Dalilin da ya sa dokar harajin latironi a Ghana ke jawo ɓacin ran 'yan ƙasar

Nana Adwoa Animfu posing in front of her wig stall in Accra, Ghana.
    • Marubuci, Thomas Naadi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Accra
  • An wallafa

Nana Adwoa Enninful ta baje kolin gashi a tsakiyar babbar kasuwar Makola da ke birnin Accra na Ghana.

Matar mai shekara 59 na sayar da gashi da ake ƙarawa da sauran abubuwa a shagonta.

Tana gudanar da wasu harkokin nata ne ta wayar salula, wata hanya da ake amfani da ita ta latironi da ke bai wa waɗanda aka yi wa rajista damar ajiyewa da turawa ko kuma karɓar kuɗi a asusunsu.

Wannan tsarin biyan kuɗin ya fi sauƙi da sauri, sannan ya fi hanyar bankuna da aka fi sabawa da ita tabbas, a cewar Enninful.

Sai dai, ƙaddamar da dokar karɓar kashi 1.5 cikin 100 na dukkan harkokin kuɗin latironi da suka zarta kuɗin Ghana cedi 100 - wanda aka fi sani da e-levy a Turance - ya saka ta cikin damuwa. Dokar ta fara aiki ne daga 1 ga watan Mayu.

"Dole ne sai mun ƙara kuɗin harajin latironi kan farashin kayayyaki, wanda hakan zai sa hauhawar farashi," kamar yadda ta faɗa wa BBC.

"In ba haka ba sai dai mu koma karɓar tsabar kuɗi, amma kuma hakan ba sauƙi ba ne saboda akan ba mu kuɗaɗen jabu ko kuma a dinga yi mana ƙwange."

Ms Enninful ɗaya ce daga cikin 'yan kasuwa da dama da ke da damuwa game da harajin na latironi.

Kazalika, harajin ya shafi dukkan kuɗaɗen da aka tura ta banki da wayoyin salula.

Masu sukar dokar na cewa za ta fi shafar masu ƙramin ƙarfi ne kawai da kuma masu ƙananan sana'o'i saboda su ne suka fi dogara da waya wajen harkokinsu.

A shekarar da ta gabata, muahwara kan dokar ta haddasa naushe-naushe a majalisar Ghana. Daga baya dai an amince da ita amma bayan 'yan majalisar adawa sun fice daga zauren majalisar.

Bankuna ba su da yawa a ƙauyuka, sannan ana ganin amfani da waya ba ya cin kuɗi sosai kuma asusun salula ba ya ɗaukar wasu kuɗaɗe masu yawa.

Sakamakon haka, akasarin 'yan Ghana kusan kashi 40 cikin 100 masu shekaru 15 zuwa sama ke amfani da waya wajen harkokin kuɗinsu.

Tuni alamu sun nuna cewa mutane sun fara janyewa daga amfani da manhajojin latironi wajen biyan kuɗi. Babban Bankin Ghana ya ba da rahoton cewa masana'antar ta yi asarar dala biliyan ɗaya cikin wata biyu daga watan Nuwamba saboda mutane sun fara amfani da tsabar kuɗi don kauce wa biyan harajin da ake shirin ƙaddamarwa.

Gwamnati na ta yunƙurin haɓaka tattalin arzikinta na latironi a 'yan shekarun nan sama da na tsabar kuɗi. Amma yanzu ta amince cewa dokar harajin za ta haifar da babbar raguwa wajen amfani da waya a farkon fara amfani da dokar.

Mataimakin Ministan Kuɗi John Kumah ya faɗa wa wata kafar yaɗa labarai cewa "za a samu raguwa ta kashi 24 cikin 100 a wata ukun farko zuwa shida na ƙaddamar da dokar".

"Binciken ya nuna mana abin da za mu yi wajen dawo da mutanen bayan ɗan lokaci, kuma mun tanadi dukkan waɗannan abubuwa," in ji shi.

Da yawan harkokin tattalin arzikin Ghana na faruwa ne ta hanyoyin da ba na hukuma ba kuma kashi 10 cikin 100 ne kacal na al'ummarta ke biyan haraji.

Cikin wata hira da ya yi da BBC a kwanan nan, Shugaban Ghana Nana Akufo Addo ya ce gudunmawar da haraji ke bayarwa wajen haɓaka tattalin arziki na cikin gida bai wuce kashi 13 ba cikin 100 - wanda ya yi ƙasa sosai in aka kwatanta da sauran nahiyar Afirka ta Yamma masu 18 a ma'aunin tsakatsaki. Akasarin ƙasashen Turai na da kashi 35 zuwa 45, yayin da Amurka ke da 25.

"Muna magana ne kan karɓar haraji daga masana'antar da ke samar da dukiya kuma muna so mu samar da irin wannan dukiyar a ɓangaren gwamnati," a cewarsa.

An yi ƙiyasin cewa an yi hada-hadar kuɗi ta wayar salula da ta kai dala biliyan 126, amma gwamnati na fatan harajin latironin zai samar mata da dala biliyan ɗaya a wannan shekarar.

Wasu ƙwararru sun ba da shawarar bin wasu hanyoyin don samar da kuɗin shiga.

Sake fasalin haraje-harajen da ake karɓa yanzu, kamar "na kamfanoni, da na ɗaiɗaikun jama'a, har ma da na VAT" zai taimaka wa gwamnati samun ƙarin kuɗaɗe, a cewar Farfesa Godfred Bokpin na Sashen Kasuwanci a Jami'ar Ghana.

Iriin waɗannan haraje-harajen da aka ƙaddamar a Kamaru da Zimbabwe sun tayar da ƙura.

A 2019, Zimbabwe ta fito da kashi 2 cikin 100 na harajin tura kuɗi da ya ƙi karɓuwa a ƙasar.

A Kamaru ma, yunƙurin saka harajin kashi 0.2 na tura kuɗi ta waya ya haifar da tayar da jijiyoyin wuya da ya sa aka ƙirƙiri yekuwa a shafukan zumunta mai maudu'in #EndMobileMoneyTax. Duk da haka sai da gwamnati ta aiwatar da shi a Janairun shekarar da ta gabata.

Ita ma gwamnatin Tanzania na shirin fara cirar harajin intanet. Wata tawagar ƙwararru daga kamfanin Meta - kamfanin da ya mallaki Facebook, da Instagram, da WhatsApp - ya ziyarci cibiyar kasuwanci ta birnin Dar es Salaam don tattaunawa da mahukunta kan yadda za a saka wa harkokinsu haraji a ƙasar.

Akwai yiwuwar sauran ƙasashen Afirka da ke neman farfaɗowa daga tasirin annobar korona kuma suke fuskantar tasirin yaƙin Rasha a Ukraine za su mayar da hankali kan harajin latironi don tara kuɗi, duk da abin da haifar wa 'yan ƙasa.

"Ina da damuwa ƙwarai a kan harajin latironi. Gwamnati ba ta wayar mana da kai yadda ya kamata ba game da shi," a cewar James Mawuli da ke aiki a matsayin mai tallan harkokin kuɗi ta waya.

Mobile money dealer
Bayanan hoto, Dubban mutane na aiki a matsayin masu tura kuɗi ta waya a Ghana

Ɗan shekara 32 ɗin na taimaka wa muatane ajiye kuɗaɗensu a wayar salula da kuma cire tsabar kuɗin idan suna buƙata.

Ya ce tuni ya fara rasa kwastomominsa saboda sabon harajin na latironi, har ma yana fargabar zai iya rasa sana'ar tasa kwatakwata.

'Yan majalisar adawa sun fara ƙalubalantar sahihancin dokar a gaban Kotun Ƙoli.

Ana sa ran za a yanke hukunci a cikin farkon watan Mayu.