Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda ake tsangwamar maza da ba sa haihuwa a Najeriya
Wani mutum da ke fama da lalurar rashin haihuwa ya bayyana irin tsangwamar da yake fuskanta sakamakon wannan matsala.
Mutumin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya fada wa BBC fadi tashin da yake yi domin samun haihuwa.
Ya ce matarsa tana da koshin lafiya, shi kadai ne yake da matsala.
"Na yi aure shekaru 7 da suka wuce, sai wata rana ta ankarar da ni ta ce ba za ta yadda na sake taba ta ba, sai na yi wani abu sakamakon ba bu wani abin da ke fitowa bayan kowane lokaci da muka yi tarayya."
Ya ce ya je wurin likitan kula da haihuwa da al'aura ya zayanna masa jerin gwaje-gwajen da zai yi kuma bayan da aka yi masa gwajin an fada masa cewa matakin sukari a jininsa ya haura 700.
"Bayan gwaje-gwajen ya ce dan samari ka yi hakuri ba ka da karfin bai wa matarka ciki, ina fama da matsalat futar maniyi," in ji shi.
Mutumin ya ce wannan ya sa ya shiga cikin damuwa.
Ya kara da cewa: "Ban fada wa matata ba, na fada wa mahaifiyata wadda ta ce za ta yi magana da wasu mutane don neman taimako, gayawa mutane sai ya koma abin kyamata yayin da wasu mata a kan titi ke yi min ba'a.
''A karshe na fada wa matata matsalar da nake fuskanta wajen haihuwa kuma ta saurari wannan magana cikin natsuwa inda ta yi alkawarin cewa za ta zaunaa wurina."
Ya kuma ce sun jwe wata cibiyar taimaka wa masu neman haihuwa amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba.
Wannan ya janyo rashin jituwa tsakaninsa da mai dakinsa.
Ya ce babban burinsa a rayuwa shi ne ya samu koshin lafiya.
A Afirka ana yawan dora wa mata laifin rashin samun haihuwa, ko da kuwa matsalar daga maza take.