Karyar Kyau: An bankado likitocin bogi da ke yi mata kwaskwarima a Masar

A kasar Masar kwararrun likitocin fata da na fida ne kadai aka amince su yi wa mutum tiyatar kara mazaunai ko kwaskwarima ta kyawun fuska. Hatta cire gashin jiki kwararrun likitoci ne kadai ke yin hakan, ko kuma karkashin kulawarsu.
Sai dai BBC ta gano gwamman mutane da ba su da kwarewa, suna aiki a masana'antun kwalliya na bogi, wanda hakan ya saba wa dokokin Masar.
A rassa biyu na fitaccen wurin La Perla, BBC ta gano dalibai masu neman sanin makamar aiki a fannin lafiya na aikin tiyatar cire gashi ba tare da kulawar babban likita ba.
Mata da dama sun shaida wa BBC sun samu konewa da tabon da ya ɓata musu jiki tun bayan da aka yi musu tiyatar kwaskwarima a asibitin La Perla.
A asibitin horas da masu son zama kwararru ta fannin kwalliya, an bai wa 'yan jaridar da suka yi bad-da-kama shaidar yi wa mata allurar kara girman mazaunai.
Mutumin ya bai wa 'yan jaridar kwarin gwiwar aiki da shi, a kuma bayyane take babu kwarewa sam tattare da horon da aka ba su, ana koya musu yadda za su yaudari abokan hulda yadda za su dauka su kwararrun likitoci ne.
Dokar Masar ta haramta wa wani fakewa da shi kwararren likita ne.
Hukumar da ke sa ido da bayar da shaidar kwarewar likita ko jami'in lafiya, ta shaida wa BBC cewa suna bakin kokarinsu amma matsalar na kara karami ta yadda dole su dauki tsauraran matakai domin magance hakan.
"Na fada wa mutane su kawo rahoton duk wanda suka gani yana wannan aiki ba bisa ka'ida ba, ko likita, ko irin wuraren nan, su sanar da hukuma domin daukar mataki," in ji Dr Gamal Omera na kungiyar Doctor's Syndicate.
"Za mu yi kwakkwaran bincike kan irin wadannan likitocin," in ji shi. Sai dai ma'aikatar lafiya a Masar ba ta ce uffan kan bukatar BBC ta jin martaninta ba.
Su ma hukumomin asibitin La Perle ba su ce komi ba.

Bayar da horo domin zama "likitan bogi"
Akwai daruruwan darussa a intanet da ke ikirarin suna bai wa mutane horo kan yadda za su tafiyar da wuraren kwaskwarima domin karin kyau.
Wadannan wurare na jabu ne. Wurare da dama sun ki amincewa su yi magana da BBC, sun kuma hana su shiga wurin a cewarsu ba kwararrun likitoci ne ba, kuma ba a amince su yi wannan aiki ba.
Amma bayan gayyatar kwanaki uku da za a yi wa fuska da mazaunai kwaskwarima, da cire gashi, da wata cibiyar hadin gwiwa ta Birtaniya da Indiya, 'yan jaridar BBC da suka bad-da-kama sun samu shaidar da za ta nuna tamkar su kwararru ne da suke yin irin wannan aiki ga masu bukata.
Saboda 'yan jaridar ba su da sani sam a fannin lafiya, wannan shaidar ta tashi a tutar babu. Kuma haka mutanen da ke cibiyar suka shaida musu kuma sai sun biya dala 2000 kafin su samu horon.
'Yan jaridar ba su yi wa kowa allura ko ma taba marasa lafiyar ba, hatta injinan aikin ba su taba su ba a lokacin horon.
Dokokin kasar Masar sun haramtawa wanda ba likita ko jami'in lafiya ya yi wa wani ko wata allurar karin kyau ko kara mazaunai. An amince wadanda ba likitoci ba su yi aikin cire gashi, amma karkashin sa idon kwararren likita a wannan fannin.

Kwararru na kallon hotunan yadda ake bada horo, sun shaida mana sun kadu matuka kan abin da suke ganin babban hadari ne ga fannin lafiya, da karya dokar bai wa mutane horon bogi, da kwararren likitan fida Dr Mohamed Madany ke koya wa dalibai, misali kin koya musu da bayani kan hadarin da ke cikin yi wa mazaunai allurar da za su kara girma, ko abin da ya kamata mutum ya yi da zarar an samu matsala bayan yi masa aiki.
Akwai wurare da Dr Madany da manajan cibiyar bada horo Ashraf Gad, suna koyawa daliban yadda za su yaudari marasa lafiya ko abokan hulda cewa su likitoci ne ta hanyar sanya farar rigar likitoci wato Lab Coat, da gabatar da lokacinsu a matsayin kwararru a fannin kyawu.
"Matan da aka gayyata domin yin gwaji kan horon, sun shaidawa 'yan jarida likitocin na fada musu su shaidawa kwastomomi su kwararru ne, yayin da Dr Ashraf ya jaddadawa 'yan jaridar su tabbatar sun yaudari mutane kan su likitoci ne.
A kasar Masar Ashraf Gad ya bai wa tarin mata shaidar kwarewa a fannin, alhalin ba su da masaniya kan duk abin da ya shafi fannin lafiya.
Ya bayyana cewa matan da ya bai wa horon na amfani da shaidar wajen yin ayyukan da suka shafi kwalliya da sauransu, har ma sun mallaki ko dai asibitoci na kashin kan su, ko kuma manyan wurare da suke jagorantar aikin.

Hayar sunan likita
Samun shaidar amincewa da bude ko tafiyar da asibitin a Masar, dole ne sai manajan ya kasance kwararren likita mai shaidar gudanar da aiki.
Babban laifi ne likita ya bai wa wani asibiti shaidar kwarewa ba tare da bincike da sanya ido ba.
Amma Dr Madany ya bai wa 'yan jaridar BBC da ba su kware a fannin ba wannan shaida, kowanne mutum guda akan Fan din Masar 6000, wato dala 3,980, kwatankwacin naira Dubu 218,500 a kowanne wata.
Ya amince da hakan ne saboda aikinsa kawai ya tsaya ganin yadda ake yin kwaskwarimar karawa mata kyau da za a dinga yi sau biyu zuwa uku a kowanne mako.
Dan jaridar da ya tsaya a matsayin dalibi na shirin yi wa abokin hulda allura ba tare da shi Dr yana wurin ba. Dr Madany ya kara da shaidawa daliban ''bayan dan takaitaccen lokaci za su iya yin allurar mazaunai kamar yadda likitoci ke yi" da ba su shawarar za su iya aiki su kadai da tafiyar da asibitin bayan watanni shida a karkashin kulawar wani.
Dr Madany ya hadawa 'yan jaridar da wani lauya da zai taimaka musu kafa asibiti.
Lauyan mai suna Mohamed Abou El Azm, ya shahara wajen sukar gwamnati kan danbarwar rashawa a fannin lafiya.
Ya yi wa 'yan jaridar BBC tayin zai dinga sanar da su da zarar tawagar gwamnati da ke duba cibiyoyin lafiya da asibitoci masu zaman kansu za su zo, yana samun bayanai sakamakon dadewar da ya yi yana hulda da su.
Wannan aiki da zai yi musu za su biya dala 254, domin tafiyar da haramtaccen aikin.
A shekarun da suka gabata, an ga yadda hukumar da ke kula da asibitoci masu zaman kansu ta Masar, wadda wani bangare ne na ma'aikatar lafiyar ya rufe asibitoci da dama, saboda danbarwar lasisin bogi, da wadanda ba su da laisisn ko da na bogi ne, sun kuma dauki matakan da ba su da kwarewa a fannin lafiya.
Ma'aikatar lafiya ta Masar ba ta ce komi ba kan tayin BBC na jin martaninta ba.
Shi ma Dr Madany da Ashraf Gad na cibiyar hadin gwiwa tsakanin Birtaniya da Masar, ba su mayar da martani ba kan bukatar BBC na wannan bincike ba.











