Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Mun yi farin-ciki da sake bude iyakokin kan tudu na Najeriya'
Mazauna garuruwan da ke kan iyakokin Najeriya da aka rufe na ci gaba da bayyana farin-cikinsu bayan da hukumomin ƙasar a hukumance suka buɗe iyakokin da ke kan tudu a ranar Litinin.
Hukumar hana fasa-ƙwauri ta ce gwamnatin tarayya ce ta ba da umarnin buɗe iyakokin huɗu a ƙarshen makon jiya.
An dai amince a bude iyakokin Idoroko a jihar Ogun da Jibiya dake jihar Katsina sai kuma iyakar Kamba a Kebbi da kuma iyakar Ikom a jihar Cross River.
Bayan bude iyakar Jibiya a Katsina, mutanen da ke yankin sun bayyana jin dadinsu kasancewar harkokin kasuwanci zai farfado a cewarsu.
Alhaji Salisu O I Jibiya, ya shaida wa BBC cewa, bude iyakokin nan ya sanya su cikin jin dadi da raha saboda sun shafe shekaru uku suna rufe abin da ya sanya su cikin takura.
Ya ce, duk da ka'idojin da hukumomi suka gindaya musu na irin abubuwan da za a rinka safararsu ta iyakokin, su kam sai san barka saboda koba komai za su ci gaba da kasuwancinsu da suka jima basa yi.
Alhaji Salisu O I Jibiya, ya ce " A yanzu an yarda mu shigo da abubuwa da suka hada da wake da aya da kuma dabino, amma duk sai mun biya kudin fito."
To amma ba suce mu biya kudin fito a kan kayan abinci kamar shinkafa da taliya da cous cous da dai makamantansu ba, in ji shi.
Ya ce, duk wadannan sharadai su kam ba su damu ba domin ba bu wani alfanu da rufe iyakokin ya kawo musu sai bakar wahala da suka sha.
A jihar Kebbi ma, an bude iyakar Kamba, inda al'ummar garin suka shaida wa BBC cewa suna cikin farin ciki marar misaltuwa saboda abin da suka jima suna jira ne ya faru.
Yahuza Sahabi, mazaunin garin Kamba ne inda aka bude iyakar, ya kuma shaida wa BBC cewa, bude iyakar nan shi ne babban alfanu garesu, domin za su samu saukin farashin kayayyaki musamman na abinci.
Ya ce," A gaskiya mu mutanen da ke rayuwa a garuruwan da ke kan iyaka, rufe su ya yi matukar taba mana rayuwa musamman ta fuskar tattalin arziki."
Yahuza Sahabi, ya ce a lokacin da aka rufe iyakarsu sun ga kalubale kala-kala, saboda yadda farashin kayan abinci ya tashi sosai, ba karamin kuncin rayuwa muka shiga ba inji shi.
Ya ce, amma a yanzu tunda an bude iyakar, farashin kayan abinci da ma sauran kayan bukatun yau da kullum zai sauko.
Karin bayani
Hukumomin Najeriya dai sun sha fada cewa, rufe iyakokin ya taimaka wajen bunkasa harkokin masana'antun cikin gida da noma musamman na shinkafa.
A karshen shekarar 2020 ne, shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya bayar da umarnin bude iyakokin kasar hudu na kan tudu da suka hada da Semi da Ilela da Maigatari da ku ma Ofong.
A watan Agustan 2019 ne gwamnatin kasar ta rufe iyakokin nata da zummar daƙile yawaitar fasa-kwauri da kuma bunƙasa tattalin arziki, ko da yake 'yan kasar da dama sun koka kan matakin.
Hukumar hana fasa-ƙwauri, wadda ta yi ruwa ta yi tsaki wajen ganin an yi aiki da rufe iyakokin, ta bugi ƙirji game da irin nasarorin da ƙasar ta samu saboda matakin da ta dauka na rufe iyakokin tudu ta fuskoki daban-daban na rayuwa.