Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mwai Kibaki: Tsohon shugaban Kenya ya mutu yana da shekara 90
Tsohon shugaban kasar Kenya, Mwai Kibaki, ya mutu yana da shekara 90, a cewar sanarwar da Shugaba Uhuru Kenyatta ya fitar.
Zaben da aka yi masa a matsayin shugaban kasa a 2002 ya kawo karshen shekaru 40 da kasar ta kwashe tana mulki na jam'iyya daya wanda aka soma tun bayan samun 'yancin kan Kenya.
Sai dai zaben da aka sake yi masa a 2007 ya yi sanadin boren da aka kwashe wata da watanni ana yi a kasar, wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 1,200.
Ya mutu ya bar 'ya'ya hudu.
Shugaba Kenyatta ya jagoranci ta'aziyyar mutuwar tsohon shugaban kasar, yana mai cewa Mr Kibaki "ya jagoranci fafutikar sanya ido a kan jam'iyya mai mulki domin ganin ta yi abin da ya kamata" kuma 'yan kasar "sun mutunta shi" a kan hakan.
Shugaban kasar ya ayyana makoki har sai lokacin da aka binne Mr Kibaki, sannan za a dawo da tutocin kasar kasa-kasa.
Za a yi wa tsohon shugaban kasar jana'izar ban-girma da karramawa irin ta soji, in ji Shugaba Kenyatta.
'Yan kasar Kenya da dama suna nuna alhininsu bisa rasuwar Mr Kibaki , mutumin da suke gani a matsayin shugaban Kenya mafi martaba tun da kasar ta samun 'yanci.
Masanin tatalin arziki ne da ya sanya kasar a tafarkin ci gaban tattalin ariki. Ya rike mukamai da dama a baitul malin kasar da kuma gwamnati a rayuwarsa ta siyasa da ya kwashe shekaru aru-aru.