Fadi-tashin rayuwa a kasar Afghanistan da ke fama da karancin kudi

    • Marubuci, Daga Secunder Kermani
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Kabul
  • An wallafa

Mai shekaru biyar Fazlur Rahman na da wani katon tsiron kansa a wuyansa kuma likitocin Afghanistan ke ta fafutikar tsawaita rayuwarsa ta hanyar yin gashi.

Yana kwance a sashen masu fama da cutae kansa mai cunkoso a asibitin Jamhuriat na birnin Kabul na kasar.

A asibitin, kana iya ganin tasirin da taimakon ke yi, da kuma dalilan da suka sama ake bukatar kari.

Jinyar kyauta ce, bayan da Kwamitin Kungiyar Bayar da Agaji ta Red Cross na Kasa da Kasa ICRC ya shigo ciki don tallafa wa ayyuka na musamman a asibitoci, amma yanz marasa lafiya dole su rika sayen akalla wasu daga cikin magungunan da kan su.

Tattalin arzikin Afghanistan ya tabarbare daga sauyin da aka samu na karbe mulkin da kungiyar Taliban ta yi, da samun dala 100 ya zama babban kalubale ga mahaifin yaron

Abdul Bari, wani manomi daga kauye mai nisa a yammacin kasar.

"Na yi ta cin bashin kudi daga duk wand ana sani don in samu isassun kudaden da zan biya zuwa wannan wuri, da wurin da zan zauna da kuma sayen magunguna,''ya shaida mana.

A baya dai a Afghanistan, kashi 75 bisa dari na kudaden da mutane ke kashewa na fitowa ne daga tallafin kasashen waje.

An dakatar da wannan tallafi tun bayan da Taliban ta kwace mulki, duk da cewa agajin jin kai ya cigaba, kana an rufe asusun ajiyar kasashen waje na Afghanistan na dala biliyan 9, kwatankwacin fan biliyan 7, da hakan ya haddasa karancin samun kudaden da tsabar kudi a cikin kasar.

Wani rahoto daga Bankin Duniya a makon da ya gabata ya yi gargadin cewa fiye da daya bisa ukun yawan al'ummar kasar yanzu ba sa iya ciyar da kan su.

Marasa lafiya a sashen masu fama da cutar kansa kama Mazaria mai shekaru daga arewacin lardin Takhar na sayar da komai da suka mallaka, don sus amu biyan kudin maganin da a baya ake bayar da su kyauta.

"Ya za mu yi?" Mazaria ta tambaya. "Mu leburori ne, muna…. da saniya da jaki, don haka mun sayar da su. Babu wani abu da ya rage mana.

"Mun karbi rancen kudi daga 'yan uwana maza da 'yan uwan mijina har ma da makwabta."

Dakta Manucher ne ke lura da sashen masu fama da cutar ta kansa. A wasu lokutan, ya kan ce, ma'aikatan asibitin su hada kai su biya kudin magugunan a madadin marasa lafiyar da ba su da galihu.

Ya bayyana cewa: "Abin takaici ba mu da isasshen kudi."

Ko shakka babu, babu ko kwabo a cikin kasafin kudinsa. Sashen har yanzu yana tafiyar da aiki ne saboda ICRC na biyan albashi da kuma wasu magungunan.

A bara ya samu kudin tafiyarwa dala miliyan daya daya ma'aikatar kula da lafiyar al'umma.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da karin dala biliyan 4 don shawo kan matsalar da ta shafi jin kai a Afghanistan.

Wani gagarumin taron manema labarai a watan da ya gabata ya yi kira da a samar da dala biliya 4 da miliyan hudu don shawo kan matsalolin a Afghanistan - dala biliyan biyu da miliyan hudu ne aka yi alkawari.

Akwai tsananin bukatar taimakon ceton rayuka, a yayin da matsalar karancin abinci mai gina jiki ke karuwa kana iyalai da ke fama da wahalhalu suka koka aurar da 'yayansu mata da kananan shekaru ba kamar yadda suka saba yi ba.

Amma ma'aikatan agaji da jami'an diplomasiyya duka sun fahimci muhimmancin duba fiye da wadannan bukatu na gaggawa da taimaka wa kasar ta Afghanistan gina makoma mai dorewa.

Amma kuma, cigaba da bayar da tallafin raya kasa, da bude asusun ajiyar Afghanistan na kasashen waje, batutuwa ne da kasashen waje har yanzu ke cigaba da nuna turjiya a kai, musamman ma da 'yan Taliban ke kar zama masu taurin kai.

Fargaba na nuna cewa fusata kan matakin kungiyar na haramta wa 'yanmata komawa makaranta a akasarin sassan kasar zai haifar da dari-dari daga kungiyoyin bayar da tallafi game da cigaba da bayar da taimakon da ake bukata.

A gabashin gefen birnin Kabul mun ziyarci wani sansanin iyalan da suka rasa matsugunansu.

Fadan da suka tsere wa yanzu ya kawo karshe, amma suna kokawa da cewa yanzu ba za su iya sake gina gidajensu ba.

Kananan yara sun cunkuso a wani aji na al'ummar yankin, Makarantar gwamnatin da ke kusa kyauta ce, amma Parwana mai shekaru 12 ta bayyana cewa ba za ta iya sayen rigar makaranta ba. Shekaru uku kenan rabonta da zuwa makaranta.

Ta ce: "Rayuwa na kara tsanani, mahaifiyata na wanke tufafi amma ba ta samun isassun kudin da za ta saya mana abinci, kuma yanzu ta kamu da rashin lafiya."

A wani wuri can a yayin da yamma ta karato, a wajen shuganan sayar da burodi da dama a Kabul, an saba ganin taron mata da kananan yara na zaune a kan dandamali suna fatan ko masu sayen burodin za su zo su sayi daya ko biyu.

A kan titin arewacin birnin, inda kungiyar bayar da agaji ta yankin ke raba burodi a kullum, mutane kusan dari ne suka hallara.

Akwai matukar nuna damuwa, bayan da wasu suka yi kuskuren tsammani cewa m ma'aikatan bayar da agaji ne, suna ta kokarin daga katunan shaidarsu a kan fuskokinmu, cike da fatan za mu saka sunayensu a cikin wadanda za a bai wa taimakon.

"Idan ba taimakon mu za ku yi ba, me ya kawo ku nan?" in ji daya daga cikinsu.

Dayan ya fashe da kuka a lokacin da muke kokarin tafiya: "Wani lokacin 'yayana kan ci abinci, wani lokacin ba sa ci.''