Kisan Thomas Sankara: Kotu ta yanke wa tsohon shugaban Burkina Faso Compaore hukuncin ɗaurin rai-da-rai

Asalin hoton, Getty Images
Wata kotun soja a Burkina Faso ta yanke wa tsohon Shugaban Ƙasa Blaise Compaore hukuncin ɗaurin rai-da-rai sakamakon kama shi da hannu a kisan wanda ya gada Thomas Sankara.
An yi wa Compaore shari'a a bayan idonsa yayin da yake gudun hijira yanzu haka.
An yanke wa tsohon shugaban sashen tsaro na gwamnatinsa, Hyacinthe Kafando, hukuncin ɗaurin rai-da-rai shi ma.
Mista Sankara wanda ɗan neman sauyi ne mai aƙidar Markisanci, wasu 'yan bindiga ne suka harbe shi a babban birnin ƙasar Ouagadougou a 1987.
Daga nan ne kuma Compaore ya mulki ƙasar tsawon shekara 27 har zuwa lokacin da aka tumɓuke shi a 2014.
Sankara da Compaore abokan juna ne da suka haɗa kai wajen yin juyin mulki a shekarar 1983.
Ana ganin Sankara a matsayin wani gwarzo a fadin Afirka saboda aƙidarsa ta ƙyamar Turawan Mulkin Mallaka.
Tun bayan da aka tumbuƙe Compaoré daga mulkibayan wasu jeri zanga-zanga a 2014 yake gudun hijira a ƙasar Ivory Coast.

Asalin hoton, AFP
An kuma samu wasu mutum 13 da hannu a laifin kisan, da suka haɗa da babban mai tsaron Compaoré, Haycinthe Kafando, wanda aka zarge shi da jagorantar mutanen da suka kashe Sankara.
Shi ma an yanke masa hukuncin ne a lokacin da ba ya kotun aka kuma yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai.
Sai dai dukkansu sun musanta tuhume-tuhumen da aka yi musu. A baya Mr Compaoré ya yi watsi da shari'ar yana mai kiranta shiriritar siyasa.
Gilbert Diendéré, ɗaya daga cikin kwamandojin rundunar sojin a lokacin juyin mulkin 1987 da kuma babban mai kare kan nasa waɗanda suke halarci kotun, su ma an yanke musu hukuncin ɗaurin rai da rai.
A yanzu haka dama yana zaman gidan kaso na shekara 20 kan laifin ƙoƙarin juyin mulki a 2015.
Wannan hukuncin na yanzu ya kawo ƙarshen shari'ar wata shida da aka yi wacce aka fara ta tun bayan mutuwar Sankara, shekara 34 da suka gabata, wanda kisan da aka yi masa a wani juyin mulki ya zama sanadin ɗarewar Compaoré mulki.
Sauran mutum takwas ɗin da ake ƙara sun ma an yanke musu hukuncin ɗauri daga shekara uku zuwa 20 a gidan yari, sannan kuma an wanke wasu ukun da ake tuhuma.
Wakiliyar BBC Lalla Sy ta ce ɗakin shari'ar ya kaure da sowa a lokacin da alkali ya sanar da hukuncin.
Har yanzu ana karrama aƙidun Sankara a faɗin Afirka.
Tun daga Ougadougo har Khartoum, ana amfani da hotunansa a wajen zanga-zanga.
A yayin zanga-zangar 2014 da aka hamɓarar da Blaise Compaoré, an sanya hotunan Sankara a tutoci da alluna. A duk shekara sai al'ummar Burkina Faso sun yi taron tuna ranar mutuwarsa.

Asalin hoton, AFP
Laƙabin da magoya bayansa ke kiransa da shi shi ne African Che Guevara.
Sankara mai aƙidar Markisanci ne wanda ya girma a lokacin Mulkin Mallaka a Afirka.
An haife shi a ƙarshen shekarun 1940, kuma a shekarun 1960 ne Sankara ya fara samun burin kawar da tsarin mulkin mallaka a Afirka.
Shekararsa 33 kacal a lokacin da ya zama shugaban ƙasa a 1983. Ya sauya sunan ƙasarsa dafa sunan da Turawan Mulkin Mallaka suka sanya mata na Upper Volta zuwa sunan Burkina Faso, da ke nufin ƙasar mutane masu gaskiya.











