Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Saurayi Tshegofatso Pule ne ya bayar da umurnin kashe budurwar tasa
- Marubuci, Pumza Fihlani
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Johannesburg
- An wallafa
An kama saurayin wata budurwa da kisanta ya girgiza mazauna Afirka ta Kudu shekara biyu da suka wuce da laifin shirya kisan nata.
Babbar Kotun Johannesburg ta yi hukuncin cewa Ntuthuko Ntokozo Shoba Ntokozo Shoba na da laifi wajen shirya kisan Tshegofatso Pule da kuma biyan makashin lada.
An tsinci gawar matashiyar mai shekara 28 tana reto a jikin bishiya shekara biyu da suka gabata da harbin bindiga a ƙirjinta.
Mutane da dama sun yi Alla-wadai da kisan, ciki har da Shugaban Ƙasa Cyril Ramaphosa.
A baya, shugaban ya taɓa cewa "Afirka ta Kudu na cikin ƙasashen da suka fi haɗari ga mata a duniya".
A ƙasar da aka fi yawan aikata wa mata laifuka a duniya, ciki har da kashe su kawai saboda jinsinsu, mutuwar Ms Pule ta gigita mutane da yawa.
Mutumin da ya amsa laifin kashe ta Muzikayise Malephane, wanda kuma yake zaman gidan yari na shekara 20, ya zama mai ba da shaida kuma ya zargi saurayin nata a matsayin makashinta.
Ya faɗa wa kotu cewa Shoba ya ɗauki hayar wani mutum don ya gayyace ta wurin haɗuwa, kuma shi ne yunƙuri na biyu da ya yi don kashe ta.
Malephane ya ce Shoba na son ya kashe ta don kar matarsa ta gano cewa ya yi mata ciki.
Shoba na tsoron rasa matarsa da kuma wata gudunmawar kuɗi da ta samu kwanan nan. Da farko ɗan kasuwar ya musanta zargind da ake yi masa, yana mai cewa tarko aka ɗana masa.
Da yake bayyana hukuncin, Mai Shari'a Stuart Wilson ya ce dukkan hujjojin da aka tattara sun nuna cewa Shoba ne ya ba da umarnin kisan.
Nan da farkon watan Mayu ake sa ran za a yanke masa hukunci.
A wajen kotu, dangin Ms Pule sun yi waƙe-waƙe, da kuka, da rungume juna, suna masu cewa an yi adalci. Tana shirin haihuwar yaronta na farko kafin a kashe ta.
Kisanta ya haddasa ƙirƙirar maudu'in #JusticeForTshego wato AdalciGaTshego a Twitter.
A martaninsa, Shugaba Cyril Ramaphosa ya fitar da sanarwar da ke Allah-wadai da cin zarafin jinsi, yana mai cewa annobar korona ta ƙara tsananta yanayi ga mata saboda "mugayen maza na amfani da damar da suka samu ta sassauta dokokin kulle wajen zaluntar mata da yara".
Aƙalla kashi 51 cikin 100 na matan Afirka ta Kudu sun fuskanci tashin hankali a hannun wani da suke da alaƙar soyayya da shi, a cewar sanarwar shugaban.