Hotunan Afirka na mako: Daga 1 zuwa 7 ga watan Afrilun 2022

An wallafa

Zababbun hotunan abubuwan da suka faru a fadin nahiyar Afirka:

Short presentational grey line
A young boy makes a funny face at the camera during prayers.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani yaro Musulmi na kallon kyamara a masallacin Juma'a a birnin Yaoundé, kasar Kamaru…
A man arranges watermelons as he waits for customers.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Kwana daya da fara azumin wata mai tsarki na Ramadan, wannan mai sayar da kankana a wata kasuwa a Mogadishu babban birnin kasar Somalia...
A Tunisian confectioner holds up a zlabia in a pastry shop in Tunis, Tunisia.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Irin kek na Zlabia, a ranar Litinin daya daga cikin fitattun kayan zaki ne a tsakanin 'yan kasar Tunisia lokacin buda-baki.
Two South African reality TV stars, Roxy Louw and Kelly Khumalo, take a selfie together.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Taurarin shirye-shiryen talabijin Roxy Louw da Kelly Khumalo sun tsaya daukar hoto a liyafar kaddamar da wasan kwaikwayo mai dogon zango na Afirka ta Kudu Tropika Island of Treasure a ranar Juma'a a birnin Johannesburg.
A man looks at artworks by Pablo Picasso at a dedicated exhibition at Dakar's Musée des Civilisations Noires.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A rana iri daya wasu ayyuka da dama na shahararen mai zanen kasar Spaniya Pablo Picasso - wanda zane-zanensa da yawanci aka aro daga fasahar zane daga Afirka - ake baje-kolinsa a Dakar babban birnin kasar Senegal.
1px transparent line
Women buy bowls and plates at a market.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Har ila yau a ranar Lahadi, mata na duba wasu kwanukan zuba abinci masu kyalli da ake sayarwa a wata kasuwa a garin Rufisque.
Men charge on horseback while firing muskets.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A kasar Morocco a ranar Jumma'a, masu sukuwar dawaki na halartar bukukuwa da ake yi wa lakabi da "tebburide" bayan harba wata nau'in bindigar toka…
A man rides a horse kitted out in ornate and colourful tack.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An bayyana cewa wannan ya samo asali ne a bayan wani bikin samun galaba kan kasar Sifaniya a cikin karni na 15.
South African football fan Mama Joy Chauke holds up a scarf with the words "South Africa" knitted into it.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Babbar mai goyon baya Mama Joy Chauke na halartar gasar wasan kwallon kaf ana cin Kofin Duniya a kasar Qatar ranar Jumma'a. Sananniya ce a kasarta a matsayinta na shugabar Kungiyar Masu Goyon Bayan 'Yan Wasan Afirka ta Kudu.
A woman wearing protective goggles and earmuffs shoots with a CZ Shadow 2 9mm pistol.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Gwamman mata ne suka halarci wurin koyon harbi a Bronkhorstspruit, Afirka ta Kudu a ranar Lahadi.
Children play billiards in the Sayeda Zainab district of Cairo.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ta wani gefen kuma wadannan yaran ke gasar wasan harbi a ranar Laraba a birnin Alkahira na kasar Masar.
People carry a portrait of Thomas Sankara to a memorial site.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Har ila yau a ranar Laraba, mutane a kasar Burkina Faso na gudanar da taron addu'oin tunawa da marigayi tsohon shugaban kasar Thomas Sankara, bayan da aka yanke wa wanda ya gaje shi Blaise Compaoré hukuncin daurin rai-da-rai a yayin da baya nan, kan kisan Sankara a shekarar 1987.
A smiling woman standing in the street holds a Sudanese flag.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kazalika a wannan ranar a Khartoum babban birnin kasar Sudan, mutane na na gudanar da gangami don tunawa da zagayowar shekaru uku da fara zanga-zangar nuna goyon bayan dimokaradiyya.

Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka