Yakin Ukraine: Yadda miliyoyin mutane suka kalli bidiyon karya a TikTok

Tambarin TikTok da aka bude a watar salula, dauke da turai Ukraine a baya.

Asalin hoton, SOPA Images

An wallafa

TikTok na daya daga cikin shafuka masu saukin yada bidiyon karya game da yakin Ukriane, da miliyoyin mutane suka kalla.

Shafin na da mabiya biliyan daya, sannan rabin masu mu'amala da shi matasa ne 'yan kasa da shekara 30, dandali ne da matasa ke samun karin bayani kan halin da ake ciki a yakin, a daidai lokacin da ake kokarin magance yawaitar bidiyon bogi da ake yadawa ta TikTok.

Kuma ba ka bukatar daukar lokaci wajen samun irin wadannan abubuwa.

Kamar yadda binciken shafin internet na NewsGuard da ke bibiyar abin da ke faruwa, shafin ya ce sabbin masu amfani da shafin na cin karo da bayanan karya da ake yadawa cikin kasa da minti 40 da fara amfani da shafin.

Yayin da shafukan kamar Facebook, Instagram da Twitter, su ma aka maganar suna yada bidiyon karya game da yaki, sai dai TikTok yana sahun gaba.

Sai dai kamfanin ya dage cewa, yana daukar matakai da suka kamata domin yaki da labaran karya.

Ga wasu daga cikin bidiyon da BBC ta gano ba su da inganci, da aka yada a shafin TikTok.

Bidiyon da ake yadawa kai tsaye na bogi

Tun daga farkon fara yakin, ake ta samun bidiyon da ake haskawa kai tsaye daga fagen daga, wanda kuma suka ja hankalin masu bibiyar TikTok.

Gane hakan ba abu ne mai wuya ba: wanda ya yada bidiyon ya yi amfani da tsohon bidiyon yaki ko na atisayen soji, da aka yi amfani da tashin bam na karya da karar harbe-harbe sannan suka fara yadawa kai tsaye, a wani bangaren suna rokon a ba su tallafi, ta shafin nasu.

Daya daga cikin irin wadannan shafukan ya ja hankalin kusan mutum miliyan 30 a tsakiyar watan Maris. Cikin shafuka uku da suka yi amfani da irin wadannan bidiyon na kai tsaye, sun samo su ne a shafin Youtube, kuma tsoho na shekar 2017 lokacin da sojojin Ukraine ke wani atisaye.

BBC

An kai gabar da wani bidiyon bogi na harbe-harben bindiga ya samu ficen, da aka yada shi sama da sau 13,000.

Masu amfani da shafin na turawa da asusun ajiya na banki da suke kubatar a sanya musu tallafi a ciki, da za su cire tsabar kudin.

"Abin da matukar tsoratarwa, da tashin hankali, kuma duk ana yi ne da nufin tara haramtattun kudade ta amfani da TikTok," in ji Abbie Richards, wata mai bincike da ta yi amfani da irin wadannan bidiyon domin tantance ingancinsu.

Yawancin bidiyon kai tsaye na bogin, ana yin su ne karkashin fitaccen maudu'in nan na #Ukraine ko #UkraineWar.

"Manufar abin da ke ciki, da bayanai shi ne a samu batun tattaunawa, da samun bayanai," in ji Ms Richards.

Bidiyon wasanni

Akwai bidiyon wasanni na Game da aka yi amfani da su ta kwamfuta, da hotuna na sojoji da yake-yake da ake amfani da su a hada bidiyo kan yakin na Ukraine.

Ana yada bidiyon yakin a fagen daga, ciki har da hotunan da ke nuna jiragen yaki da aka harbo kasa, wanda ya yi matukar farin jini a shafukan sada zumunta.

Wasu daga cikin masu amfani da TikTok da suka kara yi masa kwaskwarima, da amfani da wasu daga cikin takaitattun bidiyon ainahin yakin, da wadanda ake yadawa ta shirin Talbijin, da sauransu.

Wannan bidiyon ya nuna wani game din wasa da ba shi da alaka da yakin Ukraine

Asalin hoton, Tiktok

Bayanan hoto, Wannan bidiyon ya nuna wani game din wasa da ba shi da alaka da yakin Ukraine

Wani bidiyo, da aka kalla sama da sau miliyan 25, ya nuna wani mutum da ya jefar da abin fashewa kan wata tankar yaki.

An dauke shi ne daga bidiyon wani wasan yara da aka yi abin makamancin irin hakan sai aka hada tare da wallafawa a shafin YouTube a watan Junairu.

Wani bidiyon kai tsaye na bogi, da aka kalla sau miliyan 2.3, an yi shi ne daga bidiyon wasa, an kuma yi amfani da hotuna, da hotunan makamai masu linzami da aka kai hari ta sama, shi ma ya yi ta wadari a shafukan sada zumunta amma tun shekarar da ta wuce, yayin da yakin Ukraine aka fara shi cikin shgekarar nan.

An yi amfani da manhajar CGI awajen hada shi, kuma ya shafe watanni ya na wadari a shafukan itanet

Asalin hoton, Tiktok

Bayanan hoto, An yi amfani da manhajar CGI awajen hada shi, kuma ya shafe watanni ya na wadari a shafukan itanet

Ms Richards ta ce ta ga yawanci masu kallon bidiyon na gargadin sauran da cewa ba na gaskiya ba ne an dauko su ne daga cikin wasannin da ake gani na wasanni da wadanda hadawa aka yi. Amma duk da haka wadanda suka hada shi na toshe masu suka ko wayar da kan masu kallo, wasu lokutan ma sai a nemi irin wadannan bayanai a rasa.

Tsofaffin Bidiyo

An yi ta amfani da tsofaffin bidiyon tsohon rikicin da aka yi a daidai lokacin da ake hada sabo. BBC ta ga hotuna da bidiyon yaki kamar na Libya da Syria da Chechnya, da aka yi amfani da su a yakin na Ukraine.

Wani bidiyo da ya nuna yakin tsakanin Rasha da Ukraine, ya nuna yadda ake gwabza fada tsakanin dakarun kasashen biyu a wajen gine-ginen farar hula, da kuma aka kalla sau miliyan 7.7.

Sai dai ainahin bidiyon, an dauke shi ne a shekarar 2014 a babban birnin Chechnya, Grozny, lokacin da aka kai wani mummunann hari da mayakan jihadi suka kai da ya yi asarar rayuka da dama.

An yi amfani da Labari da Duminsa na bogi da kuma nuno kai tsaye cewa an kashe gwamman mutane.

Wannan tsohon bidiyo ne, na mummunan harin da mayakan jihadi suka kai a Chechnya shekarar 2014, an yi masa rubutun bogi da sunan labari da duminsa kan halin da ake ciki a Ukraine

Asalin hoton, Tiktok

Bayanan hoto, Wannan tsohon bidiyo ne, na mummunan harin da mayakan jihadi suka kai a Chechnya shekarar 2014, an yi masa rubutun bogi da sunan labari da duminsa kan halin da ake ciki a Ukraine

Wasu ma sun wallafa bidiyon yakin da aka yi tsakanin Ukraine da Rasha a shekarar 2014, wanda babu tamtama za a iya yin kuskuren dauka cewa yakin da ake yi na wannan lokaci ne, ko hotunann atisayen soji ko faretin shekara na bangarorin biyu.

Bidiyon tankokin yakin Ukraine a tsakiyar birnin Kyiv, na nan daram tamkar dama tuntuni an yi ne domin kare babban birnin daga munanan hare-haren da Rasha ke kai wa ta sama.

Wannan bidiyon an kalle shi sama da sau miliyan tara, sai dai an dauki bidiyon ne a bikin tunawa da karbar 'yancin Ukraine da kuma sojoji suka yi fareti a bara.

Wani bidiyon tankar yaki dauke da tutar Ukraine, da ke nun yadda ake sauke gidajen farar hula, ya samu farin jini ba kadan ba, inda aka kalle shi sau miliyan hudu, shi ma tsoho ne kan rikicin da Rasha da Ukraine suka yi a shekarar 2014.

Ms Richards ta ce kamata ya yi TikTok, ya dauki matakin magance matsalar yada bidiyo da hotunan bogi, musamman tsofafi, ta hanyar amfani da ainahin kwanan wata da lokaci da wurin da abun ya faru.

Takaitattun shaidu

Kamar dai shafukan Facebook da Instagram da babarsu Meta, TikTok na aikin hadin gwiwa da masu kutsen intanet mai zaman kan su. Amma Facebook da Instagram suna nuna bayanai da bidiyo na karya da ake yadawa kan yakin Ukraine da wuya ka ga irin hakan a TikTok.

Shi ma wannan bidiyon an dauke shi ne a shekarar 2014, a gabashin Ukraine

Asalin hoton, Tiktok

Bayanan hoto, Shi ma wannan bidiyon an dauke shi ne a shekarar 2014, a gabashin Ukraine

Wata karin matsalar kamar yadda Ms Richards ta bayyana, ita ce rashin babu takamaimai wani wakili ga masu amfani da TikTok da za su fito domin karyata wani labarin bogi da aka wallafa a shafin.

"Idan TikTok ya gagara ba ta cikakken bayani kan labarai da bidiyon karya da ake yadawa miliyoyin mutane, wannnan yana ci wa masu bincike tuwo a kwarya."

Sai dai kakakin TikTok ya shaidawa BBC: "Muna ci gaba da aiki tukuru, domin nuna alhini kan abin da ke faruwa a Ukraine, muna kuma kokarin kara matakan tsaro domin ganowa da cire duk wani abu na bogi da aka wallafa da ake yadawa kan yakin.

"Mun kara wasu abubuwa da zamu zamanantar da abubuwa, da samar da bayanai masu inganci da dorewa a TikTok, mun kara abubuwan da ke tabbatar da sahihan bayanai da aka yada da wallafawa a shafin."