Mai kada jitan da ya ceto daruruwan mutane daga jirgin ruwan da ke nutsewa

- Marubuci, Daga Sarah McDermott
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC
- An wallafa
Yayin da jirgin ruwa na alfarma mai suna Oceanos ya fara nutsewa a sanadiyyar wata igiyar ruwa mai karfi kusa da gabar tekun kasar Afirka ta Kudu a 1991, sai wani mawaki mai suna Moss Hills da abokan sana'arsa suka samu kansu cikin wani mawuyacin hali.
Suna cikin cin abincin dare ne sai Moss Hills ya fara lura cewa guguwar da suka dosa mai karfi ce matuka. Ma'aikatan jirgin da ke raba abinci sun rika fuskantar matsala inda abinci da abin shan da suke kai wa ga fasinjoji suka rika zubewa.
Moss mai kada jita ne dan kasar Zimbabwe da ke aiki a jirgin ruwan tare da matarsa Tracy, wadda ita ma mai kidan jitar bass ce. Bai taba ganin masu raba abincin jirgin na barin farantan abinci da abin sha ba.
Tun da safiyar wannan yinin wata iska mai karfi tare da ruwan sama kamar da bakin kwarya sun hana jirgin tafiya zuwa birnin Durban sau da yawa. Amma da suka ga babu alamar yanayin zai gyaru, sai kyaftin din jirgin ruwan ya yanke hukuncin barin tashar jirgin ruwan kuma jirgin na Oceanos dauke da fasinja 581 tare da ma'aikatan jirgin suka nufi tekun da igiyar ruwa mai tsawon kafa 30 da guguwa mai gudun kilomita 74 cikin kowace sa'a.
Moss da matarsa Tracy - wadanda shekarunsu na haihuwa talatin da wani abu ne - na gayyatar fasinjojin jirgin ruwan zuwa wani wuri a saman jirgin yayin da suke tafiya cikin teku. Amma a wannan yinin sai aka koma cikin wai babban dakin jirgin.
Moss ya ce "guguwar ta rika karuwa sosai".
Yayin da aka fara cin abincin dare sai ya yanke shawarar zuwa dakinsu ya hada kayan ko-ta-kwana.
"Ba da jimawa ba sai kawai muka ji wani kara, kuma jim kadan bayan haka sai duka fitullun jirgin suka mutu".

Da ya ga babu jami'an jirgin da suka bayyana domin sanar da fasinjoji halin da ake ciki da kuma matakan da za a dauka, sai Moss ya fara shiga damuwa.
"Kana cikin jirgin ruwa a tsakiyar teku yayin da wata mahaukaciyar guguwa ke tasowa kuma cikin duhun dare," in ji Moss, "Sai na ji cikina na murdewa".
Bayan da wasu fitilun jirgin ruwan na kar-ta-kwana suka kama, sai Moss ya nufi dain da suke kade-kade domin duba kayan kidansa. Ya ga kayan warwatsewa a kasa. Daga nan ne ya lura cewa ba ya jin karar injinan jirgin ruwa. Jirgin ya fara rage gudu saboda babu injinan da ke tafiyar da shi.
Jim kadan bayan haka sai jirgin ruwan mai tsawon mita 153 (wato kafa 502) ya fara kadawa a jirkice yayin da igiyar ruwa ke toroko tana bugun jikinsa.
Sai ga fasinjojin jirgin a firgice sun fara shigowa dakin da ake yin wasanni da kade-kade.
Bayan sa'a guda sai fasinjoji suka fara rikicewa. Daga nan ne Moss ya yi tunanin daukar wani mataki domin taimaka wa kowa a samu nutsuwa.
Sai ya dauko wata jitarsa kuma ya fara kada ta kuma yana waka, inda sauran 'yan kungiyarsa ta waka suka fara amsa masa domin kwantar wa fasinjojin hankulansu.
Bayan wani lokaci sai ya kula cewa jirgin ruwan na jirkicewa gefe guda - wato ba ya tangal-tangal kamar a da.
Sai Moss ya gaya ma Tracy cewa: "Wani mummunan abu na faruwa. Bari na yi kokarin duba halin da muke ciki.

Sai Moss da wani makadi mai suna Julian suka fita, suna rike karfen gefen jirgin ruwa domin kar su fada cikin teku. Sai suka sauka daga saman jirgin ruwan zuwa dakunan kasa cikin matsanancin duhu. Sun rika jin wasu muryoyi na magana cikin firgici da harsuna daban-daban. Manyan jami'an jirgin ruwan sai guje-guje suke yi, inda wasunsu ke dauke da jakunkuna, wasu kuma sun sanya rigunan da ke hana mutu nutsewa idan suka fada teku, wasu kuma sun gansu a jike.
"Mun yi kokarin tambayarsu wane hali ake ciki, amma babu wanda ya kula mu cikin jami'an jirgin," in ji Moss.
Sai Julian da Moss suka wuce zuwa dakin injin din jirgin - wanda wurin da yafi zurfi ke nan cikin jirgin.
Moss ya ce "muna shiga sai muka ga babu kowa cikin dakin jirgin. Ba a taba barin wannan dakin babu kowa cikinsa ko da uwa jirgin yana cikin tashar jirgin ruwa ne."
Sai ya lura da wani sauti na ruwan teku yana kwarara daga bayan wasu manyan kofofi. Nan take ya gane cewa jirgin ruwa Oceanos na nutsewa ne.

Ban sun koma dakin da fasinjojin suka taru a saman jirgin ruwan, sai Moss ya tambayi daraktar jirgin me ake ciki. Sai ya gaya masa cewa kyaftin din jirgin ya sanar da ita cewa dole su gudu su bar jirgin.
"A lokacin ne muka gane cewa manyan jami'an jirgin tuni sun shiga wani kwale-kwale kuma sun gudu sun bar fasinjojin," in ji ta.
Moss da sauran fasinjojin basu san yadda ake kwashe fasinjan jirgin ruwa, ko yadda ake sauko da kwale-kwalen jirgin da ke daure a gefen jirgin.
Daag nan ne suka gano yadda ake sauke su kuma suka fara yin haka, kuma duk da karfin igiyar ruwa sun rika loda kwale-kwalen da fasinjoji kimanin 80 zuwa 90 cikinsa.
Sai dai Moss bai san yadda zai tayar da injinan kwale-kwalen ba, ko ma inda makulan jirgin suke.

Ga shi kuma lokaci na kure musu saboda jirgin na nutsewa.
Sai ya garzaya dakin matukin jirgin, inda suka rika yin kokarin kunna rediyon jirgin domin su kira a taimaka musu.
Bayan sun kunna rediyon jirgin sai suka fara aika wa da sakon "May day! May day!", wato "muna neman taimako".
Jim kadan bayan haka sai suka ji muryar wani mutum na tambayarsu, "Yauwa, a kan me kuke bukatar taimako?"
Nan take Moss ya sanar da shi cea yana ckin wani jirgin ruwa ne mai suna Oceanos kuma ya fara nutsewa.
Sai suka fara magana tsakaninsu kamar haka:
"Saura sa'a nawa jirgin ya nutse?"
"Ban sani ba - muna cikin wani mawuyacin hali kuma ruwa ya kusan cika jirgin, sannan muna da kimanin fasinja 20 cikin jirgin."
"Kuna ina ne yanzu?"
"Muna tsakanin tashar jirgin ruwa ta East London da Durban".
"Ba abin da nake bukatar sani ke nan ba. Gaya min ainihin inda ku ke ta hanayar duba malejin jirgin".
Sai Moss ya ce bai san komai game da yadda ake gano inda lambobin suke ba.
Bayan kai komo tsakaninsu na wani lokaci, sai mutumin ya hada Moss da wasu jiragen ruwa da ke yankin kuma sun sanar da shi cewa ya koma dakin kyaftin din jirgin.
Abin mamaki shi ne bayan da ya shiga, sai ya ga kyaftin din cikin wani hali na gigicewa yana zaune cikin duhu.
Sai ya sanar da shi cea ga bayanin da suke nema, amma kyaftin din bai amsa ma sa ba.
Jiragen ruwan sun iso inda Oceanos ke nutsewa, kuma sun gaya wa saran jiragen ruwan da ke yankin halin da yake ciki, domin ba su da isassun kwale-kwalen da za su iya kwashe sauran fasinjojin da ke cikin jirgin.
Sai hukumomin Afirka ta Kudu suka fara shirin aikawa da jirage masu saukar ungulu domin su ceto fasinjojin.

Yayin da igiyar ruwa ke ci gaba da jujjuya jirgin, Moss da Tracy sun zauna kusa da juna cikin duhu, suna addu'a ko taimako zai iso musu kafin lokaci ya kure musu.
Shi ta Tracy na da 'ya mai shekara 15 da haihuwa mai suna Amber, wadda ta ke wata makarantar kwana a Afirka ta Kudu.
"Bai dace a ce duka iyayenta sun halaka ba," in ji Moss "Duk yadda ta kasance, dole wani cikinmu ya tsira daga cikin wannan jirgin ruwan".

Sai bayan kimanin sa'a uku sannan helikwafta na farko ya isa kuma ya tsaya a saman jirgin.
Daga nan sai sojojin ruwa biyu suka rika sauka inda suke amfani da wasu igiyoyin da aka daura a jikin helikwaftan. Sun koya ma Moss yadda zai rika taimaka musu domin su kwashe kowa cikin hanzari.
Daga baya an tura wasu helikwaftocin uku wanda ya sa suka zama guda biyar. Kowannensu ya rika daukan kimanin mutum 12 zuwa gabar teku yayin da hasken asubahi y afara bayyana.
A karshe an kwashe Moss da Tracy tare da fasinjojin da aka kwashe na karshe.
Kuma yayin da helikwaftan da ke dauke da Moss ya sauke su, sauran fasinjojin sun garzaya wurinsa suna waka kuma suna sowa, wasunsu ma sun rungume shi.
"Sai na fara kuka", in ji Moss, "kuma daga nan sai na ji gajiya ta hau ni baki daya".

Asalin hoton, Getty Images
Ranar 4 ga watan Agustan 1991, jirgin ruwan Oceanos ya nutse baki dayansa a teku. Dukkan mutanen da ke cikin jirgin sun tsira da ransu.
A yanzu Moss da Tracy mazauna birnin Liverpool ne, kuma sun ci gaba da aiki a cikin jiragen ruwa na kasaita na shekaru masu yawa.









