Yadda Singapore ke shirin daskarar da kwayayen haihuwa don taimaka wa ma'aurata

    • Marubuci, Daga Yvette Tan
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Singapore
  • An wallafa

Bayan shafe shekaru ana muhawara, a watan da ya gabata kasar Singapore ta sanar da cewa za ta dage haramcin da ta yi wa matan da ba su da miji da ke son daskare kwan mahaifarsu kan dalilan da ba na kiwon lafiya ba.

Amma a yayin da wasu suka yi lale marhabun da wadannan matakai, wasu cewa suke yi matakin har yanzu na bukatar tsare-tsaren nuna cewa har yanzu Singapore na da sauran aiki a gabanta kafin a duba yiwuwar wannan manufa da gaske.

Shekarun Gwendolyn Tan 31 lokacin da ta yanke shawarar daskarar da kwan mahaifarta.

Ma'aikaciya ce wacce ba ta da miji, da ta dade tana son ganin ta haifi 'ya'ya - amma ba ta samu ba saboda har yanzu ba ta da abokin zama.

Hanya mafi dacewa da ta fi mata itace ta daskare kwan mahaifarta - don tabbatar da cewa saduwa da wani ba abu ne da za ta yi gaggawa ba don kawai ta samu ta haifi yara.

Ta hau jirgin sama zuwa Bangkok babban birnin kasar, inda aka yi mata tiyata. Akwai tsada - Gwendolyn ta ce ta kashe dalar Singapore dubu goma sha biyar kwatankwacin dala dubu goma da dari tara da talatin da biyu a wajen tiyatar.

Amma ita da sauran mata a Singapore da ke son zuwa a daskarar musu kwan mahaifar- tafiya kasashen waje ne kawai zabin da suke da shi.

An haramta daskare kwai a kasar Singapore ko da yake an yi sassauci ga wasu kalilan.

A shekarar 2020, ma'aikatar kula da jin dadin jama'a da inganta rayuwar iyali ta kasar (MSF), ta bayyana cewa ta yi la'akari da " damuwa game da da'a da kuma al'umma kan halatta daskare kwan mahaifar", da dai sauran dalilan.

Amma kuma, a watan da ya gabata a wani sabon mataki, gwamnati ta sanar da cewa daga shekarar 2023, za a amince wa matan da ba su da miji daga shekara 21 zuwa 35 su daskare kwan mahaifarsu.

Amma da wannan sanarwa - za su iya amfani da kwan mahaifar kawai ne idan suka yi aure.

Wannan ba tare da bata lokaci ya cire matan da ba su da miji da kuma watakila ke son su raini ya raba tare da aure ba, kana abokan zama masu jinsi iri daya da ba za su iya yin aure ba a karkashin dokar kasar Singapore.

Adana haihuwa

Daskare kwan mahaifa ya na kara shahara a kasashen duniya.

Ya kunshi dauko kwayayen macen daga cikin jakunkunan kwan mahaifar, tare da adana su a cikin na'urar daskarewa inda za a daskarar da su zuwa wani lokaci mai zuwa.

A daidai wannan lokaci ne ake hada su tare da ruwan maniyyi - da fatan ko hakan zai haifar da yanayi na dan tayi kana a samu juna biyu.

A shekarar 2009, mata 475 ne suka daskarar da kwan mahaifarsu a Amurka, kamar yadda kwanan watan kungiyar Society for Assisted Reproductive Technology ya nuna. A shekarar 2018, mata 13,275 ne suka yi hakan - karuwar fiye da kashi 2500 bisa dari.

Singapore ta shaida irin wannan.

Wani asibiti a Kuala Lumpur babban birnin kasar Malaysia ya shaida wa kamfaanin dillancin labarai na AFP a shekarar 2021 cewa, tsun shaida ''karuwar adadi'' na matan Singapore na zuwa a yi musu aikin.

Kana a yayin da karin wasu mata a kasar Singapore suka koma daskarar da kwan mahaifarsu - sun kuma fara fitowa suna suka game da haramcin.

Emma, wacce a shekarar 2021 ta fara gangamin "My Eggs My Time" wato ''Kwai na Lokaci na'' - gagamin yin kira ga a halatta daskare kwai a Singapore na daga cikin.

"An samu gagarumar nasara. Na samu tarin sakonni daga mata suna bayyana labaransu kan dalilan da suka sama suke son su daskare kwan haihuwarsu,'' in ji Emma, wacce ake kwai kiranta da sunsat na farko.

Har ila yau batun abu ne da 'yar majalisar dokoki Cheng Li Hui ya yi da kawo wa a zauren majalisar.

"A shekarar 2016, lokacin da n afara bullo da batun, mutane sun rika fadin 'Menene wannan? Kin nuna mana fin wayewa," in ji ta.

"Amma da tafiya ta yi tafiya, an samu karin wasu masu tattaunawa. A shekarar da ta gabata (bayan da na kawo batun), na lura da gagarumin banbanci (a martanin). Naa kara samun sakonnin emai na godiya.''

Da dama sun kuma yi lale marhabun da cewa daskare kwan mahaifa zai iya taimaka wa wajen bunkasa adadin haihuwa na kasar ta Singapore, wacce daya daga cikin kasashe mafiya karancin haihuwa ne a duniya.

"Wannan mataki ne da ya zo a daidai lokacin da ake bukata," in ji Shailey Hingorani, jagorar bincike da wayar da kan jama'a ta kungiyar A-ware.

Matakin iyali na gargajiya

Singapore - daya daga cikin kasashe ne mafi cigaban zamani a duniya - amma kuma tana da tsananin ra'ayin mazan jiya - musamman a fannin abin da ya shafi iyali, wanda ta ke dangantawa da ''tubalin ginin al'umma''.

Kasar ta yi kokarin bai wa zamantakewar iyali wata dungulallen suna... da a gargajiyance aka bai wa ma'anar uba, da uwa da kuma 'yayansy'', in ji Mis Hingorani.

Manufofin gwamnati sun karkata ne kan karfafa bunkasar iyalai. Ga misali iyayen da ba su da aure ko wadanda ba su yi aure ba, a kan basu tallafin kalilan na gidaje ne.

Manufofin kasar Singapore na samar da gidaje ba sa saka iyaye matan da ba su yi aure ba ko 'yayansu,'' don haka an cire su daga samun cancantar duk wani tallafu,'' in ji Mis Hingorani.

Mutanen da ba su da aure - da suka hada da abikan zama masu jinsi iri daya da ba za su iya aure a bisa doka ba - dole su jira har sai sun kai shekara 35 su sayi gidan gwamnati, kana har su samu wasu zabin da suke da shi.

Lokacin da aka tambaye ta ko akwai wasu tsare-tsare game da wannan mataki, mai magana da yawun ma'aikatar kula da jin dadin jama'a ta kasar Singapore ta ce manufofin gwamnatin kasar kan al'umma na ''karfafa guiwar haihuwa yayin da aka yi aure''.

Mis Hingorani ta kara da cewa wannan ''abin takaici ne, amma kuma baa bin mamaki ba ne'', kana ta yi kira da kasar ta Singapore da ta "mayar da batun daskare kwan mahaifa ya zamana ya halatta ga kowa, ba tare da tunanin yana da aure ko babu ba, da kuma yanayin aljihunsu ko matakin iliminsu''.

Daya batun da aka gabatar tare da sabuwar manufar shi ne Singapore za ta kwai amince wa mata masu kasa da shekaru 35 su daskare kwan mahaufar na su.

A bisa la'akari da tsarin hukumar sa ido kan haihuwa ta Birtaniya HFEA, wacce ta ce raguwar haihuwa na tafiya tare da shekaru, don haka lokacin da ya dace na daskare kwan mahaifar shi ne idan mace da kai shekaru 35.

Amma kuma bayanan da aka tattara sun nuna cewa akasarin shekarun da ake yi wa mata aikin daskare a Birtaniya shekaru 38 ne, a yayin da da dama ake yi musu da shekaru 40.

Mis Cheng ta bayyana cewa mata a Singapore za su iya fuskantar irin wannan yanayi.

"Mu kasashe ne da suka cigaba, muna da mata masu ilimi da ke aiki kuma suna da zabi. Ina ga shekaru 35 da aka kayyade ya yi kusa sosai. Idan mai shekaru 37 na da kwan mahaifa mai kyau a ajiye, shin hakan na nufin ya kamata mu dakatar da su daga daskare kwan?" ta ce.

Amma kuma MSF ta bayyana cewa adadin shekaru '' ya danganta ga shaidun kimiyya na kasa da kasa da kuma amincewar kwararru cewa ingancin kwan mahaifar zai iya raguwa sosai bayan shekaru 35'', duk da cewa mata za su iya neman karin shekarun a bisa dalilai na daban.

Amma mata kamar irin su Gwendolyn na ganin cewa a yayin da matakin gwamnati ke da na shi iyakar, ta yi amanna zai ''karfafa guiwar'' karin wasu matan Singapore su je a daskare kwan mahaifarsu.

"Ya kamata mu bari mara suna da kungiya - We should allow women to have agency - kwai na ne. Don haka idan na kai shekaru 40 kana ina son in zama uwa ba tare da miji ba, zabi na ne. Amma daga karshe, ganin cewa muna bari ana yin hakan wannan ani babban mataki ne na sauyi.

Za mu iya kara yin wani abu? Ko shakka babu. Amma ina ganin a halin da ake ciki, ya kamata mu yi murna da wannan sauyi.''