Elon Musk ya sayi hannun-jarin $3bn a Twitter

An wallafa

Elon Musk ya sayi kashi 9.2 a kamfanin Tuwita, kamar yadda bayanan harkokin kasuwancin Amurka suka nuna.

Labarin sayen hannun-jarin ya sa hannayen-jarin Tuwita sun tashi da kusan 25 a kasuwar hada-hadar hannun-jari

Mutumin, wanda ya kafa kamfanin kera motoci na Tesla, ya sayi hannayen-jari 73,486,938 na Tuwita ranar 14 ga watan Maris, a cewar Hukumar da ke kula da hada-hadar hannayen-jari.

Hannayen-jarin sun kai kusan $2.89bn (£2.20bn), idan aka yi la'akari da farashin da Tuwita ta rufe hada-hadar hannun-jari ranar Juma'a.

Sayen hannayen-jarin ya sa ya zama daya daga cikin mutanen da suka yawan hannun-jari a kamfanin kuma ya fi wanda ya kamfanin na Tuwita Jack Dorsey yawan hannun-jari yanzu a kamfanin domin shi yana da kashi 2.25 ne kawai.

Musk yana yawan amfani da Tuwita inda yake da mabiya fiye da miliyan 80, ko da yake a kwanakin baya ya ce yana duba yiwuwar kafa sabon shafin sada zumunta.

A watan jiya Musk ya nemi jin ra'ayin mabiyansa kan ko suna ganin kamfanin Tuwita yana karfafa gwiwa kan fadin albarkacin baki.