Hotunan Afirka na mako daga 15 zuwa 21 na Afrilun 2022

An wallafa

Wasu zaɓaɓɓu kuma ƙayatattun hotuna daga nahiyar Afirka da wajenta a wannan makon:

Short presentational grey line
People watch as paragliders glide with passengers during the annual Easter paragliding festival in Kwahu-Atibie, Ghana.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Bikin tsallen-lema da aka yi a Kwahu-Atibie, Ghana, ya ja hankalin 'yan kallo ranar Juma'a...
People watch as Ghanaian paragliders Michael Kwakye and Stephen Asamoah land at the Nkawkaw football field.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Cikin wadanda suka shiga bikin akwai Michael Kwakye da Stephen Asamoah, wadanda a nan suke murmushi bayan sun sauka lafiya
An Egyptian troupe performs the traditional Tanoura (skirt) dance during the Muslim holy month of Ramadan, at el-Ghuri Culture Palace in Cairo.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Laraba a Alkahira, babban birnin Masar kungiyar raye-rayen kasar ta yi wasan kwaikwayon Tanoura, wanda ya kunshi salon rawar Sufaye.
Members of the Area 10 Scout brass band play along Lumley beach in Freetown. Brass bands have a long history in Sierra Leone and are slowly making a come back after the war. Most neighbourhoods, scout groups and schools have a brass marching band and competitions are held regularly. Bands spend hours training, promoting and recruiting more players by playing on public holidays and at events.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Litinin a Freetown babban birnin Saliyo, ƙungiyar raye-raye ta Area 10 Scout ke wasa a bakin tekun Lumley.
A man poses in a suit with panels of various colours, on Friday 15 April 2022.

Asalin hoton, Moses Sawasawa

Bayanan hoto, Shekara daya bayan da tsaunin Nyiragongo ya yi aman-wuta a gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango, wani mai tallan kayan kawa Kulliko ya yi taron nuna kayan kawa don tara kudade ga wadanda suka tsira daga bala'in da ke zaune a wannan sansani da ke Goma.
A ranar bikin Easter, wasu mambobin Cocin Maroon na Saliyo sun halarci ɗakin bauta mai shekaru 230.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar bikin Easter, wasu mambobin Cocin Maroon na Saliyo sun halarci ɗakin bauta mai shekaru 230.
Coptic Christians celebrate Palm Sunday inside the St Simon's Church on the Mokattam hills.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Haka kuma a ranar a kasar Masar, Kiristoci Kifdawa ke bikin Palm Sunday a Cocin St Simon's ...
Coptic Orthodox Christians take part in a mass marking Palm Sunday at the St Simon's Church.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wannan hoton cocin ke nan wadda kuma aka sani da Cocin Cave, an sassaƙa shi ne a cikin wani tsauni a gundumar Mokattam a birnin na Alkahira.
Haka kuma a birnin na Alkahira, Musulmai sun yi buda-baki tare da dimbin jama'a a kan wani teburi mai tsawon mita 750.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Haka kuma a birnin na Alkahira, Musulmai sun yi buda-baki tare da dimbin jama'a a kan wani teburi mai tsawon mita 750.
Worshipers hold candles during Easter vigil prayers at the St. Joanes, Legio Maria of African Church Mission within Fort Jesus in Kibera district of Nairobi.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wannan hoton wasu masu bauta ne da suka halarci wani babban taro na coci a ranar Lahadin da ta gabata a Nairobi babban birnin kasar Kenya.
A man performs as Jesus Christ during a procession marking the Good Friday in Abidjan, Ivory Coast.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, An ga wani mutum ya kwaikwayi yadda aka gicciye Yesu a sama a Abidjan babban birnin Ivory Coast, a ranar Good Friday....
Actors takes part in a Via Crucis procession during Holy Week in Koumassi, Abidjan.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An yi kuma amfani da jinin karya don kwaikwayon abin ƙyama da ya faru da Yesu.
The Concert, an installation by Moroccan-French artist Latifa Echakhch in the Swiss Pavilion at the 59th International Art Exhibition in Venice, Italy.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wannan hoton wasu masu sha'awar zane-zane ne aka dauka a bikin fasaha na yar kasar Maroko da ke zaune a Faransa Latifa Echakhch a Venice Biennale ranar Talata.
Volunteers and members of the public clean up on North Beach following heavy rains earlier in the week in Durban.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A nan kuma a ranar Juma'a masu aikin sa-kai ke share tarkace a bakin rairayin teku a Durban na Afirka ta Kudu, inda hukumomi suka ayyana wani yanayi na bala'i bayan mummunar ambaliyar ruwa da masana suka tabbatar da cewa sauyin yanayi ya kara tsananta ta.

Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka