Turai] bas u damu da mu kamar yadda suka damu da 'yan kasar Ukraine ba."

"Idan suka yi kokarin tura mu kasar Rwanda, babu wanda zai amince da haka," ya kara bayyanawa.

Matasan da muka tarar sun yi amanna akwai nasarori a nan gaba - cewa tafiya mai hadarin da suka yi za ta zama musu alkahiri wata rana.

"Rayuwar akwai wahala, amma mun koyi yadda za mu saba da ita. Komai zai yi kyau," in ji Irfan.

Shi da sauran ba su san yaushe ko ta yaya ba.

*An sauya sunan matashin ne a bisa bukatarsa.